33

2.6K 395 50
                                    

MRS AMIDUD...!?

KURUCIYAR JAN PARIH

https://my.w.tt/XGvckkY6N6

Dedicated to my Aunty Nice😊

𝓜𝓪𝓲_𝓓𝓪𝓶𝓫𝓾❦︎

     _Hahha! Ya kuke ci da zuci! Bafa Yar Gidan Yadiko bane wanda na gama shi a Pages 46-47!🙄 wannan da ko rabin labarin ban shiga ba kuna cewa Shiriritan Pharih yayi yawa! Nagode da shawarar ku! Amma labarina a tsare yake! Kuma in ku lura Pharih ke bada labarin kuruciyarta idan zaku iya zuwa, sai mu tafi idan baku iyawa! Ku barmu muyi tafiyarmu 🤣😂 dan ko harafi kwaya d'aya bani sauyawa 👌🏻😎Ai duk wanda yaji ance kuruciya yasan labarin ba wani abu bane sai na shirme da shashanci_

Ana zaman ‘karya, Bamaguje ya zo gari ya iske ba masussuka.

   

33.
Tafiya nake ina masifa, har da cewa jikar masu fitsari a tsaye.
Hango inda take zaune ya zuba idanun shi akan wayar hannun shi.
    Kyau yayi min, ajiye abincin nayi na leka wayar naga abinda yake gani sai janyo Ni yayi na fada kanshi. D'ago fuskana nayi ina kallon yadda ya b'ata rai kamar bashi ba, sai kallon shi yake yi.

         "Don Allah karki kwashe min kyau da ido." Ya fada a hankali.
      Kiciniyar tashi nake amma ya daura min hannun shi a bayana sosai.
          "Ni ka kyale ni, na tashi tunda ka mai dani mayya." Na fada cikin jin haushi.
"Ai! Toh kurwan Amidud yafi karfin ki ko?"

    "Allah idan baka kyale ni ba zan yanka maka cizo!"
        Juyo da fuskar shi yayi yana kallona, lashe bakin shi yayi sannan ya sunkuyar da fuskar shi dai-dai nawa, kafin na fahimci abinda yake nufi.

     Tuni naji bakin shi a saman nawa ya cijeni!, Rufe idanuna na rufe tare da saka mishi kuka.

         Ganin yadda hawaye na zuba daga idanuna,  sumbatar bakina ya fara a hankali, rike rigar shi nayi, sake matse ni yayi a jikin shi. Cikin wani irin romantic yake sumbatar bakin nawa.
           Yadda kwalla ke zuba a idanuna kamar an bude fmfo har shasheka nake bai sanya shi ya fasa ba, ban san ya akayi yasan matar shi ta ido kusada kofar shiga gidan, kawai ya janye ni ko kallon inda nake bayi ba, dai dai shigowar ta..

"Wannan wani irin hauka ne?! Kin tashi kin zo fadi akai na me yasa baki da hankali ne?! Wallahi zan kira Mamie na gaya mata "

       Juyawa nayi da gudu zan wuce, tace.
"Ai gwara ka gaya mata! Wannan haukata yayi yawa"

        Dakina na wuce na rufe kofar tare da jingina da kofar na fashe da wani irin kuka, har jikina na rawa.
  
Ban san me yasa Ya Amidud yake min haka ba, idan Kanwar shi ce ai bazai so lalata mata gobenta ba,  Alqur'an sai na rana akan wancan matar shi.

           ......
"Zoki zuba min abinci tunda baki iya kula da mijinki ba, ki dauko filet ki zuba min. Daga dawowar mu babu abinda naci. Ko hutawa ban yi ba kin fita damuwarki! Sai anyi magana kice ke kin fi kowa sona."

   Cikin borin kunya tazo cikin jin haushi ta ajiye jakar takardan da tazo dasu. Kitchen ta shiga taga Yemih a tsaye tana aikin.

        "Eh bake kika girka mishi abincin ba?!" Tambayi Yemih.

       "A'ah wata kyakyawar yarinya ce! Ta girka mishi!"
A sukwane ta fito daga kitchen ɗin dama yasan haka zai faru, Crossing leg din shi yayi, tare da tsuke fuska.

        Saka hannun tayi zata  zubda abincin.
"Don't!!!"
Ya daka mata tsawa, har yana fidda idanun shi.
 
"Abincin wancan Yarinyar ce zaka ci?!"
"Toh a Bauchin abincin waye muka ci?!"

"Honey! Just ansa my Question?!"
"Bazan amsa ba!ke me yasa a Bauchi kika ci abincinta?! Da tsabar rashin godiyar Ubangiji kice bazaki ci abincinta ba,! Ruwanki ki dauki kici abincinta ruwanki karki ci! Ba zan ci abincin wancan da kika kawo ta dan ta girka ba, abinda na sani an biya mata hakkinta!"

 
        "Amidud! Ni kake gayawa Magana kake gaya min?"
   Mik'ewa yayi ya nufi kitchen yaje ya dauko cokali da filet ya ajiye.
  Mik'ewa ya kuma ya. Yazo har kofar dakina, buga min yayi.

Da sauri na bude ina share kwalla. Tura baki nayi sannan nace.
"Kuma me zan maka bana gama abincin ba."
Watsa min harara yayi cikin fusata.
"Zaki wuce ki zuba min abinci ko sai na b'ata miki rai."
   
Ganin babu wasa a fuskar shi ya sani, bin bayan shi, naje na zuba mishi. Ina gamawa zan dawo yace min.
"Zauna"
   Kallon shi nayi, ga Aunty Lamisah a tsaye.
     Zama nayi ina kallon yadda yake cin abincin. Har ya gama bai ce min kome ba, zan mike yace.
"Baki bani ruwa ba, haka ake bada abincin babu ruwan."

  Mik'ewa nayi zan wuce, ta sha gabana dake idanunta ya rufe, kawai tasaka hannu zata mare ni, daga Ni har ita bamu san lokacin da ya iso tsakiyar mu ba.
Ya mai da hannunta baya.
     "Wallahi sai na kashe yarinyar nan, shegiya dan ubanta, tashigo rayuwata zata hanani sukuni."
  Juya idanuna nayi tare da fitar da harshe na ina mata gwalo.
Aikuwa ta juya cikin fushi ta dauki tulun flower ta wurga min na kankama bayan shi, dake idanunta ya rufe sai rusawa mijinta a goshinsa.

"Auuchw! Lamisy! Meye haka? Ke mahaukaciyar ina ce? Dube yadda kika kwala min."

   Ganin jinin dake zuba ban san lokacin da na fashe da kuka ba, ina cewa.
"Wayyo Yaya! Jini na zuba."
Duk na rud'e.
Riko hannuna yayi muka haura can inda dakin shi yake.

Buɗe baki nayi ina kallon ikon Allah, ji nayi an fincikoni ni. Kafin nasan meye ai ta turo Ni waje.

      "Lamisy! Wannan wani irin Iskanci ne?!" Ya fada mata da karfi yana tureta itama.
Ya buɗe kofar yayi. Yaga bana bana nan, rike ciwon yayi da yake zubda jini ya sauko da sauri yazo kofar dakina ya buɗe.
Akwance ya same ni.
"Jaaaaaal!"
Da sauri na mike, cikin kuka nace.
"Yaya! Zo muje na wanke maka, kana zubda jini."
       Jan hannunshi nayi muka shiga ban daki, kamar yaro haka ya koma min.  Na zaunar dashi, ruwa na tara dan hauka na ciro karamin towel na tsoma a ruwan na shiga saka mishi ina goge mishi jinin.

                  Lallai Lamisah bata da hankali, domin har dakin ta biyo mu.

        Jin tana murda kofar ban dakin, ya sashi mik'ewa ya janyo Ni tare da hadani da kofar, ya matse Ni da kirjin shi yadda bazai takurani ba.

         Kallon cikin idanuna yayi, yaga yadda nake raba su, kamar mara gaskiya.

         "Dama kina jin tsoron Mata na?!" Ya tambaye ni.
"Kai Haba sai dai taji tsorona!"
"Ba gashi idanunki sun nuna you scare"

     "Sikure! Me haka yake nufi?!"
"Zaki sani idan Lamisah ta kamani."
   Murguda mishi baki nayi tare da cewa.
"Mu kama juna! Dai"
         Kawo fuskar shi yayi zai hada da nawa na kauce cikin jin haushi nace.
"Filis! I no lek dis, kazanta i go teli mamie yu dey eti mey mauti!"
"Pharih! Baki da hankali ne?! Idan ke mahaukaciya ce gaya mata mana?!"
"Mahaukaciya fa?! Ka kirani, Kwarankwatsa sai na gaya mata. Sai ka tabbatar da haukar ko daga turu nake, wancan da ta roseka baka kirata mahaukaciya ba sai Ni da nazo na wanke maka ciwon, toh fita min daga d'aki ko na rufe idanuna na...."

      Ajiyar zuciya na sauke sakamakon jin hannun shi cikin burodina.
😂🤣🤪

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now