Page 3

3.4K 307 8
                                    

*MRS AMIDUD....?!*

_KURUCIYAR JAN PARIH_

Dedicated to my Aunty Nice😊

Page_2

Murmushi Baffa yayi sannan yace.
"Ai mota ce itama"
   
Shiru nayi domin tun da nake ban tab'a ganin wannan damuwar ba,juyawa nayi zan koma hanyar da muka fito Nura yayi maza ya kwabko Ni, kuka na saka tare cewa.
"Aradun Allah na fasa, kome zaku yi sai kuyi."
    Aikuwa cusani yayi cikin yar kurkura, ihu na saka tare da kame jikina a bisa wani lallausar abu, tsalle nayi sai da kaina ya buga da rumfar yar kurkura, safe kaina nayi tare da fashewa da kuka nace.
"Wayyo Allah na dakwalwata"

        Tadda yar kurkura Nura yayi,
     Naji ta fara numfashi huuuuuuuuuu.
"Wayyo Allah na, wallahi Ni ban nime mutuwa ba, gashi yau za a kaini a cikin yar kurkura, wayyo Allah na wallahi ban gama zuwa binnin ba sai gashi yar kurkura zata kaini lahira"
 
Haba me de na zai ban da dariya, shima Baffa dariyar yake.
Shiru nayi ina raba idanu, can idanuna ya sauka akan bishiyoyin da muketa wucce su.

  Sake baki nayi na koma jikin tagar motar ina kallon yadda dariya nasaka sannan nace.
"Yan banza in ba tsoron ba, ku kara sauri mana"

       Girgiza Baffa yayi tsabar dariya, juyawa nayi nace.
"Baffa! Nikam A ina muke tafiya badai akan taburma da ruwa nan muke sharara uban gudu nan kamar mu kai sautu bangon duniya."

        Bai ce min komai ba, shigar mu garin misau, na sake baki ina kallon wata yar karamar Y'ar kurkura, me kafa uku.
"Baffa wancan yar kurkura me kafa ukun da"

      "Keke Napep kenan! Wasu suna kiran da adedaita sahu ko kafin babur"
Shiru nayi ina nazarin yar kurkura, can da wata banzar tunani yazo min nace.
"Aihoo wancan babur me numfashin ya haifi wannan kafin babur din, ayya hi wancan me kafa biyu. Wannan me kafa uku."

    Ta madubin drvn ya kalle ni.
             Shiru suka yi har nima, can kuma nace.
"Baffa! Wai me yasa bishiyoyin nan suke binmu da gudu."

    Juyawa yayi cikin gajiya da damuwata yace.
"Sabida su cinye bakin matambayi, koma ki kwanta ko kuma su zo su cinye bakin ki."

    Zaro ido nayi cikin tsoro nace.
"Toh su bishiyoyi binnin haka suke dama"

    Bai kuma bin takaina ba, har muka bar misau muka nufo Bauchi.
          Tsayawa mukayi a wani gidan me yawan bututu, sai kallon gidan nake, ina ganin me tuka yar kurkura yaje ya sayo min wani abu da ruwan tare da wasu abubuwa ya kawo min, na amsa sai kallon abin nske.
              Fita suka yi ina zaune Baffa ya shigo kallona yayi sannan yace.
" Parih muje kiyi sayi."

       "Hmm" nace sannan na fito, muna zuwa ya nuna min ban d'akin da bauta karba nayi ina shiga bayin naga wata yar tunkuya me ban sha'awa, tsayawa nayi ina kare mata kallon cikin jimamin nace.
"Alkur'ani bazan tab'a ki ba, sayin ma na fasa to tukunya da rufi, waye zai so b'ata ta."

  Fitowa nayi naga Baffa yana kallon agogon hannun shi, ajiye butar nayi muka wucce.

       Muna shiga Baffa ya amshi kayan ya buɗe min sannan ya mika mini wata ruwa baka sai kumfa take.

  Kare mata kallo nayi sannan na girgizata, ai kuwa sai ga kumfa fuuuuuuuu. Ai ban san lokacin da nayi wurgi da goran ba na daka uban tsalle jikina na kerrma.
"Wayyo ni Parih naga siddabaru! Wallahi bani shan wannan kayan maitar kaga abu hi daya yana kumfa sai kace tsatsamar nono."

       Juyowa Baffa yayi dan wurgin da nayi da abin ya b'ata mishi kayan shi.
"Sannu Jan ai ba haka ake yi ba, duk kin jika mu."

           "Wallahi Baffa wancan abin kumfa yake "

     Jinjina kai yayi sannan ya duba goran wani ruwa ya miko min, Mika min yayi, nasa hannun na amsa cike da tsoro na kai bakina naji babu wannan alluran da suka soke min harshena, wasu abubuwa na leka na kasa ci kamar zanyi kuka nace.
"Alkur'an bani cin wanga ana"

     Ajiye musu nayi a gefe ina tura baki.
            Muna isa soro naga me rogo washe baki nayi sannan nace.
"Baffa ga can rogoji, da kosae"
    Tsayar da me tuka yar kurkura yayi sannan ya mika mishi kudi, can sai ga shi da nikinikin cima, har da barodi.

Kashe bakina nayi cikin dariya nace.
"Yau zanci cimar binnin."

  Yana miko min na amsa na yaga ledar, na zabtari barodi, na shiga dangwala da wannan ruwan dadin nan ina ci.

    Ai ina gama ci na bingire sai barci, leko Ni Baffa yayi yace "arkin tambaye har tayi barci."

            Karfe biyu muka iso bauchi, dai dai da farkawata.
   Kallon garin na shiga yi ina mamakin wani gini da muka wucce, me dororo.

   "Baffa shi wannan abin mutane basu tsoron ya diro musu tsakar ka."

        "Me fa Parih!?"
Ya tambayeta,
    "Wancan dororon mana da muka wucce."

           Jingina kai yayi, tabbas fito da fari daga can shine zai taimakawa rayuwarta gurin samun ilimin addini da na boko,
     

MRS AMIDUD.....!!?Where stories live. Discover now