MR AMIDUD...!?
KURUCIYAR JAN PARIH
Dedicated to my Aunty Nice.
Page_10
Kallon Jalal kowa yayi suka fashe da dariya, musamman yadda bakin ya koma.
Mik'ewa yayi ya bar cikin gidan yana nazarin me zai mata ya huce haushin sa akanta."Toh kice mihi ya daina, kirar hansatu d'akin shi."
Shiru falon yayi kafin ta kuma buɗe baki tayi magana sai ji tayi an buge baƙinta, rikewa tayi tana kallon Mamie dan ta baya aka daki bakinta, juyawa tayi dan tana kirar kukanta ne ganin yanayin fuskar shi babu Annuri yasata kifa kanta jikin Mamie ta fashe da kuka, tana cewa.
"Wayyo Allah na! Mama na! Wayyo Allah na! Abba na zai kahe Ni, Ni kan ku mai dani gurin Iyata."
Birkita musu lissafi tayi da bori na fitar hankali, tare da mugun rikici.Dama jikinta da zazzabi take ya kara tasowa, a jikin Mamie ta makale.
Har lokacin barci yayi Buhayyah tazo ta rike ta suka kwanta.Bayan tafiyarsu ne Alhaji Muhmood ya juya ga AMIDUD cikin fada yace.
"Bana son saurin hannu! Idan bata gani ba ai bazata fada ba, karka kuma dukar ta, bana so dan yau naji ba dad'i kaji tsabar dukar ya shageta tana kirar iyayenta""Amma Daddy haka zaku cigaba da ganinta tana tab'ara son ranta, wallahi zata lalace."
"Idan masifarka bata lalata ba! Babu abinda zai faru kune kuke ganin illar abinda take yi Kuruciyar ta ce haka."
Karshe fada suka koma mishi, shi da yake ganin gyara.
----
Cikin dare zazzaɓi ya hanata barci sai kuka take tana cewa.
"Zan sha ruwa!!!"
A firgice Fahhamah ta tashi zuwa d'akin Mamie sai gasu nan tare, dole suka tattara ta zuwa Asibitin Ni'ima, dake can new g.r.a,Suna zuwa aka amshe su, ba wani abu bane sai tsoro da ya haifar mata da zazzaɓi.
Ruwan na karewa zuwa karfe biyar aka sallame su.
Koda gari ya waye a bata tashi da wuri ba, sai karfe biyu ta farka dake D'akin Mamie aka kawota, tana tashi ta fito falo ganin duk suna hira sai wata ƙatuwar doll da ta gani ko nace Teddy, babba.
Ihu tasaka tare da komawa ciki da gudu.
"Parih! "
Buhayyah ta kira sunanta. Dariya Aarib yake
"bakin mugu kawai ai nasan saboda ita kasaka a gurin kuma sai na gayawa Daddy, ai kasan bata da lafiya zata ji sauki tayi maganin ka kato ajebo"Tura baki yayi sannan yace.
"Ke kuma tsinken biro kawai"
Make keyarshi Amrozia tayi cikin fada tace.
"Wawa kawai katon banza ina ruwanka da ita da zaka razana, kuma sai mun kona Teddyn."Shigowa dakin da take suka yi suka ganta can kuryan gadon, zama suka yi suna bata hakuri, ban daki Buhayyah ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka, sannan ta ce taje tayi.
Dake bata jin dai dai, bata ce komai ba har tafito wankar.Kayanta Amrozia ta kawo mata ta saka sannan saka ta kuwa fito falon, kallon Aarib tayi ta kauda kanta.
Dumamen tuwonta aka kawo mata, taci kadan a sannan Mamie ta sauko daga dakin Alhaji Muhmood tasa aka dauko mata maganinta.
B'allo mata maganin tayi tare da mik'a mata, kallon maganin tayi tare da zaro ido tace.
"Na higa uku! Ina zan tura su! Wallahi ina hain su mutuwa zanyi dan wancan rike min wuya zata yi""Ke amsa bana ciki da sakarci" Mamie tace mata,
"Wallahi bani shan su"
"Buɗe baki na zuba miki"
"Allah fasa min makoshin zasu yi""Parih zan zane ki fa! Buɗe maza na saka miki"
"Kwarankwatsa bani shan su!"
"Ya ilahi! Kina da lafiya kuwa magani ne ai"
Dariya tasaka sannan tace.
"Ranar da muka je ruga naga Hard'o yabawa wata karsanan shi tasha Ni ba karsana nace Alqur'ani bani shan su! Kalan na koma Yar mataki""Ke Buhayyah dauko min bulalar can na zane fitinanniyar yarinyar nan"
"Allah Mamie karki zane Ni dan bazan iya had'iye dindinkeken maganin can ba, dama kananun ne"
"Toh naji bari na jika miji!"
Tura baki tayi tace.
"Ni yar akuya ce da za a bani jikakken magani Allah Ni na tsani maganin naji sauki ma""Assalamu alaikum!"
Muryan shi ya gauraye falon,
"Mamiena! Jika min nasha bani kuma miki gardama"Jika mata tayi maganin, tana kwalla tana komai, zama tayi yana kallon tv bai masana tana gurin ba, dan tunda yace.
"Good Aftenoon Mamie!"
Bai kuma cewa komai ba, mika mata kofin Mamie tayi sannan tace.
"Lafiya lau! Ya gajiyar hanya"
Karba tayi ta kalli maganin, ta kalli Mamie ta kuma kalli inda yake sai ta fashe da kuka tace.
"Toh wallahi nikan ki dureni kawai dan bani iya shan su da hannuna"Dafe goshi Mamie tayi tana kallon ta, kafin tace..
"Yayansu! Don Allah bata ganin nan tasha"Idanun shi na kan tv yace.
"Ayya Mamie ki karasa aikinki kawai dan Ni zan b'allo muku tekune kuma baku da abin tare wa."Tashi tayi ta bar falon.
Juyawa yayi sannan yace.
"Kafin na kara karar tv nan naga babu komai a cikin kofin ko na miki dukar da sai kin had'iye kofin baki d'aya."Jikinta na rawa ta dauka, ta kifa a bakinta, tana sha tana yunkurin amai,
Ai kuwa tana shanyewa amai na zuwa mata, duk ta kwara mishi a jiki. A tsorace ta ja baya tana kallon kayan shi da shi kan shi Yadda ta jika shi da aman, wulla mata remote yayi ya bar falon.
Dariya tasaka tace.
"Dan gayu toh yau na ga karhen gayu tunda na zabga maka amai na kuma sai kayi yadda ka gadama dani"_Allah ka shirya mana haula! Amma Parih na bidar du'a'i 🤣😂_