'Yan mata ne su uku ke tafe, sanye da uniform, dukkan nin su tsaf suke, kayan nan sun sha guga, da bula, kasancewar kayan na su, farare ne, wandon kore, kowacce su na dauke da murmushi, da alama hirar da suke na musu dadi, daya a cikin su ce ta kalli ta tsakiyar su ta ce,
"Gaskiya Zeenat ba ki da M, kina jin Usamatu na ta maki magana, amma kika wani share shi, kamar ba ki ji shi ba,"
Fari ta yi da idanun ta, madaidaita, wanda ta qawata su da kwalli, sannan ta ja hancin ta madaidaici , ta dage kai, sannan ta banqaro qirji gaba, wall tai da idanun ta kafin ta motsa lips din ta da suka sha mai, sannan ta ce,
"Hummm Suhailah kina wasa da lamari na na ga alama, an fada ma ki ni sa'ar wannan dan yaron ce? Duka duka nawa ya ke? Aji daya fa mu ke"
Dayar da ke gefen hagun ta ce ta fashe da dariya mai qarfi, tare da saurin dafe bakin ta, saboda kallon da Zeenat ta mata, na baki da aji, sannan ta fara magana cikin dariya.
"Ko ni nan ba zan kula Usamatu ba, ballantana Zeenat , haba suhailah wai yaushe za ki daina zubar mana da aji, yara qanana na raina mu?"
"Ni fa Zulfa'u ba nufi na ta biye ma yara su na soyayya ba, sallama fa ya mata ai ya kamata ta amsa, a matsayin ta na Musulma, sannan magana mai dadi sadaqa ce, inda ace da ya yi sallama ta amsa ta masa bayani da bai je yana yada qaryar da ya ke yaɗawa a yanzu ba"
Shiru sukai dukan su, daga baya Zeenat ta kalle su ta ce,
"Banni da shi, zan sa a min maganin shi, gobe sai na sa malam Bala ya zane masa jikin shi, in an ce ya kula wata ba zai yi marmari ba"
"Dan Allah kar ki hada shi da wannan mugun, shi fa da biyu ya ke dukan yara akan ki, tunda shi ma so yake, kunga ba zai so kishiya ba"
Dariya suka kwashe da shi, suna siffanta halittar malam Bala mai qaton tumbi da kai, (Malam Bala🤣)
"Oh ikon Allah wai har mun kai SS 1 mun girma, Zeenat ke kuwa duk kin fimu morewa SS 2, Nan da shekara daya kin gama kin bar......."
Maganar ta ce ta katse a lokacin da ta hango shi tsaye a qofar gidan su, yana jingine da katangar gidan su, yana danna carbi irin na zamani na roba dinnan, sanye ya ke da jallabiyya, sai dogon wando baqi, da hula baqa, Zulfa'u ce ta kece da dariya mugunta, har tana kama ciki, hijabi ta sa ta ɗan kare bakin ta, ta sanar da su wanda ke qofar gidan su a tsaye, Zeenat na gani ta bata rai, sannan ta sanya sauri dan shigewa ta bar matashin a tsaye, ganin haka ne ya sa shi saurin tsayawa a hanyar shigewa gidan nasu, ta yanda ba zata samu damar wuce shi ba kamar yanda ta saba.
Tana isa wajen ta doka tsaki, tare da buga masa harara, kamar zata zazzago da idanun ta, tare da doka tsaki, hannun ta na dama ta sa ta gyara zaman jakar ta, sannan ta ce,
"Malami ka ban waje na wuce, ko na bangaje ka na shiga, tunda gidan na uba na ne, ba na wani ba"
"Haba Zeenat, ban cancanci haka a wajen ki ba, Ni mai son ki ne, ina kika taba ganin masoyi ya zama maqiyi"
"Sau nawa kuma? Sau nawa ana hakan, kai ne dai da baka sani ba, shi ya sa na ce maka ni ba Sa'ar ka ba ce, dan Allah indai ba tsaurin ido ba, ina kai ina Ni? Tun da ka gama jami'a yau shekara biyu, kana nan sai da ka bi nan ka bi can, ba aikin yi, ka kama zuwa kasuwa kamar a can aka haife ka, a haka za ka tara abinda za ka auren? Ka dube Ni da kyau, Ni Zeenat na ci suna na, iyaye na ba su zaban sunan banza ba, sai wanda ya ci ya tada kai, ya ke miqawa wasu, shi zan aura, ban waje"
"Zeenat a kullum ina fada maki, arziqi na Allah ne, kuma dukkan mai rai, baya wuce arziqin shi, komai daren dadewa, sannan mara arziqi baya taba samun arziqi indai Allah bai rubuto shi cikin masu akwai ba, ba ki san me gaba za ta haifar ba, ki yi hakuri mu ci gaba da soyayya, ka fin nan kafin ki gama makaranta na san da yardar Allah ko koyarwa ce zan samu"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...