ALBASA BATAI HALIN...45

417 59 9
                                    

Wani kallon tara saura kwata ta ke mishi, mota guda ya yo na kayan Nawwarah, sai saukewa ake, bai sake juyawa dan kallon Zaituna ba, saboda yau ya yanke hukunci ba tare da neman izinin ta ba, so ya ke sau daya dai ya yi acting din mai gida arayuwar shi, ya na tsananin son qanwar shi, ta rasu, daidai da rana daya bai taba zuwa ganin su Nawwarah ba tunda suka koma birnin Kano, dan haka yanzu dole ya nuna ikon shi na mai gida ya riqe marainiya kuma jinin shi, ko ba komai ba su da d'a ba su da jika, za ta zama mabudin alkhairi a wajen su da ikon Allah.

"Kar ka sallami mai motar nan, ka bashi yarinyar nan ya maida ta inda ya dakko ta, ko kuma ta tafi dangin uban ta,"

Ko juyawa bai ba, sai da mai motar ya tada mota ya tafi ya fara diban akwatuna, Nawwarah na taya shi,

"Bassu Nawwarah zan debe su sun maki nauyi,"

"Wai ba magana na ke da kai ba?"

Sai da ya zo daidai inda take tsaye ya ce,

"Indai ba qirjin ki ba bu zuciya ba kwata kwata, kin fi kowa sanin ciwon maraici kafin na aure ki, dan haka ki matsa na wuce ciki, ban taba bata raina da ke ba saboda son da nake miki, ba wai dan tsoro ba, kar ki bari raina ya baci akan wannan, da ni da ke ba zamu ji dadin hukuncin d zan zartar ba"

A hankali ya ke magana cikin sanyin shi na masu hakuri, amma kalamai ne masu ratsa zuciyar mai sauraro, Zaituna ba shiri ta matsa daga hanya, jikin ta ya yi mugun sanyi tuna mata baya da ya yi, tabbas shi ne babban rufin asirin ta a rayuwa, da ba shi da tuni ta na can ta na watangaririya a tsakanin dangi

Amma fa ba zata yarda a kawo kowa gidan ta ba, saboda ba ta son raba mijin ta da kowa, ko da d'an cikin ta ne kuwa, in aka fi kula da shi a yanda take ji a ran ta sai ta ji haushi, balle 'yar riqo,da sauri ta shiga dan ganin inda zai aje Nawwarah, dakin da ke kusa da nasu ta ga ya shiga, kamar tsuntsuwa haka ta fada dakin,

"Kan ubancan kayyasa, inna yarda na tafashe, yasin sai dai ka kai mata kayan ta can dakin bakin hanyar, ka na nufin dakin nawa za a ajiye ta?"

"Daki biyu ne da ke fa, me ne ne dan ta zauna a nan? Ko a gidan su na nan qauyen dakin su gado biyu ne da shi ita da 'yar uwar ta, balle a binni, daki ne sukutum da guda gare ta, dan Allah ki bari na sa ta anan, can katifa ne kawai, da leda fa,"

"To ba ta ma samu ba? Ba wanda ya isa ya shiga min daki, Jafaru ka ga ni dai kar ka nemi fada na,ka maida ita can dakin na waje, tammm"

Sai jijjiga jiki take ta na harare harare, ranta baqiqqirin, Nawwarah kuwa sai kuka take, tabbas ba kowa ne ya ja mata wannan tozarcin ba illa mahaifin ta, dole ta shanye, d ya mutu a mutumin kirki da har rige rigen ta za ai, amma ya mace a matsafi, dan shaye shaye, dubi yanda kowa ke gudun mugun iri a gidan shi.

"Haba Zaitee ta, ki duba fa ki ga dakin nan daga shi sai soro, in min shiga ciki rufe parlour ake,sai mu bar yarinya ita daya a tsakar gida?"

"Ai da qofa ita ma rufewa zata yi, ba fa zai yu ba Jafaru, ka ga na barta ta zauna kar ka sa na tsane ta tun yanzu zaman lafiya ya gagare ta a gidan nan, ka bi abinda na ce maka yanda muka saba, tammm in ka bari ta shiga tsakani na da kai zaman gidan nan sai ya gagare ta, shawara nake baku dika, tammm"

"Uncle Ja'afar dan Allah ka dawon da kaya na nan din, ba komai,dama rayuwa ba ta tabbata cikin jin dadi, ko wahala, ina son nan dakin"

Cike da tausayawa ya fara kwashe kayan ya maida can, ya jera mata duk wasu kayan ta, da akwatunan ta, daki ya cika ya yi fam, gwanin sha'awa, ga katifar ta qatuwa, sai sabuwar ledar daki, da alama dakin ba a komai a ciki, ya na nan a ajiye ne, labulayen dakin kalar ledar dakin jajaye,sai zanin gadon ruwan toka, pillow daya ne a dakin, sai fankar sama, Nawwarah bata ga laifin dakin ba, amma ta kula Kawun nata bai ji dadin hana ta daki mai gado da carpet ba,murmushi ta sanya na dole a fuskar ta, ta hau murna,da sauri ta hau katifar ta na dariya,

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now