ALBASA BATAI HALIN..44

418 46 9
                                    

Kamar wanda aka tasa, haka ya farka, ranar bai bacci ba saboda ganin Waleedah da Hajiyah da ya dinga yi kamar su na raye, da bacci ya debe shi zai fara mafarkin Hajiyah na tsananin fushi da shi, ta na qoqarin shaqe mishi wuya, tare da fada masa shi ma sai ta kashe shi, haka zai farka a kidime ya na bata hakuri, ya kusan kwana uku ya na cikin wannan uquba, Rabi da ke dakin ta sai ta yi ta jin ihu, da buge buge, da safe ta je ta gyara, Hasheem na cikin wannan hali zabe ya zo, ya zama kamar dan kwaya saboda rashin samun isasshen bacci, gashi ana zaune lafiya za a ga ya firgita,sai kuma ya koma daidai.

Gidan shi kullum d mutane cike, wasu saboda siyasa suke zuwa mishi ta'aziyya, wasu ma sake zuwan suke dan dai a san da su, ana haka sakamakon zabe ya fito, mutanen Hasheem kowa ya sakankance su ne za su lashe zaben, Hasheem na zaune cikin zumudi dan jin wa ya lashe zabe, Rabi na can rakube baki washe ta na son jin wanda ya lashe kujerar sanata, sai suka ji an ambaci abokin takarar Hasheem, Hasheem sake bude kunne ya yi dan ya ji anya gaskiya ya ji kuwa? Nan ya sake jin an jaddada sunan abokin takarar shi, da remote din ya yi jifa zuwa ga TV din, ko gezau batai ba, sai ma ci gaba da rattabo bayanan zabe da tai, ashar kawai ya samu kan shi da lailayawa, cikin bacin ran da bai taba shiga ba ya bar gidan,ba ya ko tunanin bige wani tunda dare ne, haka ya ke sharara gudu, fatan shi ya gan shi ga shi ga Boka Umar,saboda ya ga bayan shi, daga baya ya samu hanyar gamawa da Zhulqiyyah, sun ci amanar shi, ba haka sukai da shi ba, an dauke mishi mahaifiya da yarinya a banza kenan? In ba tada Zeenat ba me suka masa? Yau ko shi ko Umar.

Ko da ya isa Umar na tsaye a qofar gida ya na sauraran redio, ya na murnar nasarar kada Hasheem da akai, bisa Umarnin Aljana Zhulqiyyah, wadda ta ji haushin yanda Hasheem ya yi disrespecting din ta, a tarihin ta ba wani bil'adama da ya taba fada ta fada sai shi, har da ikirarin ganin bayan ta, da kuma qone mahimman abubuwan sihiri da ta bashi, ta hannun Umar din, hakan ne ya sa ta umarci Umar akan y dau mataki akan Hasheem, da ta so su kashe shi take amma Umar ya bata shawara ko za a kashe shi a bari ya dandani wulaqanci, ya biya butulcin da ya mata, bayan ita ce rufin asirin dukiyar da ya ke taqama da ita.

Qarar motar Hasheem ce ta dawo da shi hayyacin shi, da murmushin mugunta ya kalli Hasheem,ya ce.

"Na san ka na tafe, shi ya sa na fito na jira ka, tare da sauraran faduwar ka a idon duniya,kar ka yi gigin aiwatar da abinda zai lalata rayuwar ka gaba daya, ko ma ka rasa ta, domin a shirye nake tsaf na ga bayan ka,"

Sake qulewa Hasheem ya yi, shi da suka wa rashin adalci akewa barazana? Ai bai bata lokaci wajen daga Umar ba ya soka shi da qasa, ya bishi ya taushe ya na duka, tare da kiran sai ya kashe shi,aljanun da ke wa Umar hidima na ganin haka suka bayyana a jikin Umar dan taya shi hukunta Hasheem, wurgi sukai da shi gefe, Umar ya yi matuqar zuciya, ga fushin shi ga na aljanu, umarni suka samu direct daga wajen Zhulqiyya akan a kawar da Hasheem a yau ba sai gobe ba.

Hasheem na miqewa sai ya ji ya ma manta me ke faruwa gaba daya, bai kula Umar ba ya shiga mota ya kama hanyar barin Kano gaba daya zuwa Kaduna, tafe yake bai san inda ya ke tafiya ba, kawai motar shi ta kwace ya shiga daji, wani irin mummunan hatsari ya samu wanda ya yi daga daga da shi da kyar za a iya gane shi, Zhulqiyyah ba qaramin farin ciki ta yi da hakan ba,jinin shi ta shanye tasss, sanan ta tafi, mayun da ke qarqashin ikon ta sun so daukan gawar su cinye ta hana, ta na son duniya ta san wane ne Hasheem bayan ya mutu, kayan tsafe tsafe suka saka mishi a motar, wiwi din da yake sha dama na ciki, a nan su ka bar Hasheem ba bu numfashi a tare da shi 😢😢😢😢😢😢

Da safe makiyaya da ke kiwo ta wajejen ne suka ga gawar shi, nan aka kira jami'an tsaro da asibiti, aka kawo motar daukan gawa,an dau lokaci kafin mutane suka gano ko wane ne shi, ai kuwa ya sha tsinuwa da zagi, ganin kayan asirin da ke cikin motar shi da Wiwi, wasu kuma mutanen cewa sukai wadan da su kuma sun ce sharrin abokan gaba ne, amma Hasheem ba zai taba aikata hakan ba,(duk yanda ka kai ga yin maqiya a rayuwar ka ba ka rasa mai son ka, haka duk yanda ka kai ga yin masoya ba ka rasa masu qin ka, Allah ka sa masoyan mu domin Allah suke son mu, maqiyan mu Allah ka sa domin ka suke qin mu)

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now