Gudu kawai yake shararawa, jijiyoyin kan shi sun tashi,fuskar shi ta yi jawur, bakin shi a bushe kamar wanda ya yi kwana da kwanaki bai sha ruwa ba, bai tsaya a ko ina ba sai qofar gidan Boka Umar,ba neman izini ya fada har cikin gidan auren shi,
"Umar! Umar !! Umar!!! Ina ka ke? Fito nan, Um..."
"Lafiya za ka shigo min gida kamar wani tababbe? Ka na min ihu? Ba za ka tsaya a can dakin zaure ba za ka shigon cikin iyali?"
"Ina matan su ke nan? Wadannan qazaman abun su ka ke kira Mata?"
"HASHEEMM, ka nutsu, ban san me ya sa ka ke wannan haukan ba, amma zan maka abinda ba ka taba zata ba in ka zagi mata na,"
"Me za ka min wanda ba ka min ba? Kun kashen mahaifiya ta, sannan bai ishe ku ba kun hada da 'ya ta, gudan jini na, abar so na"
Cikin raunin murya sosai ya qarasa qarshen,hawaye na zuba a idanun shi, wani irin quna zuciyar shi ke mishi,kamar ana damqe mishi ita, cikin abinda bai fi seconds ba ya ke hango murmushin ta da shagwabar ta,
"Hasheem ka nutsu ka fita daga mafarkin banzan da ka ke, kai ke son duniya da abinda ke cikin ta, yanda ka ke morar Zhulqiyya ni ban more ta haka ba, sannan da izinin ka aka dauki Hajiyar ka, sannan 'yar ka da ta hada da ita taimakon ka ta yi, dole za ka ji zafin abun, amma b lokacin jiran sai ka yanke hukunci, ta duba a tsakanin Waleedah da Nawwarah ka fi son Nawwarah,..."
"Ina ruwan ta da wanda na fi so? Ban amince ba ta zalunce ni, ba zan taba barin ku ba sai na dau fansa,"
Da sauri ya bar gidan ya na share hawayen da ke zuba masa ba qaqqaunatawa, a jikin motar ya zauna ya na ta kuka kamar ba Hon Hasheem ba, sai da ya yi kuka mai isar shi sannan ya shiga motar ya kunna sai gida.
***************************
"Wai ni wannan kukan na meye ne? Na fada maki Allah za ki godewa akan wannan lafiyar da ya baki, sannan ki godewa mijin ki da ya tsaya tsayin daka dan ganin kin samu lafiya, yanzu ki shirya Baban ki ya ce gidan ki za a maida ki, domin can yafi cancanta ki koma, da so samu na ne mu je gida, in kk sake samun qarfin jikin ki an maida ki"
Cikin kuka mai tsanani ta ke magana, ba dan Umman ta nutsu ba da kyau da ba za ta fahimta ba,
"Uuummaaa...ba...ba...zann... koma baaa, ni ku tafi....da niii"
"Me ya sa? Umarnin Baban ku ne...Sa'adatu hada kayan nan mu tafi an kusan azahar, sai bata lokaci muke, tunda aka sallame ta ake abu daya"
Da sauri Zeenat ta dauki wani qarfe mai dan karfi a gefen gadon ta, ta saka a tsintsiyar hannnun ta, tare da fadin,
"In ku ka matsa sai na koma gidan Hasheem kashe kai na zan yi yanzun nan, ba zan koma ba, na fada maku ba na son komawa, har abada"
Mamaki ne sosai a fuskokin su, me ya ke damun Zeenat ne? Cikin fushi Umma ta matsa kusa da ita, Zeenat ta ja baya, tare da sake danna qarfen a jijiyar hannun ta,
"Yanka dan Allah,in baki yanka ba ke ba jini na bace, ba ni na haife ki ba, wato ke a rayuwar ki duk abinda ki ka yi ra'ayi shi zaki yi ko? Duk wani abu da ki ka ga shi ya miki shi za ki bi, umarnin mu ke maki wahala ki bi ko, dan uban ki ki yanka hannun naki, in kin mace kin huta, iyakar mu muyi kukan takaicin haifar 'yar wuta, tunda duk wanda ya kashe kan shi d'an wuta ne, wace iriyar yarinya na haifa ne Sa'adatu? Ya Allah ka yafe min, ka tausaya min ka shirya min zuri'ata"
Zuciyar ta ta yi rauni sosai, idanun ta sun yi jawur, Zeenat kuwa kuka kawai take ta kasa ci gaba da qudirin ta, Qaseem ne ya yi sallama Suhailah na biye da shi, sai Innaah da ta so zuwa dubiya tun tini bata samu dama ba saboda zazzabi da ta dan yi.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...