ALBASA BATAI HALIN....5

391 37 3
                                    

Hannun ta na hagu ta janyo da qarfi, Wanda ya sa Zeenat tsayawa a gaban Kaka Fatu, ba tare da ta shiryawa hakan ba, tana cikin mamakin qarfin tsohuwar ta ji wani irin zafi a kuncin ta, Wanda ya sa ganin ta ya dauke na wucin gadi, a hankali ganin ta ya Fara dawowa ,tana hada ido da Kaka Fatu, ta ji qafafun ta sun Fara rawa saboda tsoro, tunda take da ita, Bata taba ganin fushin ta haka ba, dik da tana Jin labarin fada ne da ita, amma Kaka Fatu kullum soyayya ta ke nunawa Zeenat indai sun hadu, yau ta tabbatar da maganar mutane, in ka tabo Fatu za ka gane wace ce ita, daga sama ta ji kalaman ta, Wanda suka Sanya ta sake shiga tashin hankali.

"Me ya sami waya ta, ta daina Yi daga zuwan ki garin Nan?"

Ja da baya ta Fara Yi, Amma ta ji hannun ta a na Kaka Fatu, tsayawa ta Yi, tana hawayen azaba, Kamar ba tsohuwa ce ta riqe ta ba, hannun ta dafe da kuncin ta, ta Fara qoqarin magana,

"Ciccccire sim din na Yi"

"Me nee ne sim? Ko ma dai me ne ne shi, dakkon Abu na, ki maida min yanda ya ke, sannan ki Kira min mahaifin ki"

Kuka sosai Zeenat ta rushe da shi, ta durqusa ta na bama Kaka Fatu hakuri, tare da Kiran ta rufa Mata asiri, Baban ta kashe ta zai in ya damqe ta, wata tsawa da Kaka Fatu ta dakawa Zeenat ne ya Sanya ta durqusawa a gaban ta da kyau, tana sake gunjin kuka,

"Kaka Fatu bana son shi, in kuka Kai ni gidan shi mutuwa zanyi, ba zan iya rayuwa da shi ba, ba kalar mijin da na ke fatan aura ba ne, Dan Allah ki tausaya min, ke kadai ke so na, shi ya sa na zo wajen ki,neman mafaka, Kar ki maida ni wajen su"

Finciko ta Kaka Fatu ta Yi ta wurga ta hanyar fita,

"Ba su son ki? Su da suka haife ki? Sannan ki ke neman soyayya a waje na? To ni ma 'ya'yana na ke so, ke Kuma tunda na ki iyayen ba su son ki,sai ki rataye kan ki, miqo min abun wayata ki kiramin Baban naku"

Hannu na rawa jiki ba kwari, ta ja jikin ta zuwa inda ta daga leda ta saka sim din, Kaka Fatu mamakin Zeenat ya Mata yawa, tana kallo ta hada wayar, sannan ta Fara Kira, amshewa ta Yi, ta Kara a kunnen ta, cikin sallama Baban Zeenat ya amsa hayaniya mutane ta Yi yawa, Dan har yanzu ba a tattafi ba daga wajen daurin auren.

"In kun gama hidimar daura auren, Ku Aiko mota a zo daukan amarya anan, Ina jiran ku,.......to sai kun zo"

Riqe wayar ta Yi, Baban su Zeenat kuwa bakin shi Kamar zai tsage Dan farin ciki, Nan da Nan ya ja 'yan uwan Qaseem ya sanar da su, kowa ya Yi farin ciki, a qalla kowa ya San ba wani mummunan waje ta tafi ba, Qaseem da ke cikin baqin ciki, dik da ya San ba ta son shi, sai da ya murmusa, haqoran shi suka bayyana, sannan ya Yi hamdala, ji ya ke Kamar ya tafi ya dakko ta ya dawo da ita, Kar ta tafi wani wajen.

Matar Baffa Nura da Yayar Umman ta Mai suna Atika su ne za su dakko ta, ko Umman bai sanar wa ba, Dan ya San halin ta, tana iya fadawa Mama, in ko Mama ta sani sai kowa ya San Zeenat guduwa ta yi da, abokin Qaseem Haruna shi Baban Zeenat ya ba wa motar shi Dan ya dakko ta, domin in shi ya je da kan shi, ya San da tabo za a Kai ta gidan miji, and he don't want that, a sace suka bar gidan, ba Wanda ya San fitar su, suka shige mota, sai Panda.

'Yan jere har sun dawo, suna ta yaba qoqarin da mahaifin Zeenat ya yi, tunda dakin guda Daya ne, Kuma ba wani babba ba, sai ya sai Mata Kaya masu tsada, aka hada Mata daki Mai matuqar kyau, kujera daya dakin ya dauka, bayan gado da wardrobe da side lockers, sai kayan girki irin su tukwane, non stick da gas madaidaici, qasan floor din kuwa carpet ne Mai laushin gaske aka shimfida Mata, labulaye masu kyau da tsada, dakin 'yar gata dai, dik da kayan kitchen din ta ba su da yawa, Amma fa suna da tsada, dik Wanda ya gani, ya San mahaifan ta sun Yi qoqari.

Masu jere sun yo vedio sai nunawa mutane su ke, ana ta yabawa, ana Sanya albarka, budar bakin Mama da ta gani sai cewa ta yi.

"Ohhhh ni Sa'a, daki Kamar akurkin kaji, wajen ai ya matse, wasu kayan ma lalata su za ai, Nan ba da jimawa ba, tunda ba su Dace da irin gidan ba"

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now