A kwanakin da suka rage, kowa ya ga yanda Zeenat ta sauya sai ya yi mamaki, hakan bai Yi wa mama dad'i ba, ta so a ce Zeenat ta ci gaba da rashin mutunci, ba ribar da za ta ci, amma hakan na Mata dad'i.
Yau da safe Zeenat ta tashi cikin farin ciki, ta Sha wankan ta, ta Sanya kayan ta masu kyau, sannan ta shiga dakin Umman ta, zaune ta gan ta tana qirga robobin da za su yi amfani da su domin ba wa baqi abinci, da sallama ta shiga ta zauna gefen Umman nata,
"Umman mu Ina kwana,"
"Lafiya qalou Zeenat, kin tashi lafiya?"
"Lafiya qlou,"
"Kina buqatar wani Abu ne?"
"Ehh Umma, na ga jibi ne bikin, shi ne na ce, ummm, dama immm, in akwai Dan kudi, ki bani, zan je gyaran Kai"
"Ohhhh Zeenat ba ko dan Jin kunya, da ki na ta Baki so, ba ki so, yanzu dai ga shi Nan, da Kika kwantar da hankalin ki, Dan Allah ke ma Baki fi Jin dadin ran ki ba? Allah ya Miki albarka, ke ma ya Baki Wanda za su maki biyayya,Allah Kuma ya baku zaman lafiya, da zuri' dayyiba, na ji dadin sauyawar halayen ki, a da Ina damuwa, saboda qin daukan dik wata tarbiyya da na ke baku, ashe akwai ranar da za ki faranta min, Allah ya faranta maki, ya qara shiryar min da ku, da sauran yaran musulmi Baki daya"
"Ameen Umman mu,"
Shiru ta yi, ta na jiran Umman na su ta Bata kudin, ta na nan zaune, har Umman ta Gama abinda za tai, jakar ta ta bude ta dakko dubu uku ta miqa wa Zeenat ,amsa ta Yi tana ta godiya, sannan ta fita daga dakin,murmushi ta juya ta Yi wa Umman nata, sannan ta fita, duba kudin ta yi ,ta soke a jikin ta, saboda Kar kowa ya zarge ta, ta dau mayafin ta, da takalmin ta ta fita, Zulfa'u na ta cewa za ta raka ta, amma Tai Mata banza ta fice, tafiya ta fara tana waiwaye, cike da farin ciki, sai da ta ga tayi Nisa sosai da gidan su, ta tsaida abun hawa, ta ce ya Kai ta tashar mariri.
Nan ya dauke ta suka Kama hanya, zancen zuci ta Fara, tare da qunshe dariya.
'Sai ku aura wa Qaseemun naku wata Zeenat din, ba dai Ni ba, Kaka Fatu ga ni nan zuwa, yau ki na da babbar baquwa'
Sun Isa tasha lafiya, motar da za ta Kai ta qauyen Panda ta samu, ta shiga, bayan wasu lokuta, motar ta cika, suka dau hanyar garin panda, garin fulani,😍.
Koda ta Isa a bakin titi aka aje ta, ta shaqi iskar garin, ta saki murmushin Jin dadi, ta san Nan ne kawai babbar mafitar ta, a qafa ta Fara takawa zuwa cikin garin, ta gaji liqis ga uwar yunwa tana ji,ta yi hamma ta fi qirga, Dan ko karyawa ba ta yi ba, Masu awara ne da gyada, da chofe, suke wucewa Dan zuwa kasuwar qauyen, wani yawu Zeenat ta hadiya ganin awara sai zufa ta ke, Kiran yaran ta yi, ta siyi ta nera dari, sannan ta basu kudi, suka Bata canji, suka tafi, qasan wata bishiya ta zauna ta ci ta yi nak, sai shan yaji ta ke, sai da ta huta sosai sannan ta miqe ta Kade jikin ta, sannan ta shiga gari.
A qofar daki ta ga kakar tasu ta na alwalar azahar, sallama ta doka, sannan ta shiga, tare da murnar ganin kakar su.
"Ah ah ahhh mutan kano, ke ce ke tafe da ranar nan,"
"Eh ni ce Kaka Fatu,'yar tsohuwa"
"'yannema, Ni din har wani tsufa na yi? Amma zeenatu me ya kawo ki garin Nan, gobe na ke son na tafi fa, ba Dan masassara da ta Kama Ni ba, da na bi matan Nura, ai da tuni nima Ina can,"
"Ai shi ne dalilin ma zuwa na, saboda an daga auren, saboda iyayen shi Qaseem din ne suka roqi Baba hakan, to saboda surutun mutane, suna ganin Kamar Baba na bai da kudin Yi min kayan daki, shi ne su ka ce na taho Nan da wata Daya za a Yi bikin sai mu tafi tare,an jima sai ki Kira baba, zai qara Miki bayanin komai"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...