Cikin Zeenat ya gota wata takwas, da kwanaki, Kaka Fatu ta zo daga panda, ta yi shawara da iyayen Zeenat akan ta je gida domin ta haihu a can, in ya so bayan haihuwa, in an gyara ta, a maida ta Kamar sabuwar amarya, Baba ya yi iya qoqarin shi ya Hana, haka ma Ummaa da mama, Dan a cewar Mama takura musu kawai za ayi, kalen Kaka Fatu ta dawo gidan da Zama ne, ita kuwa ta tsani abinda zai hada ta Zama da suruka gida daya, da kyar aka tsaida matsayar Kaka Fatu za ta je ta roqa, ita da Atika, da matar Baffa Nura.
Innaa ta so ta hana, Qaseem ya nuna Mata ba komai, gwanda ta tafi, tunda ita ma Zeenat ba kyale ta tayi ba, ta na iya zuwa haihuwar ta masu rashin mutuncin nata, bayan tattaunawa tsakanin Innaa da Qaseem, suka koma, wajen su Kaka Fatu, suka sanar da su amincewar su, Qaseem da kan shi ya shiga ya Fara hada Mata kayan ta, Atika da Kaka Fatu sai tausaya mashi suke, matar Baffa Nura kuwa na Taya shi murna, domin dik iskancin da ta ke suna Jin labari, ta wajen Zulfa'u ,ta na kwance gimbiyar, ta na jiran su Kakan su shiga wajen ta, in sun Gama da munafukar surukar ta,in ji ta, Dan ta San za su Mata munafurci.
"Malami Meye ka ke taban kayana? Ka na wani fito da su,"
"Yau ranar farin ciki ce a gare ki Zeenat,za ki koma gida domin ki haihu, wannan shi ne abinda Su Kaka Fatu, suka zo roqa a wajen mu, na San za ki matuqar farin ciki shi ya Sa zamu bar ki zuwa"
Durowa ta yi daga gado cikin zumudi, da Jin Dadi,
"Da gaske ka ke, ko Wasa?"
"Na taba Baki izinin zuwa gida? Da gaske na ke man, tashi ki sauya kayan ki"
Da kyar ta daddafe gado ta miqe,shi ya Taya ta sauya kayan ta, ko musu ba ta Masa ba, kwalla ya ji ta taru a idanun shi,ya Sa hannu ya share, da kallo ta bi shi, sun dade suna kallon juna, Wanda ya kasa gane Meye a fuskar ta, shin ta na son shi kuwa? Ko daidai da kwayar zarra ne? Inaa bai ga alama ba, a idanun ta, sai ma wani Abu da ya hango, na murnar rabuwa da shi da za ta Yi,wani Abu Mai tsini ya ji ya soke shi, saboda bacin Rai, kauda kan shi ya Yi, ya miqa Mata dankwalin kayan ta, ya fita ya bargidan dika.
Nan su Kaka Fatu suka shiga suka ga kayan ta a hade tsaf, ta shirya sai tafiya, fitar da kayan suka yi, suka ja qofar, sanan suka dau hanyar fita, Zeenat na gaba, Kaka Fatu ce ta daka Mata tsawa.
"Ke ba ki da hanKali ko? Shin abinda aka koya maki kenan a gidan KU, wato rashin tarbiyya? Yanzu xa ki tafi ba ki San ki je ki wa Innar taku sallama ba? Haihuwa za ki, ba Mai tabbas a haihuwa, ko a mutu ne, ko a yi Rai,"
Tana turo Baki, da qunquni ta nufi dakin Innar, Nan suka hadu da ita, itama ta na fitowa, ledar hannun ta ta miqawa Zeenat ,kayan jarirai ne, unisex da man shafawa seti, da sabulu, da yar safa, da kwalli, miqa Mata tayi, fuskar ta dauke da murmushi, ba ta so Zeenat ta tafi ba, a ganin ta dik abinda iyayen ta za su Mata ita ma za ta yi Mata, sannan a wajen ta zai Zama Kamar gazawa ace surukar ta ta tafi gida haihuwa, me ta ke yi ita?
"Ga wannan, an sanyawa jariri ko jinjira, Allah ya sauke ki lafiya,, Allah ya Sa k haihu cikin sa'a, Allah ya Sa ki haifi abinda musulunci da musulmai za su yi alfahari d samuwar shi/ta a duniya" (Addu'a ga masu cikin dik duniya, Allah sauke ki lafiya)
Cikin zumburo Baki da qosawa ta ce,
"Ameen, mu min tafi"
"To Zeenat ai Kamar yau ne, da kin haihu, sai ki ga lokaci ya yi na dawowar ki"
Daidai Nan Qaseem ya dawo, domin har ya fita, zuciyar shi, ta Fara azalzalar shi ya dawo su yi sallama, Dan haka ya nemo mai adaidaita suka taho tare, sake gaida su Kaka Fatu da ke qofar gidan su na jiran Zeenat ya yi, sannan ya shige ciki, daidai lokacin kuwa Zeenat ta dafe qugu, ta kalli Innaa a shege, ta ce.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...