Baffah Nurah ne ya tashi cikin hade fuska, da qarfin hali, ya nuna Zeenat da yatsan shi na dama, sannan ya ce,
"Ke ba na son shashanci, me ye haka ki ke wa mutane magana cikin daga murya, wa ki ka ji ya yi maganar suhailah da Qaseem"
Har yanzu ba ta yi sanyi ba akan bacin ran da ta ke ciki, sai ma qara hasala da ta yi, jin za a raina mata wayo,
"Yanzu na ji Kaka na ce maka Umman mu ta yi waya ta sanar da cewa suhailah ba ta Jin Dadi in ji Qaseem sannan ku ce ban ji ba?"
"To tuhumar mu ki ke da qarya kenan? Da aka ce ba ta da lafiya inji Qaseem kin ji an ce mi ki matar Qaseem ce? In matar Qaseem ce kin isa a boye Miki ne? Wa ke tsoron ki, ya ana magana yarinyar nan ki na neman yi wa mutane rashin kunya, kin san dai Ni ba Yaya Sule bane, casa ki zan mara kunyar yarinya kai"
Da jin Yanda Baffah Nurah ke magana, ta san ta matsa zai kai mata hannu, saboda rai bace ya ke magana, sai ta fara kokonton saurin yanke hukunci da ta yi, wataqila akwai wani dalilin da ya sa Qaseem ya ji labarin ya sanar, amma me zai kawo maganar Qaseem da suhailah, dukan goshin ta tayi tare da rintse ido, kan ta ya kulle mata, ta kasa hada zaren maganar da kyau.
Kaka Fatu ce ta ce,
"Zeenat a gaskiyar magana har yanzu ki na da gyara, ba ki san me ne ne ladabi ba sam, in so ki ke ki ji mijin da mahaifin ku ya zaba mata bayan abinda kikai a gidan miji ya janyo masoyin ta ya guje ta ai sai ki zauna cikin kwanciyar hankali ki nemi sani,ba ki samu a gaba kamar yaran ki ba"
'Da jin yanda Kaka ke maganar an qi auren suhailah saboda ni tabbas sai an min cin mutunci kafin a sanar da Ni mijin suhailah,'
"Kaka basshi kawai, ba sai na ji ba, ku yi hakuri, na zaci miji na ta aura tunda dama ita kullum sai ta min surutai akan zamana da shi"
Baffah Nurah ne ya kalle ta sannan ya karkata kan shi gefe ya ce,
"Saboda ta fiki nutsuwa ba, ta san haukan da ki ka dinga yi ba daidai bane"
Qunquni ta fara sannan ta fice daga wajen, ajiyar zuciya su Kaka fatu suka sauke kusan a tare, Baffah Nurah ya kalli Kaka ya ce,
"Ni fa ban ga amfanin boye mata ba, dan ba tsoron ta muke ji ba, ita ta haife mu ko mu muka haife ta, yarinyar nan an bata miji, ta wulaqanta shi, dan an bashi qanwar ta kuma sai a boye mata? Me ta isa ta yi?"
"Kai dai Nurah a bar maganar, wannan yarinyar mai danyen kai kamar danyen tuwo, in ta sani rashin mutuncin da za ta yi sai ta zubar mana da mutunci anan, gwanda in ta koma can ta ji, dama sun saba, nan kuwa mutuncin mu riqe ya ke, ba wanda ya taba jin matan ka sun daga maka murya balle yaran ka, ba wanda ya taba daga min murya ko ya ji na daga ma mahaifin ku murya har ya bar duniya, dan haka ba zan bari ta wulaqanta mu a nan ba, akwai lokacin da za ta san komai, ya na nan tafe"
"Allah ya kai mu, bari na tafi majalisa, daga nan na wuce masallaci"
"To Nurah, sai ka dawo, amma da za ka bi shawara ta da ka hakura da majalisar nan, kullum da ka dawo kasuwa can ka nufa, ka wuni ba ka gida tun safe, baka zauna da iyalin ka kaji damuwar su ba sun ji taka, matar ka in ka yi hira da ita lada za ka samu, a can kuwa banda zunubi ba abinda ku ke kwasar wa kan ku, in waccan ta wuce ku kalle ta, ku yi gulmar ta, in wannan bai zo ba ku kasa naman shi kuna dauka kuna taunawa, Nurah ka wa kanka fada"
Sosa kai ya yi, sannan ya sanya takalman shi,
"To kaka watarana sai labari, in ka zauna a gidan ne ba wasu kalamai masu dadi, daga a kawo qarar wane sai qarar wance, kin san yaran nan ba nata bane ita daya, duk sanda muka zauna ta dinga kawo qorafin wasu yaran, kinga dole in dau mataki kar ta ce Ni nake basu damar raina ta, ga yawan bani bani, wataran haka nake fita ba ko sisi duk ta amshe,"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...