Ba Nawwarah kadai ba hatta Uncle Ja'afar maganar ta taba shi, amma bai da ikon magana, balle ya hana, tambaya daya ya mata shi ne,"Da wa za a hada ta auren tunda ba ta da manemi?"
"Ita ko ta ke da maneni, ba ga Aqilu ba? Yaro mai hankali, mai mutunci, ya na da sana'a kala kala. Ya iya gyaran wuta, ya iya kafinta, ga kasuwa ya na bin ka ka san amanar shi, kullum yabon shi ka ke"
"Haka ne, ina iya aurawa 'ya ta ta ciki na Aqilu, saboda nutsuwa da hankalin shi,amma mutane za su ga mun aura mata maraya, mara kowa da kowa, ba za a zage mu ba?"
"Ina ruwan mu da mutane? Zaman su muke? Ko in 'yar su ce ba za su aura mata miji na gari ba?"
"To mu dan bari ko sha hudu ta cike tunda sauran watanni biyu zuwa uku, kafin nan mun taimaka masa ya kammala ginin shi, kuma mun sanar da shi qudirin mu, ko ya kk gani?"
Ta so a yi auren su zauna a gidan haka, dk da ba a qarasa ginin ba, ita dai kawai a bar mata gidan ta, ranta bai so ba aka bar shi sai sanda Nawwarah ta cike shekara sha hudu.
Lokacin da aka sanar ma da Aqilu, duk da bai taba ganin Nawwarah ba zuciyar shi ta amince da hadin, ba shi da kowa, tun ya na qaramin yaro sosai aka kawo shi almajirta, har ya girma ba mai zuwa masa a dangin shi, malamin shi da aka kawo shi wajen shi tun ya na qarami ya rasu, ko sunan garin su bai sani ba, (iyaye na birni in kun san mutan qauyen dake kai yara almajiranci, ku n qoqarin wayar musu da kai akn illolon da ke ciki, ba sai yaron ka ya br gabn ka bane zai karatu).
Aqilu yaro ne Baqi matsakaici a tsaho da jiki,ya na da doguwar fuska mai dauke da saje kwantacce, duk inda Aqilu ya fito da alama gidan fulani ne, saboda ya nayin sumar kan shi baqa suduk irin mai cikar nan, in yayi aski har wani layi layi take zanawa akan shi, baqin shi irin na mutanen Katsina, baqi mai kyau da daukan hankali (My respect mutan KT wajen Kyau ba ku da tsara).
Aqilu mahaddacin alqur'ani ne, kuma ya na da ilimin boko amma iya matakin sakandire, ya iya sana'o'in hannu kala kala, ya na noma, ga gini ya na yi, ya yi nisa, an rufe amma ba a qarasa filasta da simintin qasa ba, balle a kai g fenti,a hankali ya ke ginin, da ya samu kudi masu dan kauri zai ci gaba, har da shi ake ginin, saboda ya iya gini,kusan sana'o'in hannu daidai ne Aqilu bai iya ba, ya na da sauqin hali, amma ya na da fushi, musamman a inda ya san ya na da gaskiya, in Aqilu ya tsani abu, to ya tsane shi kenan, ko sunan abun ba yason a ambata, in kuma ya na son abu, quda ba ya son ya taba abun, ya na da saurin Sauka in ya yi fushi, kuma ya na da yawan fara'a, yawan fara'ar shi ba ya hana da an bata masa ya daure fuska kamar bai taba dariya ba, babban abinda ya fi burgewa a rayuwar shi shi ne riqo da addini, gaskiya da riqon amanar shi, Uncle ya sha manta kudi a shago, ko ya zubar ko ya aike shi ya rago canji qarami wanda in ya riqe ma ba za a gane ba, amma sai ya bada kudin nan, daidai da nera daya bai ta ba ci na haramun ba, ya na da matuqar kulawa, wannan shi ne Aqilu.
Nawwarah ta ci kuka ta godewa Allah, an zaba mata miji ba ta san shi ba, ga shi da qananan shekarun ta za a aurar da ita, an katse mata duk wani mafarki da burin ta na rayuwa, anya ba zata gudu ba?
'Na gudu na je wajen wa? Ai gwanda ma nan su na so na sun riqe ni, sauran dangi da suka guje ni fa? Momma na har yau ba ta waiwaye ni ba,ina kyautata zaton ta daina so na itama, ta manta da ni tunda ba mu hada alaqar komai ba'
Kuka ne ya ci qarfin ta har ta na shidewa, uncle ne ya shiga dakin,ya zauna a gefen ta, shiru ta fara yi tare da share hawayen ta, gaishe shi ta yi ya amsa, sannan ya kalle ta cike da tausayawa,
"Nawwarah ki yi hakuri da yanda rayuwa ta zo miki, kar ki damu kan ki akan zabin da muka miki, na tabbata ba za ki wulaqanta ba, na san wane ne Aqilu, zan bashi dama ya zo ya gan ki kamar yanda musulunci ya ce, wannan doguwar soyayyar ta zamani ni dama gaskiya ba na son ta, yawan bawa samari da 'yan mata damar yin shekara da shekaru ana nema, tare da yawan haduwa wasu har da zuwa unguwa, ko a shiga soro ko a je gidan qawaye a yi zance duk su ke kawo lalacewa, da gina neman auren akan haram, amma iyaye su ke da haqqin nemawa yaran su aure, ka ga diyar abokin ka ko yaron maqocin ka, su na da hankali nemar wa naka,ku basu dama su hadu a inda kowa na iya ganin su tare da dan rakiya, haka islam ya ce, in sun ga juna sun amince da junan su, shi kenan, a sake bincike ta kowanne bangare, in an tabbatar da nagarta yaro da yarinya da tsatson shi sai a fara shirye shiryen auren, kafin aure in ana ga ya cancanta su sake haduwa to sai a bar su su sake hduwa, amma ba su kebe ba,daga nan har a daura musu aure cikin tsafta, kinga Nawwarah Aqilu yaron kirki ne, Auntyn ki ba ta zaba maki shi dan wani abu mara kyau ba, sai dan sanin zai riqe ki amana ko bayan ran mu, dan haka kar ki bata ran ki, ki share hawayen ki, in Allah ya kawo shi za ki ga ni, da kin ji bai maki ba, ki sanar da ni"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...