"Babes pls ki hakuri ba yanzu za ki tafi da ita ba, ki bari jibi da kai na zan zo na dauko ta na kawo maki ita, kin ji?"
Hawaye ne ke zuba a idon Zeenat sosai, ji ta ke kamar in ta tafi ta rabu da Fateema kenan, da kyar da sidin goshi ta hakura, sai da Kaka Fatu ta shige gida suka rufe qofar, ta qaraci kukan ta da buga gidan ba wanda ya kula ta, a lokacin Hasheem ya kai iya wuya da haushi da takaicin Zeenat, amma ya danne bai nuna mata ba, sai ma lallashin ta da ya dinga yi, tun daga sannan ya tsani Fatee, ba ya son ma a kawo ta inda ya ke, kuma ya daukar wa kan shi alqawari Fatee ba za tai zaman gidan shi na dindindin ba, bai qi ba ta je tai hutu ta tafi.
Waleeda na mota ta na jiran su, masu ganin gidan Amarya duk sun yi gaba, bayan ya saka ta a mota ne ya shaqi wata iska ya furzar,
'Zan fanshe wannan iskancin da ki ka min ne,kin batan lokaci wajen awa daya ana abu guda'
Shiga ya yi dauke da murmushi, sannan suka dau hanyar gidan, Zeenat na ta kuka, da share majina da tissue din da ke cikin motar.
Ko da suka isa qofar gidan, Zeenat ta daga kai za ta zari tissue, sake ware ido ta yi, nan ina ne? Da sauri ta kalli Hasheem, wanda ya sake wani qayataccen murmushi na isa da nuna shi wani shegen mai kudi ne, tsayawa sukai a bakin qofar gidan, ya bude ma Waleeda, ya ce,
"Dear shiga gida, ni da Momman ku za mu je siyo wani abu, na yi mantuwa kin ji, ki samu Hajiya ita daya ki sanar da ita, in mun yi dare sosai kawai ta sa a rufe gidan, ba yau zamu dawo ba, ok?"
"Ok Dad, byeee"
"Byee baby"
Sauka ta yi ta tsaya bakin gate din madaidaici mai tsananin kyau, sai da ta danna wata qararrawa sannan aka bude mata ta shige, Hasheem ba qaramin gyara gidan ya yi ba, da da ya boye auren shi ko mai gadi babu a gidan, shi ke bude ma kan shi kuma ya rufe da kan shi, makulli da komai na hannun shi, sabanin yanzu har da mai aiki ya sa Hajiyar shi ta samo masa daga Panda, mai suna Rabi, ga mai gadi Lawan ya samu shi ma fullo ne daga Panda, Lawan har diploma gare shi bangaren computer, ya masu alqawarin samun albashi mai tsoka, in suka tsare aikin su yanda ya dace, ya musu gargadin sa ido, da gulma, dik da cewar ya yi sa'ar samun mutanen kirki, dan kuwa Hajiya mutuniyar kirki ce, mutanen da ke kewaye da ita da dama mutanen kirki ne, shi ya sa samun irin su Rabi da Lawan bai mata wahala ba.
"Ina za mu je?"
Cikn dasasshiyar muryar da ta sha kuka ta qoshi Zeenat ke tambayar Hasheem,
"Za mu je Hotel din......ne, abokai na 'yan siyasa sun hada mana party, ni ba na son ma zuwa, amma kin san abu in ya hada da politics sai ka kare kan ka wajen mutanen da ka ke hulda da su, ba dan haka ba, ba abinda zai kai ki wajen nan"
Zeenat kallon shi take dan ta tabbatar da gaskiyar shi, tabbas ba ta ga alamar son zuwa wajen ko zumudin zuwa ba,hasali ma kamar ran shi ba ya so, dan haka sai ba ta sake magana ba, jakar hannun ta ta bude ta dakko powder, ta shafa, ta saka maskara, ta gyara fuskar ta sosai, sai ga ta ta fito fess, wani material ne mai dan karen kyau a jikin ta, kalar purple da ratsin golden, da shi aka mata dauri mai kyau, sake gyara daurin ta yi, sannan ta fesa turare, ta kame a kujera,Hasheem gaba daya ji ya ke anya ba zai zagaye partyn nan ba ya wuce dakin da aka tanadar masu kawai, wani irin kishin ta ne ya kama shi, ganin yanda ta yi kyau na ban mamaki.
"Ke kuma me ne ne na kwalliyar, har da fesa turare, na fada maki 'yan siyasa ne mutanen nan, ba kowa ke da imanin ganin mace ya kyale ba"
"So?"
"Ai ba sai kin yi kwalliya ba"
"Kai ka ke ganin haka, so ka ke a raina ka, a ga matar ka wurjanjan, na sha kuka ko? Fuska duk ta kwabe, yanzu na tabbata in ba kudi ba ba wadda zata nunan komai a wajen,"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...