Ganin tashin hankali kwance a kan fuskar ta ne ya sanya shi zama sannan ya tausasa kalaman shi,"Nawwarah sharadi na shi ne, za ki yi karatu, har ki kai wani matakin da za ki zama wata a Nigeria, ko a duniya,in kuma Allah bai sa za ki daukaka ba, ina son ki yi ilimin da za ki yaye wa kan ki duhun jahilci, sharadi na biyu shi ne, ba zan yi tarayyar aure da ke ba har sai kin kammala Secondary din ki, zan je da kai na na roqi azziqi a barki ki ci gaba da karatun ki, sharadi na biyu, ba na son ki dinga yawo ba mayafi in ina gida, kuma ba na son ki na shiga daki na, ni ma ba zan shiga naki ba, kowa ya tsaya a mazaunin shi, sharadi na gaba shi ne, ban yarda ki je gidan Alhaji ba tare da ni ba, kuma in matar Alhaji ta zo, ban amince ki shigar min da ita daki ba,ki shimfida mata tabarma a waje, komai zata fada ta fada a nan"
Da sauri Nawwarah ta daga kai ta kalle shi, tabbas ta samu kwanciyar hankali, da jin sharrudan shi masu kama da umarni, ita gaba ta kai ta, kuma hakan na nuna zai kula da ita, amma umarnin qarshe gaskiya ba mai yuwa bane, ko ma mene ne, bai kamata ya ce kar ta bar Zaituna shiga daki ba, duk lalacewar ta ita ce sanadin auren su, bai kamata su mata butulci ba, me ye a dakin nasu ma da zai ce kar a bari ta shiga? Bude baki ta yi da nufin yi mishi magana akan hakan ya daga hannu ya dakatar da ita,
"Sharadi na gaba, ba na son innai magana ki min gardama akai, daga nan har zuwa sanda za ki kammala sakandiren ki, a lokacin kike da 'yancin yi da fadin duk abinda kk ga dama, amma a yanzu ki dauke ni a matsayin yayan ki, mai zartarwa mai kuma hani a kan ki"
Daga kai ta yi tare da hadiyar wani abu mai kama da tsoro, yanzu ya xata yi ta hana Zaituna shiga dakin ta? Gaskiya ya dora mata babban aiki akan ta, dan haka addu'a ta dinga yi kar Allah ya bawa Zaituna ikon zuwa gidan.
*****************************
Sai da Zeenat ta qara kwana uku sannan ta sake zuwa gidan Nawwarah, ta zo lokacin Nawwarah na baccin rana Aqilu ya tafi kasuwa, domin ba ya zama a gida sabida ba ya son abinda zai sa shi karya qudirin shi akan Nawwarah, ya san tarihin ta a wajen Alhajin shi, dan haka ya ke tausaya mata, gani ya ke shi da ita ba su da banbanci a rayuwar su na maraici, ya na ganin abinda Zaituna ke mata in ya kai aike gidan,tun kafin Alhajin ya same shi da maganar auren ta ya ke tausayin ta, duk da bai taba kawo maganar aure ba a ran shi, shi ya sa ya na samun damar auren ta ya karbi tayin da aka masa, ya ke da manyan burika a akan Nawwarah na ganin ta zama wata a qasar nan, ko kuma ta cire duhun jahilci, dan ya san Zaituna ta hada auren su ne dan kar ta ci gaba da karatu, kuma ta na masa kallon jahili da bai san dad'in ilimi ba, ba lallai ya bar Nawwarah ci gaba da karatu ba, to zai bata mamaki kuwa.
Nawwarah murna kamar ta taka rawa, tunda ta maqale Zeenat, Zeenat motsi da kyar ta ke yi, Fatee na ganin ikon Allah an kwace mata fada, suna cikin hira,Aqilu ya dawo, hannayen shi riqe da ledoji, Nawwarah zama ta yi ba ta je amsa ba, dan ya na daga abinda Aqilu baya so, ita kuwa duk abinda ba ya so ba ta yi a 'yan kwanakin da sukai, Zeenat ce ta ce ta je ta amshi ledar hannun shi mana,dan a take ta tuna zaman ta da Qaseem, Aqilu ne ya yi murmushi mai kyau, sannan ya ce,
"Ah ba sai ta tashi ba ma, sannu da zuwa, kun zo lafiya?"
"Lafiya qlou, ya kasuwa?"
"Alhamdu lilLAAH"
Fateema ya kira ya dan mata wasa, sannan ya sa hannu a aljihu ya miqa mata ledar sweet da ya siyo wa Nawwarah.
"Allah to ya sanya albarka, Allah kuma ya baku zaman lafiya, Allah ya kiyaye sharrin shaidan a zaman ku, dan Allah Aqilu ga amana nan, kar ka bari kowa ya cutar min da ita, kar ka cutar min da ita, inna tafi ba zan dawo ba sai mun kammala jarabawar qarshe da ke gabana, ina fatan in dawo in tadda ta cikin walwala, Aqilu Nawwarah marainiya ce, in ka kula da maraicin ta sai Allah ya saka maka da ladan mai kula da maraya, sannan ga ladan kula da iyalin ka, ka ga kenan daukaka ta same ka a wajen Allah, in ta maka laifi dan Allah kar ka tsane ta, ko ka hantare ta, ka zaunar da ita cikin lumana ka sanar da ita kuren da ta yi, ke kuma Nawwarah ki kiyaye duk abinda zai bata ran mijin ki, komai qanqantar shi, daga qarami ake tadda babba, tun ki na bata masa rai ya na hakuri za ta kai lokacin da zaki fita a ran shi, rashin iya magana na fitar da soyayya da mutunta juna, kar ku na yabowa junan ku magana yanda kuka ga dama, Nawwarah ba zan gaji da nusar da ke ki dinga tuna rayuwar da na yi ba, da irin sakayyar da na gani, ki guji maimaita abinda na yi na fada halin quncin rayuwa na rashin abokin tarayya, ki riqe mijin ki da amana da so da qauna,"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...