ALBASA BATAI HALIN...6

414 43 10
                                    

Cikin bacin rai Qaseem ya tashi, amma Innar shi ta riqe qafar shi, tare da daga masa hannu, cikin murmushin da har zuciyar ta, ta na ganin yarinyar Zeenat , in ba yarinta ba, me ne ne hakan? Ita a dole sai ta bata musu rai , in ya ji haushi ya sake ta, lallai za su nuna mata me ake kira da hakuri.

"Tashi maza ka tafi dakin matar ka, in da ka na kwana anan, yanzu ka yi matar da za ka kwana da ita, dama shi d'a, bayan ya bar qarqashin kulawar uwa, yana komawa qarqashin kulawar mata ne, Allah ya muku albarka, maza ku tafi, ga shayi nan na sa Bilkisu ta dafa maka kan su tafi, ku dauka ku wuce da shi, sai dai ba biredi"

"Dama ta ina za ku yi bread a wannan gidan? Kuma Ni ba d'an wadda na zo kula da ehe, ni ma kulawa na ke nema, dan haka ba d'an da zan kula da shi, gwanda ma ki ci gaba da kula da d'an ki"

Fizgar ledar da kazar ta ke ciki ta yi, ta wuce, ta na tafe ta ji kamar motsin a bu a wajejen dakin su, wani mugun tsoro ne ya kama ta, yawu ta hadiya, ta ja ta tsaya, shawara ta ke, ta ruga da gudu ta koma masu, ko ta yi shahada ta shige, inaa ba ta da wannan kwarin guiwar, ido ta fara zarowa, tare da raba su cikin yanayi na tsoro, gashi ko wayar nan ta zamani ba ta da shi.

Ja ta fara yi da baya, a hankali, dan kar ta janyo hankalin koma mene ya shiga masu daki, ji ta yi ta jingina da abu mai motsi, wata razananniyar qara ta sake, ta qanqame Qaseem, daidai lokacin da ta tabbatar shi ne.

Inna ce ta leqo cikin yanayi na damuwa, sai ta ga yanda Zeenat ta maqale Mata yaro,murmushi ta Yi, ta koma daki, ba Wanda ya San ta fita, balle komawar ta.

Wani irin numfashi ya ja mai qarfin gaske, tare da lumshe idanun shi, jikin ta mai laushi ta ke ta goma mi shi,duk inda hankalin Qaseem ya ke, to fa ya tashi, sake rungume ta ya yi, ya manna fuskar shi a wuyan ta, yana sauke numfashi, bata tashi kula da kuma gane me yake yi ba sai da ta ji ya na matsa mata baya, da hannayen shi duka biyun,tura shi baya tayi da mugun qarfi, sai da ya daki gini, ta bude baki dan zazzage masa ruwan rashin mutunci mage/mussa/kuliya, ta fito daga dakin su da gudu, wata qara ta sake saukewa tare da yadda ledar hannun ta ta cakumi Qaseem a karo na biyu, gaba ɗaya ta raba kan ta da qasa, kyakkyawar tarba ya mata, tare da sake tallabe ta, ya durqusa ya dauki ledar ya fara tafiya da ita, zuwa dakin nasu.

Magen kuwa na biye da su, sai da ya ajiye Zeenat da ke ta rawar jiki, da sauke numfashi tsabar tsoro, sannan ya juya ya kori magen, ta tsaya ta qi tafiya.

"Tiger tafi dakin Inna ki kwana yau, baquwar mu da alama tsoron ki ta ke ji, "

Lumshe ido magen ta yi kamar ranta ya baci, dan ta gane ba zata kwana da shi ba,kwantawa ta yi a wajen,ta kwantar da kan ta a qasa,komawa ya yi, dakin ya ga yanda Zeenat ke zaune cikin matsanancin tsoro.

Murmushi ya yi, a qalla ya samu abinda Zeenat ke tsoro, zama ya yi, ya dauki ledar, ya duba plate ya juye Naman, qamshi shi ya sa magen da ke waje kuka, tana kartar jikin qofar da farcen ta, Zeenat ma kukan ta saka,

"Na shiga uku Ni Zeenat an kawo Ni inda zan mutu, komai na gidan nan ba abun so bane, yanzu fisabillahi me ne kuma na aje mage a gida? Kawai dan a hana Ni sakewa, a gaskiya ni da ka maida Ni gidan mu, ba zan zauna anan ba"

Kuka sosai ta ke, kamar wadda akaiwa duka, cikin Muryar lallashi ya fara magana.

"Yi hakuri Zeenat magen nan ba anan gidan ta ke ba asali, ta maqota ce, amma lokaci zuwa lokaci ta na shigowa, watarana mu kwana, watarana ta je wajen Inna ta kwana, ta fi zuwa in tana jin yunwa, yanzu bari ki ga na bata nama ta ci, tafiyar ta za tai"

Shiru Zeenat ta yi, tana tunani, shin za ta yadda a bawa magen naman ne, ko kuwa? Har ya kai hannu zai dauka ta riqe hannun shi,

"Tsaya Ni zan zaba maka, kafin ka kwashe ka kai mata"

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now