Ta koma gida ta tadda Kaka Fatu na waya da su Umman ta, har ta miqa mata wayar domin su gaisa,amma da ke Zeenat ba 'yar goyo da zani bace ta yi wucewar ta, bayan ta ajiye ma Kaka Fatu takwarar ta, ko da ta isa madafin, kaca-kaca ta gan shi, cikin jin haushi ta fara neman tsintsiya, wata mai datti ta hango yashe a qasa, da ta taba wannan tsintsiyar, gwanda ta ɗora girkin haka, ai kuwa ba bata lokaci ta hasa wuta, da kyar, ido ya mata jawur, hancin ta sai zubar majina ya ke saboda hayaqi.
Ta na gamawa ta kira yaro ya karbo mata kayan miyar tuwon daren, bata bar yaron ya tafi ba, sai da ya taya ta, dakan kayan miyar, harda tankade garin tuwon, ta na yi ta na mita.
"Me ye amfanin ku, in ba a more ku ba? Indai zan yi aiki, to kowa ma sai ya yi"
Har bayan magrib sannan ta kammala, ta debi na su ita da Kaka, ta kwashe musu sauran a wasu ribobi, da kwanuka da ta gani, ta yi tafiyar ta.
Ummalo kuwa na daki, Allah Allah ta ke ta gama, ta je ta kwashi tuwon, qamshin miyar kamar an saka nama,a cewar ta.
Haka rayuwar Zeenat ta ci gaba da kasancewa a qauyen, daga aiki, sai yawo, watarana ta je gidan Atika, watarana ta zaga garin, musamman ranar kasuwa, haka nan za ta ci wanka, ta biya gidan Atika ta dauki diyar ta su yi ta zaga gari.
Baffah bai taba hana ta ba, duk da Ummalo ta so matuqa ya hana ta, a cewar ta, ta na zubar mishi da mutunci a gari, kowa ya ga bazawarar 'yar dan uwan shi ba ta da kamun kai, ya kan ce mata ya zai yi? Komai da suke so Zeenat na musu, so ta ke su maida ta kamar prisoner ?da wannan ya kashe bakin ta, Kaka Fatu ma ba ta hana ta, dan kuwa watarana ma ita ke riqe Takwarar ta, har su je su dawo, sam ba ta son a takurawa Zeenat din.
Zeenat ta samu wata daya a qauyen Panda, a cikin rayuwar da ta ke kira Mara 'yanci, rayuwar takura, rayuwar qauye, talauci da rashin wayewa, dik qoqarin Baffan ta da Kaka, na ganin ta sake, amma ita gani take bata da maqiya bayan iyayen ta, sama da su.
Ta na zaune dauke da Fatee, ta na yanke mata farcen hannun ta, ta yi bacci ta na shan mama, ta ji Kaka Fatu ta na waya, a daki, tare da fadin,
"To inshaa Allahu, za mu zo yau din, Allah dai ya sa lafiya, dan na ji Muryar ka gaba daya ba walwala,........to shi kenan, zan sa nuran ya kawo ni.......to sai an jima, sai mun iso."
Kaka na qoqarin fitowa, Zeenat na qoqarin shiga, tambayar ta ta fara yi, akan lafiya? Ta ji ta na son zuwa Kano? Bayanin komai ta mata, sai ta ji tana son zuwa, kar dai wani abu ne ya faru a gidan,ake boye musu, ta yi ta roqon kaka akan za ta bi ta, amma ta qi, ta Bata hakuri, ta ce ta bari sai ta dawo, in abun ya cancanta ta je,ko daga baya ne, ta je, suna maganar Baffan Zeenat ya shigo, Yayan shi ya sanar da shi komai, dan haka cikin minti goma suka shirya, suka fita tasha, sai Kano.
Zeenat ba ta san me ya sa ba, sai ta ji tafiyar ta su ba ta kwanta mata ba, da da yanda za ta yi sai ta je, ko ba a gayyace ta ba, rashin kuɗi ne kawai matsalar ta.
**************************
Gidan ya yi shiru kamar an yi mutuwa, Muryar mutum daya kawai ke tashi, ta na ta masifa,tare da fadin,
"In kun ga na bari auren nan ya faru ba na numfashi, wanne irin abu ne wannan? A bar mu muji da wannan bala'in da ya sakko mana mana,kawai za a yi mana wannan kwadon, kwadon da aka yi ba a ji dadin shi ba, ya lalata ciki, shi ne za a maimaita, ba zai yu ba, ke kuma munafuka, kin yi shiru, ba ki cewa komai, ko dama son shi kike ne?"
"Sa'adatu, ki rabu da yarinyar nan, Ni ne nan na yanke hukunci,da Ni za kiyi ba ita ba, in ke baki da biyayya kamar Zeenat to ita kamar Sailuba ta ke, in Kuma ki ka matsa za ki sa Ni yanke hukuncin da zai girgiza ki, dan kuwa in wani abu ya faru da wannan auren, na ki auren ma sai ya samu matsala, na fada maki"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...