Kaka Fatu na qoqarin yin magana Suhailah ta shiga ta zauna a gefen ta, sannan ta bude baki cike da ladabi ta fara magana.
"Yah Qaseem dan Allah ka yi hakuri, laifi na ne, ina ganin ruwa a qasa amma na taka, dalilin da ya sa santsi ya kwashe ni kenan na fadi, tabbas mun yi sa in sa da Zeenat, amma Zeenat ba za ta taba cutar da ni har haka ba, i am really sorry"
Hawaye ne ya zubo a idanun ta zuwa kuncin ta,cike da tausayawa Qaseem ke bin ta da kallo ba dan mahaifan ta da ke kusa ba da ya durqusa a gaban ta ya share mata su, sannan ya lallashe ta, cikin murya mai cike da tausayawa ya ce,
"Suhailah kar ki ban hakuri dan Allah, sai ka ce ban san me nake yi ba? Ai tsautsayi na iya faruwa kan kowa,kuma lafiyar ki ta fi min ta babyn da ban gani ba ma,a zato na ko Zeenat ta miki wani abu ne, musamman da na ga yanda ta ke cikin fushi, ince dai ba ki ji ciwo ba? Ki na lafiya?"
Cikin dan murmushin samun nasarar qaryar da tai ta daga kai, tare da sunkuyar da kan ta,murmushi shi ma ya mata. Sannan ya miqa mata Fateema, ta dauke ta, sallama ya ma mutanen gidan ya ce zai dawo ya dauke ta da dare, amma ta roqe shi akan za ta kwana, saboda ba ta jin dadi,
Baban Zeenat da ya kula kamar Qaseem ya fi son tafiya da matar shi sai ya tursasa sai ta bishi, amma Qaseem din ya daure duk da ba haka ya so ba dole ya bar ta kwana.
Hasheem kuwa sallama ya musu shi ma ya ce zai je gidan shi da ke nan kano din, Zeenat na jin haka kuwa wani dadi ya kama ta, wato ma ya na da gida a garin kano? Shi ne ya ke son aje ta a Qauye, ai kuwa bai isa ba, ta na ji su na sallama ta labe, dan ba zata iya fita a haka ba fuskar ta kumbure, da kuka da mari, haka ya tafi ba su hadu ba.
Kallon kallo ne a tsakanin Suhailah da Zeenat, a lokacin da suka hadu a tsakar gida, tsaki mai tsahon gaske Zeenat ta ja, sannan ta tofar da yawu a gaban Suhailah, kauda kai suhailah ta yi kamar ba ta gani ba, ta rabe gefe za ta je dakin Umman Zeenat din,
"Ina zaki malama? Ko ba ku da d'aki ne a gidannan? Ko kuma uwar tawa ma amshe ta zaki kamar yanda kk amshen miji?"
"Zeenat bani hanya na wuce na gama magana da ke akan Yah Qaseem,"
"Ni kuma.ban gama magana da ke ba sai akai yaya?"
"Sai ki ta yi ke daya"
Zagaye ta ta sake yunquri zeenat ta janyo ta ta koma gaban ta, cikin fushin da Suhailah ba ta san ta na da shi ba, ta tura Zeenat baya, ta daku da ginin wajen, sannan ta nuna ta da yatsa,
"Ke Zeenat ki fita ido na na rufe, ba fa tsoron ki nake ji ba, ina dai baki girman ki ne a matsayin ki na wadda ta girmen, amma ba dan ban da bakin kare kai na ba, duk abinda ki ka min yanzu ke ba ki nadama ba? Tuhuma ta ma.kike akan mijin da ki ke fada ki na qarawa kin tsane shi, ba ki qaunar shi? Ya sake ki sannan na aure shi to wanne irin toshewar basira ke damin ki? Shin wai ba wanda za ki aura ki ka kawo ba? Ko shi ma ba son shi ki ke ba wani abu na shi ki ke so? Tabbas da dikkan alamu ke baki san so ba, akan ki na rasa wanda na ke so aka aura min Qaseem, akan ki na rasa gudan jini na dazu dazu, ke wacce iriyar mace ce mara imani? To ina gargadin ki, ki fita sha'ani na kar ran ki ya baci, dan duk wani rashin mutuncin da kk ji da shi kowa ma ya iya,kawai ina diba abinda ya kamata ne, mtsss"
Zeenat fa kamar an kafa ta a wajen, Iyayen su mata har da Kaka Fatu da suka leqo tun tura Zeenat da Suhailah ta yi ba wanda ya ce uffan, saboda ko ba komai Suhailah ta fidda bacin ran da ke ran ta yau, kuma da alama Zeenat ta tsorata.
Suhailah ba ta fasa shiga dakin Umma ba ta zauna, su na tsaitsaye su na tattauna abinda Zeenat din ta yi a tsakanin su,Mama dai nutsuwa ta same ta,dan haka jira take.Umma ko Kaka su yi maganar da ta dace, ita kuma ta yi kawaici.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...