ALBASA BATAI HALIN...31

358 43 8
                                    


Da safe kuwa Zeenat ba ta samu damar tashi sallar asuba ba, saboda bashin baccin da ta ci, tunda ba ta kwanta bacci ba sai wajen 12am na dare, ko da ta tashi bandaki ta shiga ta yo wankan ta, ta goge gashin ta tass, ta taje ta saka kan cikin hula, saboda tsoron kar a gane, (Tsarguwa) sallah ta yi a daddafe, dan wani irin bacci ta ke ji kuma, mai nauyi, ta na idarwa ta haye katifar ta da niyyar bacci, nan kiran Hasheem ya daga ta, idon ta a kulle ta amsa wayar, cike da shagwaba ta ke magana,

"Dan Allah ka barni na yi bacci, na gaji sosai, bacci na ke jiiii"

Turo baki ta yi kamar ya na ganin ta, hango yanda ta ke yi ya ke a zuciyar shi, wata kasala ta saukar mishi, da ta sa ya sake gyara kwanciyar shi zuwa ruf da ciki, shi ma cikin wata murya mai kashe gabban jiki ya ce,

"Habaa Babyn Hasheem kar ki zama raguwa mana? Ke da in aka daura auren mu kwana za muyi mu na farantawa juna rai, da safe mu qara, sannan...."

"Waaa? Tabb ai sai na rasu"

Dariya sosai Hasheem ya ke yi, saboda yanda ya ji da gaske ta tsorata, itan ma dariya ta ke yi, juyawa ya yi ya kwanta, tare da zura hannun shi ta qasan kan shi, daya wayar shi da ya ke chatting ya dauka ya ma qirjin shi hoto ya tura mata,

"Babe duba Whatsapp din ki, na tura maki good morning picture na"

Cikin sauri hannu na rawa ta ce,

"Ok ina zuwa"

Kashe kiran ta yi,ta kunna data, baccin da ta ke ji gaba daya babu shi, ko da hoton ya gama budewa sai da ta ji hankalin ta ya tashi,wannan wanne irin kyau gari Hasheem, da safe ne fa, amma ji wani irin kyau da fuskar shi ta yi, tsabar zaqewa hango su ta yi sun haihu, kyawawan yara ta ke hangowa sun samu, qirjin shi ta ke ta kallo, ta bata cikin kallon shi, ta ga vedio call na shiga, da sauri ta amsa, tare da sauke ajiyar zuciya,

"Gaskiya ka hadu"

Dariya mai qarfi ya bushe da ita, ya na daga abinda ya sa ya ke qara son ta, ta iya yabon halittar shi,

"Koh My Zee?"

"Ba kadan ba, sauran kadan numfashi na ya dauke, i love u my Hasheem"

Ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi, gaskiya ya na son Zeenat sosai, ko dan ta iya soyayya ne?

"I love u My Zee"

Murmishi su kai, sannan ta ga ya gyara kwanciyar shi, tun daga sama har qasa ya fara nuna mata kan shi, kama baki ta yi, ta na murmushi, cikin jin kunya,

"Me ne ne abun jin kunya? Ni fa mijin ki ne, sauran kwana biyu kacal auren mu"

"Ni dai gaskiya ka na ban kunya, zan kashe"

"Tabbb ai kuwa ba ki isa ba,ki gama gani na ki kashe ban gan ki ba"

Ba ta jira ya gama.magana ba ta kashe,.Hasheem kuwa ranshi ya baci sosai, tsaki ya dinga ja, gaskiya za su na samun matsala, bai saba neman abu ana hana shi ba, yanzu sai ya kai duka.

Qara ya ji alamar shigar saqo, ya na dubawa sai ya ga hoto ne Zeenat ta tura masa,da azama ya shiga ya bude, nan da nan ya ga hoton ta ta turo masa na dika jikin ta, har da fuskar ta, murna ya dinga yi kamar yaron da aka bawa sweet mai tsinke.

Kashe datar shi ma ya yi dika ya kwanta ya na ta kallon tsiraicin Zeenat, wanda ke da daukan hankali,duk da ta yi shayarwa amma ba mai cewa ta yi shayarwa in ba an fada masa ba.

Ita kuwa da ta ga ya sauka online sai ta zaci fushi ya ke, kawai sai ta tura baki ta saka kayan ta ta tashi, ta fita daga dakin, zuwa dakin Umman ta, dan gaishe ta,Mama ce da girki dan haka ta na kitchen ta na abun karyawa, sai da ta tsaya ta gaishe ta, sannan ta fada dakin Umman, zaune ta ganta kan sallaya, ta na karanta qur'ani kamar kullum, Fateema na gefen ta ta na wasa, durqusawa ta yi kusa da Fateen ta yi kissing kuncin ta, sannan ta mata wasa, Umma na kaiwa qarshen suratul Noor ta yi addu'a sannan ta kalli Zeenat cike da murmushi, a qalla yanzu ba rashin kunya,ba taurin kai, Allah ya amsa addu'ar ta (Umma kin ban tausayi, ba ki san me ta komawa ba kuma😢 ana maganin qaba kai na kumburewa)

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now