Yau ma Kamar kullum ta tattake qasan doguwar rigar ta, sannan ta Goya hannayen ta a qirjin ta, idan ta ke kullewa a hanKali, Amma ba ta son su rufe gaba daya, tsoro ta ke ji, Kar Qaseem ya nemi wani Abu a wajen ta, she is not ready yet, Qaseem na kula da rashin nutsuwar da ta ke samu, tsakanin shekaran jiya da yau, baccin rana ma da ta yi dazun a cikin tsoro ta Yi shi, tashi ya yi ya zauna, sannan ya shafa kan shi da hannun shi na dama, tare da sauke ajiyar zuciya,
"Suhailah,....suhailah"
Kulle ido ta yi sosai, hannun ta damqe da rigar ta, bakin ta na rawa saboda tsoro, Wai ita a Hakan bacci ta ke,
"Na San idon ki biyu, ki tashi ki zauna za muyi magana"
Cikin turo Baki, ta miqe, ta zauna, ta ya akai ya Gane idon ta biyu? Bayan ba abude ya ke,
"Na'am?"
Murmushi ya yi Mai sauti, duk ya fuskance ta, Amma Bari ya cire Mata tsoron shi da take ji
"Suhailah tsoro na ki ke ji?"
Cikin zaro ido ta ke kada Kai, in fa ya Gane ta na tsoron shi, zai iya amfani da wannan damar ya kusance ta, daga Kai ta Yi, a qoqarin ta na kawar da tsoron ta,
"Hhh haba wanne irin tsoro Kuma, Kamar wani dodo?"
"Exactly , haka ki ka dauke Ni, Ni Kuma ga shi ba na cizo, Ni in ba a cijen ba bana cizo, Kuma ke gashi tun shekaran jiya da aka kawo ki, ki ke gudu na, ki kwantar da hankalin ki, suhailah na Miki alqawari ba abinda zan Miki, sai da amincewar ki, daidai da hannun ki ba zan taba maki ba, sai dai a bisa kuskure ko da izinin ki, kin ji? So ki kwanta ki baccin ki da kyau, bana cizo"
Wata iriyar kwanciyar hanKali ke shigar ta, haka Nan ta ji ta yarda da kalaman shi, domin kowa ya San halayyar shi, shi mutum ne Mai gaskiya, Dan dariya ta Yi qasa qasa, sannan ta ce,
"Yah Qaseem ni fa ban ce kana cizo ba, sai maimaitawa ka ke, da ka na cizo ai da ba zan kwanta a gado Daya da Kai ba,"
"To ai ke din ce, Kamar wata amaryar qauye, ki na ta gudu na, Kamar na ce zan cije ki"
Ita dai kalmar cizon na Bata dariya sosai, Dan haka ta shagala ta na ta dariya, tare da sake jan maganar, ba su San dare ya yi sosai ba, sai da garin dariya ya Danna wayar shi bai sani ba, hasken wayar na bayyana ya miqa hannu ya dauka, ganin time ne ya Sanya shi saurin kwantawa ya rufu ba tare da ya ce komai ba, suhailah na ganin ya kwanta da sauri ya rufu tsoro Mai tsanani ya Kama ta, ya bude Baki zai Mata magana ya fada Mata time ya ja, kawai ya ji ta a jikin shi, ta matse shi sosai, jikin ta na rawa, cikin muryar kuka ta ce,
"Yah Qaseem me ya faru?"
Bai San sanda ya bushe da dariya ba, sannan ya juya, ya janye ta a jikin shi,
"Ke wace iriyar matsoraciya ce wai? Lokaci fa na gani ya ja sosai, shi ne na kwanta, ina so na ce Miki mu kwanta Kar mu makara' sallar asuba, shi ne za ki firgita haka"
Dariya ta Dan Yi cikin Jin kunya, ta ja baya sosai, kallon ta ya dinga yi, cikin hasken fitilar da ya gauraye dakin, kallon gefen ta ya Fara Yana zaro ido Yana nuna wajen, ai kafin ya qarasa Bata tsoron ma da ya yi niyya har ta zabura ta daka tsalle ta dawo gefen shi, jikin ta na rawa, dariya a wajen Qaseem Kamar zai Fado daga gado, ya na so ya yi magana dariya ta Hana shi, ai kuwa ta na gano abinda ya Mata, sai ta Fara kukan shagwaba ta na dukan shi a hanKali, dariyar shi na raguwa Yana kallon yanda fuskar ta ke mishi kyau a cikin hasken, bai taba zaton bayan Zeenat akwai wadda zai ga kyaun ta ba, ganin irin kallon da ya ke Mata ne ya Sa ta sauke hannun ta, tare da sunkuyar da kan ta, kwanciya ta Yi, tare da yin addu'ar bacci, ta shafa, ta rufe idanun ta.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...