ALBASA BATAI HALIN...29

440 43 7
                                    

Zeenat ta ci gaba da harkokin ta, ba ta sake tunawa da wani maganar ajiye Fatee ba, shirye shiryen biki take ba kama hannun yaro, in ta je siyayya ta ga ba kudi, sai ta danna kiran Hasheem, shi kuwa tuni zai aiko wani yaron shi Sadee, ya kawo mata kudi, duk inda ta ke ya kai mata.

Hasheem ne duqe gaban Bokan shi, ya jima a zaune, Bokan na dube dube, ba yan ya kammala ya gyara zama, ya kira sunan Hasheem sau uku, Hasheem ya amsa, ya sake duqar da kai, ko a sallah ba ya qasqan da kai kamar yanda ya yi a yanzu.

"Yau binciken mu ya zo qarshe akan wannan auren da zakai, sai dai akwai wani lamari da ya shige min duhu game da yarinyar nan, ba dan komai ba sai dan yawan addu'a da iyayen ta suke mata, duk yanda na so gano lamarin abun ya faskara, amma albishiri daya zan maka, Zeenatu na dauke da azziqi, auren ta zai sake bude maka hanyoyin samun ka, sai ka yi hakuri da halayen ta,domin na yi bincike akan ta sosai, ta na da danyen kai, ba kadan ba"

"Kwarai kuwa ni shaida ne Malam (Boka), domin yarinyar nan ba ta ji ko kadan,abinda ta sa a gaba shi ta ke yi, ni kuma ka san ina da matsala, ba na son raini, ba na son raini sam,"

"Dole ne ka qoqarta hakuri da ita, indai ka na son ka dawwama da ita,kuma azziqin ka ya bunqasa, ka sani, dole ne ka sake boye kayayyakin tsafin ka, domin rawar kan Zeenatu ba boyayye bane har a dubana"

"To Malam (Boka) zan sake boye su da kyau, ka na ganin zan iya sakin ta gida na yanzu ko? Tunda akwai tabbacin aure na da Zeenat ko?"

"Kwarai ka sake ta, ka sake ta ba matsalar komai"

"To na gode, nasara da sa'a ta tabbata a gare ka....ga wannan"

Kudi ya debo masu yawa ya ajiye, ya yi sallama da bokan shi ya tafi, daya daga cikin halayen Hasheem boyayyu kenan, akan ya samu dukiya komai ma ya na iyawa, komai zai gabatar a rayuwar shi zai je a duba masa ko ya nemi sa'a, shi ya sa ya ke ganin zai iya taka kowa, kuma zai iya samun duk wani abu da yake so a rayuwar shi.

Ko da ya koma gida, ya tadda matar shi na ta zabga tari, saboda ta dora miya, ta ji ta na son ta zaga, sai ta shiga toilte, ba ta zaci z ta jima ba, ta na dawowa ta ga hayaqi ya turniqe ko ina, dan haka ta ke ta zabga tari,numfashin ta na sama sama.

Da gudu ya qarasa shiga gidan gaban shi na faduwa, a zaton shi ko gobara ta hada masa a gidan, ko da ya shiga ya ga me ya faru, kawai ya zari memo a aljihu da biro, ya rattaba mata saki uku, ya miqa mata, sannan ya janyo ta har bakin qofar dakin ta,

"Yau dai burin ki ya cika, zaman ki ya zo qarshe a gidan nan, tattara kayan ki, ke in ma ki na son gadon ga aron waya, kira gida su aiko mota a kwashe kayan dakin nan kafff, kar ki taban kayan babban parlour, ki hada da na kitchen, na san kwadayayyun iyayen ki za suyi murna da hakan,"

"Ah ah ka bar shi. Ai ni sakin nan da ka min ba qaramin abu bane a waje na, na gode maka, Allah kuma ya mana hisabi, ranar da baka da komai, sai ladan ka, in ma ka na aikata alkhairi kenan"

"Iyyyee wato ni kk gaya wa magana yau ko? Saboda na sake ki? Da kyau,maza kwashe ki fita, bari n kira iyayen ki na fada masu ki ji yanda makwadaitan iyayen ki za su saka kuka, da ihu, saboda na saki yar su, ke kuwa sai kin sha duka yau,sannan zan musu albishir su zo su kwashe kayan dakin da na kwanta da diyar su,"

Wani irin qarfi ta ji ya zo mata, ta samu ta zabga masa mari, ta kutufe shi, sai da bakin shi ya tsartar da jini, (a kiyayi macen da aka kai bango) nan fa ta samu ta haye kan shi ta na duka, da kyar ya samu ya bige ta gefe, ya miqe da kyar, babbar rigar shi duk ta yamutse, idanun shi sun yi jawur saboda bacin rai da kuma dana sanin sakin ta haka kawai ba tare da ya koya mata hankali ba, (wanne hankalin banda wanda ta koya tuni na maka duka a yau?)

Hannu daya yasa ya make ta ta fadi qasa ta na kuka, wayar shi ya zaro ya kira mahaifiyar ta, ta jima ta na ringing kafin ta dauka, jin kukan diyar ta ne ya sa ta dafe qirji, gaban ta ya sake faduwa, dama tun dazu take jin faduwar gaba, kar dai wani mummunan labarin ne zai same su.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now