ALBASA BATAI HALIN..35

406 46 7
                                    


Durqushe ta ke a gaban shi, qafar shi na saman cinyar ta, sai raki ya ke, da ka kalli fuskar shi za ka tabbatar a tsorace ya ke, ita kuwa murmushi kawai ta ke zubawa, dan ba qaramin burge ta ya ke ba, in ya na nuna jin tsoron yanke farcen.

"Yah Qaseem, wai a ce ni da nake mace ban ji tsoron yanke farce ba sai kai, gaskiya ka ji kunya"

Shiru ya yi, dan ba ya ko son ya yi magana, gani ya ke kamar in ya yi magana za ta yanke shi, da hannu ya mata alamar ta yi shiru, dariya ce ta kwace mata, daidai lokacin da ta gama yatsan qarshe.

Ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi sannan ya kalle ta, cikin kulawa da so da qauna, tare da dumbin godiya a gare ta, tunda ta zo gidan, ita ce wankin shi, na Innaa, na ta, kullum ba fashi, in yau bata yi ba to gobe za ta yi, dan ma Innaa bata cika bata nata ba, saboda cewa ta ke kayan ta ba su yi datti ba, daga sawa daya in akai wanki ai za su kode, Suhailah ita ke wanke-wanke, shara, da girki, wataran kuma Innaa ta yi girkin, daidai da rana daya bata sawa kan ta bauta take masu ba, ta sawa ran ta bautar Allah take, kuma ko a gidan su ta na aiki irin haka, a babin tunani da hankali ma ya kamata ace ita ke yin komai, tunda Innaa ta manyan ta,ko ba komai gaba take da ita, bai kamata a ce ta na zaune ita ta na aiki ba, maganar girki kuwa, ita kanta tafi jin dadin girkin Innaan, shi ya sa bata taba damuwa ta sawa ran ta, wai Innaar ke abinci ba, Qasheem a kullum ya tashi sai ya ga ta fito da sabon abu da zai kyautata masa shi da mahaifiyar shi, Ko kuma ta sabunta wanda take musu a da, abinda ke sanya shi girmama ta kenan, da ganin mutuncin ta.

Innaa ce ta fito daga daki dauke da dariya a bakin ta, ta ajiye tsintsiya sannan ta nufi wajen zubar da shara, Suhailah ta miqe da sauri dan ta amsa ta zubar, tare da bawa Innar hakurin barin ta yin shara,

"Innaa da kin kira ni ai n share"

"Kar ki damu, bari nai, Omo ne bera ya fasa ledar na dakko na adana na zubar kuma,...ina ciki ai ina maku dariya, ai Qaseem tun ya na yaro tsoron yanke farce ne da shi, baki ga yanda farcen shi ya yi duhu ba? Ai saboda tsabagen tsoro baya bari a yanke masa, sai da ya girma dinan ne ya ke yankewa a kasuwa, in masu yankan farcen sun gilma,ni ba na son yankan farcen kasuwa, baka san da wa da wa akai wa amfani da abun yankan ba,na ma yi mamaki da ya barki ki ka yanke masa, ko dake ba abun mamaki bane,"

Sunkuyar da kan ta qasa ta yi, ta ji kunyar kalaman Innaa na qarshe, Qaseem kuwa sai ya cafe maganar,

"Wato Innaa in ana yanken farce ji nake kamar yatsan za a cire,"

"Amma ai ka iya yankewa mutane ko?"

"Eh ai na san ba zan yanke su ba"

"To su ma ba za su yanke ka ba ai,"

"Kaiii inaa ba zan taba iya sake raina ba a gutsuren yatsa"

Dariya sosai suke ta yi, suka ji sallama, ya miqe ya na kade jikin shi,sai da ya kusan isa bakin qofar ya amsa, ya na zuwa soron mamaki ya kama shi, maqocin su ne, wani Alhaji Musa, ba zai fi shekaru 35 ba, ya na zaune da iyalin shi,a gidan shi wanda ya fi kowanne gida kyau a unguwar, suna mutunci sosai da Qaseem, in sun hadu a masjid, tunda suke ba su taba ziyarar juna ba, Qaseem ya kame kan shi ne saboda halin rayuwa kar a ce kwadayi ne ya sa ya maqale mishi,shi kuma Musa bai zuwa wajen Qaseem ne saboda bai da lokaci, ba mazauni bane, sai ya na gari za su hadu a masjid.

Gaisawa sukai suka hau hirar yaushe gamo, dan ya yi tafiya Germany, ya yi watanni biyu, sai jiya ya dawo, labari ya bashi akan ya samu aiki a can, zai koma da zama nan da sati uku, sannan ya ce,

"Al-qaseem, na zo na sanar da kai tafiyar mu ne sannan na yi maka wani tayi, amma sai kana so, in ba ka so, dan Allah kar ka ji kunya ko nauyi na, ka sanar da ni gaskiya"

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now