ALBASA BATAI HALIN...18

456 49 4
                                    

Yau Zeenat ta bawa kowa mamaki, ta yanda ta ke ta aiki tuquru, ba mita, ba tsaki, balle Yi wa yara masifa, sannan ba yaron da ta Kira ta Sanya shi aiki, burin ta kawai ta kammala abinda ke gaban ta, ta tafi gidan aunty, da ace za a Bata izini ma kwana za ta Yi, tunda mijin auntyn ya tafi Umara tun kwana uku da suka wuce,

'Na San me zan yi, yau dole na kwana gidan aunty Atika, ko da kuwa ba ta kammalan labarin ta dika ba, a qalla za mu fi rabi'

Murmushi ta Yi, da ta tuna me za ta yi, Dan ta samu damar kwana din, ta shirya tsaf Dan tafiya, Amma ta samu waje ta zauna, Kaka Fatu na kula da ita, ta na ganin yanda ta ke yatsina fuska, cikin nuna kulawa ta kalli Zeenat ta ce,

"Zeenat lafiya ki ke kuwa? Ko dai aikin ne ya Miki yawa, Dan na ga har abincin dare kin Yi, kin saka a kwarya Dan Kar yayi sanyi, in akwai abinda ke Miki ciwo, ki sanar da ni, Nurah ya Kai ki asibitin Sha ka tafi da ke Nan kusa"

Cikin Dan yatsina fuska ta ce,

"Kaka ciki na ne ya ke Dan juyawa, Ina Jin ya na ciwo kadan kadan,Amma na San zai bari, Ni zaman gidan nan da yaran Nan masu shegen ihu da cika kunne ke samin ciwon Kai,Bari na zo na tafi gidan Aunty Atika, yaran ta akwai tarbiyya, hayaniya wannan Bata Dame su ba, Amma Nan kamar Ana kunna su, sai su wani rashin Ji"

"Allah sarki Atika, ai ita dai yarinyar nan, akwai hankali, ba bu ruwan ta da hayaniya, dole yaran ta su Zama a nutse, tunda ba ta son harigido, Nurah ya so auren ta sosai a da,amma tsoro ya Hana shi fada Mata, sai da aka Mata aure, ya kwanta jinya, da kyar ya sanarwa mahaifin ku, sanda muka sani mun yi mishi fada, da kyakkyawan iri, irin Atika bai wuce mu ba, Dan na tabbata mahaifan ta za su ba shi, ba ruwan su, mutanen kirki ne"

Zeenat dariya kamar za ta suqe, wanne Baffah Nuran za a aurawa Auntyn ta Atika, tabb kwado, wayayyiya da ita, shi kuwa irin mazan qauyen Nan ne, dik da ya yi karatu zuwa matakin sakandire Amma kamar bai San bihim ba, Banda karatun hausa da rubuta hausa Bata Jin ya San ingilishi, to gwanda ma bangaren muhammadiyya, ta na Masa kallon Mai ilimin addini, kaiii dik da haka gaskiya ba mahada a kifi da kaska, gashi ta auri daidai ita, ta na kaiwa Nan a tunanin ta maza ta miqe, ta goya Fatee, sannan ta dau mayafin ta, da ledar da take zuba 'yan abubuwan da za ta buqata na yarinyar ta.

"Baki da dama Zeenat, me nee nee abun dariya a labari na?"

"Ba bu komai Kaka, kawai Ina hango Baffah ya auri Atika ne, kwata kwata hadin ne na ga bai mun ba"

"Saboda me?"

"Kaka Ni dai ba komai, kar ki daure ni igiya tai saura, a daure ki"

"Yo ni me na yi da za a daure ni?"

"Kaka kin Fara tambayoyin Nan naki na tsufa, na wuce, in Baffah ya shigo Dan Allah ki ce a siyo min maganin ciwon ciki"

"To zan sanar da shi,da kin sani ma zaman ki kikai, tunda ba ki da lafiya"

"Tabb ai na zauna sai yaran can sun raban Kai gida biyu, kin ji yanda Kai na ke sarawa yanzu ma, ka masu fada su yi shiru uwar su ta ce ka Dame su, Ni na tafi"

"Ki gaishe ta to da yaran"

"To Kaka"

Ta na fita ta yi murmushi, tabbas ta samu makamin kwana gidan Atika yau, sai ta ji kwal uwar daka.

Atika ta Yi mamakin ganin ta da wuri, bayan sun gaisa, ta zauna tare da kwantar da Fatee a gefen ta, ta na ta baccin ta cikin kwanciyar hanKali .

"Aunty Ina fatan ba wani aiki da ki ke Yi?na matsu na ji yanda za KU furta ma junan KU kuna son juna musamman ke"

Dariya Atika ta Yi sosai, saboda ta fahimci inda ta dosa, wato ta na ganin ba za ta iya furta kalmar so ba, saboda ta na shiru-shuru, Kuma Mai kunya.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now