Wani irin abu ta hadiya fuskar ta cike da fargabar me zai je ya zo, cikin son wayancewa ta miqa hannu dan kamo Nawwarah zuwa jikin ta, Nawwarah kuwa na ganin hannun Zeenat zai taba ta ta sa ihu ta qanqame Mahaifin su, wanda ya ke jin ihun ta kamar sukan wuqa a zuciyar shi, daukar ta ya yi kamar wata qaramar yarinya, ya hau rarrashin ta, sannan ya aje ta, bai ce ma kowa komi ba ya sanya kayan shi, a gaban yaran, sannan ya kama hannun su dika, ya yi hanyar fita, juyawa ya yi ya kalli Zeenat sannan ya ce,
"Ba a cin bashin Hasheem, ba a biya ba, za ki biya wannan abin da kika yi ma Nawwarah, ko ba yau ba,"
Su na barin dakin ta zube a bakin gado, ko da wannan kallon a ka barta ai ta ji jiki, wannan fuskar ta Hasheem na matuqar firgita ta, fuska ce da sai ka rantse cewar zai iya kashe mutum in ya sanya ta, to me zai mata? Da me zai rama? Ohhh Hasheem akwai son shiga sabgar yara, ta na kula da shi, tun da tazo gidan ya fi bawa yaran mahimmanci sama da kowa da komai, saboda yaran tun sanda ya kusance ta a hotel din nan har yau ba wani bayani, irin soyayyar dama da za su ci kenan? Dama akan irin wannan soyayyar ta biye mishi suka sabawa Allah a baya? Tsaki ta ja mai qarfi sannan ta miqe, ta fara cire kayan ta dan yin wanka, (ta tuna zunubin da ta aikata, madadin yin istigifari,sai ta yi tsaki)
Ta na wanka ta ji shigar mutum dakin, bata fito ba sai da ta gama sanye take da bathrobe, kalar pink, mai haske, ta daure kan ta da towel, sai pink takalmi na rigar, ko da ta shiga dakin ta yi mamakin ganin Nawwarah zaune a bakin gadon ta na shan Ice cream, abun ka da yaro, ta fi tuna kyautatawar da Zeenat ke mata akan tsawar da ta daka mata dazun, amma ba shi ya hana ta jin tsoron shirun da Zeenat ta yi ba, a zaton ta za ta sake yi mata tsawa, sai ta dan kwabe fuska, Zeenat na ganin haka ta dawo daga duniyar mamaki da tunanin da take ciki, ta isa gaban ta cikin fara'a, ta tsugunna, shafa gefen fuskar Nawwarah ta yi, sannan ta ce,
"My dear ki yafewa Momma kin ji? Dazu raina ne a bace shi ya sa na miki tsawa, kin yi min hakuri Nawwarah na?"
Daga kai ta yi, sannan ta yi fari da ido, irin na manyance nan,
"Mommaa dan Allah ki daina min magana kamar ki na magana da qaramar yarinya,i am 10 now, ba sai ki na min baby talk ba zan gane me kike nufi, kawai dan ban saba da tsawa bane ya sa dazu na tsorata, amma Hajiya ta mana fadan abinda mukai dazu, Waleedah ta yi fushi, saboda an mata fada, ta na can ta qi shan ice cream din ta da Daddy ya dakko mana a fridge"
"Da gaske? Kenan ta na fushi da ni?"
"Ba kadan ba,"
"Ki raka ni na bata hakuri, ba na son bacin ran ku, dazu ma raina ne a bace"
"Mommaa, wa ya bata miki rai ne?"
Shiru Zeenat ta yi, ta hau saka kayan ta, wanda ta ke jin haushin yanda Nawwarah ta kafe ta da ido sanda ta na sauya kayan, su ba su da tarbiyya sam in ana sauya kaya su dauke ido, (su zeenat masu tarbiyya😂).
"Never mind Nawwarah, na gama muje ki raka ni"
"To muje....Mommaa"
"Na'am Nawwarahn Mommaa?"
"Gaskiya ke mai kyau ce, jikin ki mai kyau, irin na 'yan film din qasar waje, su ne cikin su a dame, kuma..."
Zeenat ce ta sauya fuska kamar zata daki Nawwarah sai ta dake, ta hau yaqe, wadannan yaran su haka suke ne?ashe qare mata kallon da ta tsaya yi kenan, gaskiya da sake, ba burgewa a barin yara su na kallon tsiraici, ta haka ne suke tashi da son kallon tsiraicin, har a zarce da zinace-zinace Allah ya kiyaye.
Ko da suka je dakin Waleedah, ta na kwance ta na kallon film din America na yara, ta na ganin Zeenat fuskar ta ta dan sake, ba yabo ba fallasa, sannan ta tashi ta zauna, Zeenat cikin murmushi ta ce,
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...