Yana kasuwa hankalin shi na gida wajen Zeenat, kowa ya kalli fuskar shi sai ya San ya na cikin nishadi, da annashuwa, ga shi Kuma cikin taimakon Allah ranar ya samu ciniki sosai, Dan haka da yamma bayan an tashi daga kasuwa, wajen masu sai da gasasshiyar kaza ya tsaya, tana tururi haka aka yanka Masa biyu aka mishi qunshi guda biyu da su, Yana godiya ya nufi gida, Inna na alwalar magrib, ya Yi sallama ya shiga, cike da Jin nauyin ta ya durqusa ya gaishe ta, kallon shi ta yi fuska ba walwala kamar kullum, gaban shi ya ji ya fadi,hankalin shi ya tashi,
"Inna lafiya? Ko ba ki da lafiya ne? Me ke damun ki?"
"Lafiya ta qalaou, amma marasa lafiyan ai haka ka tafi ka barsu, ba ka sanar da Ni ba, yanzu fisabillahi Al-Qaseem a binda ka aikata ka kyauta? Ka tafi ka bar yarinyar mutane, ba taimako, sannan Ni ba ka sanar da ni ba, sai kukan ta da ya yi yawa na jiyo na leqa, na tadda ta kwance zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, sannan ga shi ta kasa fitowa sallar azahar qafafun ta na mata ciwo, ba a haka, da zaka fita da ka sanar da Ni da na taimaka mata,"
"Inna Dan Allah ki Yi hakuri, bana son ran ki ya ɓaci akai na, sai na ji hankali na ya tashi, ki yafe min, na rasa ta yanda zan mi ki bayani ne shi ya sa, amma ki yafe min"
"Dama akwai abinda za ka iya boye min?kar ka manta a tsakanin mu ba boyon sirri, ballantana ban ce ka tallata me ka yi ba, ka sanar da Ni kawai bata jin dadi ya wadatar, ai ni ba sokuwa ba ce zan gane, sai ka tashi ka shiga ciki, tun tea da na haɗa mata ta qi Sha ko cin komai, sai kuka, dan haka zazzabin ya qi sauka,"
"Innata ki yi hakuri, ga wannan na kawo, bari na je na bata, sai ta samu ta ci, in ya so Inna dawo daga isha'i sai na kawo mata magani"
"Allah ya muku albarka, maza kai mata, ka dawo na deba maka wannan ku qara, ya min yawa, ka san ba abinci na ke ci mai yawa ba, ku kuwa yanzu kuna da yawa"
"Ba komai inna, in kin rage ki aje kawai"
Godiya ta mishi, ya shige ciki, ita kuma ta shiga dakin ta, yana shiga ya ganta kwance ta rufu, yanda ya zata zai ji jikin ta, abun ya fi haka, jikin ta zafin gaske, musamman kan ta, tsabar zazzabin ko doke hannun shi ba tai ba, dan ya san a karon banza bai isa taba ta ba ya ji shiru.
Janyo ta yayi jikin shi ya jinginar da ita, nan ma bata kwace ba, sai ya ɗora kan ta a pillow, ya dauki dan qaramin towel ya debo ruwa, ya dinga shafa mata, a jiki, musamman kan ta, da alama ba qaramin ciwo ya ke mata ba,
"Dan Allah ki daina kukan nan, in ki na kuka, jikin ki ba zai sauqi da wuri ba, tashi ki ci nama na kawo Miki"
Ba kunya ba tsoron Allah, Zeenat in an yago kaza sai ta Yi ram da tsokar kaza a Baki, ba dan tausayin ta da ke damun Qaseem ba da ya yi dariya, haka ta yi ta ci, sai da ta qoshi, Dan dama lamarin har da yunwa, Kuma ga taurin Kai, ta qi daina kuka.
Kwana uku Qaseem ya dauka ya na jinyar Zeenat, ta maida shi Kamar wani banki, kullum sai ta ci nama, in ba ta ci nama ba ta dinga Masa ruwan rashin mutunci, sannan tun ranar ba ta sake Bari ya kusance ta ba.
************************
Watanni biyu kenan da auren Zeenat da Qaseem, qiyayya sai abinda ya Yi gaba, yau tun safe ko na ce tun asuba ta ke Masa wulaqanci akan ya ce ta hakura da zuwa gidan su, sai ya dan samu kudi, yanda za ta masu tsaraba, shi ne ta ja ta kame a bakin qofa ta na ta gurza Masa rashin mutunci.
"Dik da ban fito gidan hamshaqan masu kudi ba amma dai ka San Iyaye na sun fi qarfin ka musu tsaraba ko? Me za ka bayar, omo ko sabulu? Ni na ma tsaya Bata yawun Baki na Ina neman izinin ka, an jima za ni, ka Hana ni in ka Isa"
"Zeenat na fada maki Kar ki je, muddin ki ka fita ba izini na, zan ma Baba waya na sanar da shi, kin San sauran"
Dariya ya kwashe da shi da ya ga ta yi zaman 'yan bori a qofar dakin, tana gunjin kuka, tare da watso Masa baqaqen maganganu, tabbas baya jin dadin zagin da ta ke mishi , amma son da ya ke Mata ya rufe Masa ido, ba ya damuwa.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...