ALBASA BATAI HALIN...17

442 38 1
                                    


Kamar yanda ki ka ji labari mun Yi zaman Kano, kafin rasuwar mahaifan mu, a lokacin an Sanya bikin Umman ki da Baban ku, yayun mu maza Kuma su na zaune da matan su a nan gidan iyayen mu da ke nan garin, Ana Gama shagalin biki muka yo qaura muka dawo garin Kano da Zama, unguwar Jan bulo, lokacin na gama secondary school a Nan garin panda, sai iyayen mu su ka yanke shawarar sanya ni a makarantar FCE da ke Kano, cikin sa'a kuwa na samu gurbin karatu, a inda na ke karantar Eng/Geo, a gaskiya ni ban kasance mace Mai yawan surutu ba, Kuma Banda hayaniya, sannan bana son hayaniya, na fi son a Koda yaushe na zauna ni kadai, ko Ina karatu, ko Ina sauraran redio a waya ta, ko Kuma na yi karatu.

Muna da kyakkyawar alaqa da ni da iyaye na, musamman mahaifin mu, ya bamu dikkan gata, sannan ya bamu ilimi na addini, da na Boko.

Ban taba manta ranar da aka Kai ni makaranta, bayan kammala komai da ya dace, Dan kasancewa ta daliba a makarantar, Ina zaune a aji, lecturer din mu, ya shigo, na tattare dikkan hanKali na, domin sauraran abinda zai fada, gefe na, wata yarinya ce Mai suna Bilkisu, a yanda na kula ita ma halin mu kusan Daya ne, ba ta da hayaniya, Kuma ta na da son karatu, bayan fitar lecturer din ne, ta karbo time table guda daya, a wajen wasu matasa a ajin, ta miqo min sannan ta ce mu kwafa a tare, na amsa na Mata godiya, sannan na miqa Mata hannu, muka gaisa, tare da gabatar da kan mu ga junan mu, a Nan ne na San sunan ta Bilkisu, Kuma unguwa Daya muke da ita, sai dai layi mu na da nisa da na junan mu.

Tun daga ranar ni da Bilkisu muka Zama abokan juna, mu ke mutunci sosai, dik Wanda ya sanni, to ya San ta, haka dik Wanda ya San ta ya sanni, mutanen makarantar da dama, su na Kiran mu, da masu girman Kai, saboda ba mu kula kowa, musamman samari.

Ranar da muka Fara haduwa da shi, Rana ce da ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwa ta, wata ranar litinin, na shigo makaranta Ina qoqarin Isa class , shi Kuma ya na zaune cikin abokan shi, ya na daddana wayar shi, sai abokan shi suka fara tattaunawa a tsakanin su, akan cewa ga ni nan na wuce, sarkin shariya, dik maganar da suke, ya na sauraran su, sai dai har a lokacin bai daga Kai ba, har na wuce, a ranar har suka bar wajen magana ta su ke yi"

"Aunty Atika Kar ki ce na katse ki, ta ya akai ki ka San me suke tattaunawa ba yan kin bar wajen, Kuma ke ba Mai shisshigi ba ce balle na ce kin kutsa Kai Dan Jin me ke faruwa?"

Dariya Atika ta yi sosai, saboda wautar Zeenat na Bata dariya,

"Zeenat Kar ki Manta labarin masoyi na zan Baki, Dan haka na San komai ne a wajen shi, dik labarin da za ki ji, ki qaddara ni da shi muke ba ki wannan labarin, kin gane?"

"Eh na gane, aunty ci gaba, dama ban katse ki ba,"

Murmushi Atika ta yi, sannan ta ci gaba da labarin ,

"An tashi daga makaranta, Ina ta sauri dan tafiya gida, Bilkisu na jira na a gate, sai suka ganni, zan wuce, a Nan take, Daya daga abokan shi, suka saka kudi, ga dik Wanda ya min magana na kula shi, ba Bata lokaci kuwa ya yi saurin amsawa, tare da cewa shi zai je, saboda dik Wanda ya kwana ya tashi a makarantar Nan ya San wane ne, Adam, wajen magana, da iya tsara zance, ya na da kyau, irin kyaun nan mai kwantar da hankali, ba fari bane, Amma kalar shi, na wahala ki same ta a wajen kowa, ya ajiye gemun shi madaidaici, Wanda ya qayata kyawun fuskar shi, ga shi da iya daukan wanka,...Kar na cika ki da surutun kyawun siffar shi, saboda dik yanda zan maki kwatancen Adam ba za ki gane ba sai kin gan shi"

"Kaiii amma aunty da ga ji, kina son Adam dinnan sosai"

Murmushi Mai ciwo ne ya bayyana a fuskar Atika, sannan ta gyara zaman ta, ta ci gaba da labarin ta,

"Qamshin turaren shi ne ya Fara dukan hanci na, sannan sallamar shi da daddadar muryar shi, shiru na Yi ban amsa mishi ba, sai da ya maimaita har sau biyu,ban amsa ba, ganin haka, sai gaban shi ya Dan Fadi, Dan Kar na bashi kunya wajen abokan shi, sai ya gyara tsayuwar shi sannan ya ce

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now