ALBASA BATAI HALIN..38

391 47 9
                                    

Umma da Mama na tsakar gida su na aikace-aikace na yau da kullum su na ta hira, abinda tun da aka auri Mama ba su taba yi ba, yanzu sai su bata awanni su na hira, sai in Umma ce ta kula da lokaci ya tafi ba ta more shi ta hanyar yin ibada kamar yanda ta saba ba, sai ta taqaita hirar, yanzu Mama ma ta koyi yawan karanta al'qur'ani, da sauraron shi, yawan yin tasbihi da yin sallah akan lokaci, duk dan kusancin da ta samu da Umma ne, (haka abota take, ba ka sani ba ma sai ka fara halayyar wanda ka ke tarayya da shi, in mai kyau in mara kyau, wasu lokutan sai abun ya yi nisa baka farga ba, kafin ka dawo daidai ana daukan lokaci, Allah ka hada mu da abokai na gari a ko ina muke a rayuwae mu).

Umma ce ta jinginar da tsintsiyar ta ta ce,

"Ni kam Sa'adatu Zeenat na kiran ki kuwa?"

"Ah ah gaskiya,"

"Ok"

Sharar ta ta ci gaba da yi, zuciyar ta na ci gaba da mata saqe-saqe akan qin neman su da Zeenat din bata yi,

"Ni fa ina ganin kawai Zeenat ta samu kwanciyar hankali ne, lafiya ke boyo yaya, kar ki damu"

"Ai gani na yi Zulfa'u da Suhailah na kira gida akai akai, a gaisa, su ji ya muke,mu ji ya suke, amma ita ta jima ba ta kira na shiru, shekaran jiya da Suhailah ta kira ni sai da ta tambayen ita,Zulfa'u dazu da safe da ta kira ni sai da ta tambayen Zeenat din,ta ce sun jima sosai ba su gaisa ba,to kin ga kenan ba su zumunci, kuma a yanda ta ke tsananin son Fateema, yau kusan wata uku, ai ya kamata a ce ta neme ta ko? Gashi har Kaka Fatu ta wuce da ita Panda ba a sanar da ita ba, duk da ba wai mu na neman izinin ta bane kafin gabatar da hakan, amma da ya kamata ta sani,gaskiya shirun ta ya fara bani tsoro, dama irin dukiyar da take nema kenan ta manta da angin ta?"

Shiru sukai vaki dayan su, dan Mama ma bata da abin cewa, indai irin dukiyar da Zeenat ke nema kenan akwai matsala, ta zama mai halaye kala kala kenan, daga wannan ta yi wannan,

"Ki kwantar da hankalin ki, inshaa Allahu lafiya take, ba wata matsala bane, tsabar jin dad'in gidan miji ne kawai, in bata zo ba ai mu za mu iya zuwa, sannan mu ma da laifin mu ai, da muka ji ta shiru haka da mun leqa ta ko sau daya ne, ko mu kira ta, ai ba d'a ne kawai ke da alhakin kira ya ji ya iyayen shi suke ba,iyaye ma na da haqqin kira su ji ya yaron su yake, shi sada zumunci ba na mutum daya bane ai"

"Haka ne kuma, to yanzu yaushe ki ke ganin zamu je? Sannan ke za ki tambayar mana, ni dai ina jin kunya na tambayi zuwa gidan Zeenat"

Dariya sosai Mama ta yi, sannan ta ce,

"Ohhh kunyar har yanzu ta na nan kenan, ai na zaci kin jima da aje ta gefe"

"Jinin fulani ce fa ni, ai ko kin san kunya ba a taba rabuwa da ita"

Hira sukai ta yi gwanin sha'awa, girki a tare suka yi shi, su na dariyar za su rudar da Baban Zeenat ya rasa wa ce ta yi girkin, bayan sun kammala sukai wanka, suka shirya tsaf, kowa da kalar ta ta kwalliyar, Umma ba ta fita ba, dan ba ita ke da girki ba, littafin addu'o'i ta dauka ta na yi, Mama na d'akin Baba ta na gyarawa, ya kusn dawowa, bayan ta kammala ta samu waje ta zauna, ta na kallo.

Sallamar shi ce ta dawo da ita daga duniyar kallon da ta fada, kallon gidan kawai ya ke ya na qarawa cike da farin ciki,abinda bai samu ba tun da quruciyar su sai yanzu da girma ya kama su, lallai da alama zai yi tsufa mai kyau, murmushin shi ne ya qaru, d'akin Sailuba ya nufa, Mama na fita ta ga ya yi hanyar dakin Umma kawai sai ta nufi kitchen ita kuma, dan hada masa kayan abinci, da sallama ya shiga, suka gaisa, ya sanya mata albarkar hakurin da tai da Mama, gashi yanzu gidan su na zaune lafiya, kowa hankalin shi kwance, har wata murmurewa sukai baki dayan su, godiya ta mishi, sannan ya dau jakar shi ya yi dakin shi.

Mama ma ta sha yabo, saboda sauyawar ta ba qaramin ci gaba ta kawo masu ba a gidan, ko ina tsaftsaf ga qamshi na tashi, ga kwalliya ya na gani kala kala, da kuwa Ummaa ce kawai ta damu da yi masa gayu, duk da cewar Maman ta fita yarinta.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now