ALBASA BATAI HALIN...30

501 46 18
                                    


Makullin mota ya dauka, bayan ya shiga bayi ya wanke baki, ya jefa sweet mai qamshin Banana, sannan ya fesa turarukan shi masu tsada, da dadin qamshi, gyara zaman hular shi ya yi da kyau, sannan ya debi kudi masu dan yawa, wani wajen gashin kaji ya je su na saida drinks kala kala, da gasasshiyar hanta, siya ya yi da dan yawa, sannan ya nufi supar market ya sai dangin chocolates d biscuits, ya debi manya na kwali masu tsada, sai gidan su Zeenat, ta shirya tsaf ta na jiran zuwan shi, bayan ta nemi izinin fita wajen iyayen ta,sun amince mata, Umma na daki Zeenat ta gama shirin ta, jin qamshin turare har dakin ta ne ya sa ta fita dan gane ma idon ta abinda Zeenat din ke yi, ko da ta shiga sai ta gan ta sanye da damammen skirt, da T'shirt da ta dame ta, an yi rubutu a jikin ta da manyan baqi, YOU ARE MINE, mamaki da kuma tsoro ne ya shiga Umma, ba ta san sanda ta zauna a katifa ba kusa da Zeenat din sannan ta kama hannun ta cikin kulawa, da tattausan lafazi ta ke magana,saboda sanin halin Zeenat da tai, ta na iya mata nasiha ta fassara ta ta ce an ce mata 'yar iska.

"Zeenat wannan shigar fa? Kin ko ji yanda ki ke qamshi har daki na fa, haba Zeenatun mu, ke ce sanyin idaniyar mu, kar ki manta fa ke uwa ce, ki na da yarinyar da za ki kare mutuncin ki domin ta, ki kalli fa shigar ki, shin an sanar da ke cewar shaidan ba ya tare da duk wani d'an Adam ne? Akwai fa shaidan in ke ki na taqama da imani, manyan sahabbai da Annabawa shaidan ya samu galaba akan su, musulunci bai yarda mace ta yi irin wannan shigar da ki kai ba, kuma bai yarda mace ta fita ta na qamshi haka ba, ina ki ka bar roll on? Ki shafa yanda ba zaki wari ba ki je inda za ki ki dawo, hankalin ki kwance,ba zunubi ba kuma tadawa kan ki da wasu hankali, na sani Zeenat ki na da hankalin ki, da sanin ya kamata, ba za ki bar kowanne namiji ya keta mutuncin ki ba, duk rashin jin ki na miki shaidar kamun kai, ina mai maki nasiha da ki ji tsoron Allah, ki sauya yanayin shigar ki, Hasheem mutumin kirki ne, kar ki ja maku fushin Allah, duk kirkin shi shi ba ma'asumi bane,wannan shiga a aje ta sai bayan an yi aure, sai a sha gayu, ko Zeenat din Umma? A ji tsoron Allah,idan umma da Baba ba sa waje, to Allahn da ya halicci wajen ya halicce ki yana wajen, domin da ke da wajen da abinda za ki aikata duk na shi ne, iyaka ya baki lada a kyakkyawa, sannan ya baki zunubi a mummuna, zabin na hannun ki"

(Iyaye a dinga kulawa da shigar yara, last week na shiga kasuwa, wata yarinya an mata dinki irin damamammen nan, ga ta qarana a fuska, ba zata wuce sha uku sha hudu ba, amma ta na da jiki mai kyau,duk inda ta bi maza a kasuwar nan sunna kallon ta, mayafin ta a wuya, ya ilahi ta ya za ku dinga barin yaran ku na fita a gaban idon ku tsirara? In an masu nasiha ma su na iya ce maka a gaban uwa ta da ubana na fita ba su hana ni ba ba ku isa hana ni ba, to ko kun manta yanzu samarinin sun kyasa har gida suke bi su fyade maka yarinya su tafi? A bar ki da shiga uku da tashin hankali? In ba ku kiyaye ba ba mai kiyaye maku a wannan zamani na son zuciya da son kai da muk ciki)

Zeenat tunda take tsiyar ta ba ta taba jin maganganu masu ratsa zuciya irin wadannan ba, da sauri ta miqe bayan Umma ta fita, ta sauya kaya da wata doguwar riga qirar Dubai, kalar blue, da milk din aiki a wuya da hannu, sai stones masu kyalli da shegi, bata sake saka turare ba, dan a hakan ma akwai qamshin na dazu kadan a jikin ta, sai ta ji da da lokaci ma wanka za ta sake, mayafin kayan ta nade kan ta da shi, ba qaramin kyau Zeenat ta yi ba, ba a cewa komai sai masha Allah, ba ta jima da zama ba Hasheem ya mata waya gashi nan, takalmin ta mai dan tudu kadan ta saka, mai stones farare, sannan ta dauki wayar ta, ta dauki Fatee ta fita, Umma na zaune ta na jiran ta ga gilmawar Zeenat dan ta ga ko ta dau nasihar ta? Sai ta ji sallamar ta, dauke da fatee da tai bacci.

"Umma ga ta ya zo, ba ri na je,"

"Ok to, sai kin dawo, masha Allah, ba dan kar nai son kai ba, sai na ce Zeenat di na ta fi kowa kyau"

Ta ji dadin yabon da Umman ta ta mata sosai, sai ta ke jin ashe da ta kwantar da hankalin ta a da, Umman ta mai son ta ce, ba tsanar ta ake ba ko a da, ta na wannan zancen zucin ta miqa Fatee ta fita, ya na zaune duk ya matsu ta zo ko dan tattaba ta ne ya yi,ko kuma su bar unguwar ma ya kaita wani hotel din su dan shana, a matse yake, da ya sani bai saki ummee da wuri ba,ko ba komai za ta debe masa kewa, shi kuma ya na da kyankyamin matan waje, sai dai in ya samu mace maitsafta kyakkyawa ya kan bi, amma ba koda yaushe ba, ya fi ga ya auri mace akan ya neme ta a waje.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now