Suhailah na zaune su na hira da Kaka Fatu da Maman ta, gaban ta farfesu ne da ya sha kayan qamshi, sai zuba santi take, su na mata dariya, ta sha wankan ta tayi kyau, Kaka Fatu wankan jego ta mata, a cewar ta b'arin ma ai duk d'a ne ya fita da ga jikin ta.
Bangare guda kuwa Zeenat ce ke qoqarin fitowa daga daki, cikin ado mai qayatar da wanda ya kalle ta, daga ita har baby Fatee, gashin kan ta ta gyara shi ya zauna a dokin wuyan ta, ga qamshi su na zubawa, dakin Umman ta ta shiga, ta tadda ta ta na karatun qur'ani, saboda rashin zaman lafiya da suke da Mama ko da yaushe cikin karanta qur'ani take, shi ne abokin hirar ta, sallamar ta kawai Umma ta amsa, ba ta sake magana ba, sai karatun ta, Zeenat ta qaraci tsugunnon ta,da gaisuwar ta ba ta amsa ta ba, miqewa ta yi, ta fice ranta a bace, a tunanin ta Umma bata damu da farin cikin ta ba, me ye laifin ta dan ta na fada akan haqqin ta? Qaseem na ta ne, ba na wata ba, ko zai aure ai bai kamata ya auri qanwae ta ba, in ba so ake a ci mata mutunci ba ina Suhailah ina Qaseem?
Mayafin ta ta yafa a kafadar ta, sannan ta shuri takalmi ta sanya a qafarta, qoqarin rataya jakar ta take ta ji Sallama, gane masu dauke da muroyoyin da tai ne ya sa ta saurin juyawa, tare da sauke jakar qasa ta fadi,cikin zumudi da kewar da bata tabbatar ta gaske ba ce ko ta son zuciya ba ce ta tafi da sauri ta rungume dattijuwar, tare da fadin.
"Innarmu ina kwana?"
Innar Qaseem cikin mamaki, da sake duba mai maganar da kyau, ta amsa da,
"Lafiya qlou, Zeenat?"
Daga kai Zeenat ta yi cikin murmushin jin kunya,sannan ta amshi ledar da ke hannun Inna ta kai ta dakin Ummaan ta, itama Innar can ta nufa, ai duk daya ne.
Bayan ta zauna Zeenat ta zube a qasan qafar ta, ta sake gaishe ta, amsawa ta yi, cikin sakin fuska, dan da alama, zeenat ta nutsu, amsar Baby Fatee ta yi, ta fara mata wasa,Fatee tayi shiru ta na bin Inna da kallo kawai, budar bakin Zeenat sai cewa tayi,
"Ai dake na yaye ta jiya, shi ya sa ki ka ga bata walwala, amma akwai fara'a kamar ki Innarmu"
Abun duk wani banbarakwai Inna ke jin shi amma sai ta dai yi shiru, Qaseem da ke tsaye a tsakar gida Zeenat ta fita da sauri ta daukarwa tabarma za ta kai mishi, har ta kusan isa wajen shi, Suhailah ta fito, dauke da carpet, da pillow, da sauri ya amsa, ya fara shimfidawa, sannan ya amshi pillow ya saka mata, sai da ya miqa mata hannu ta kama, ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna, daf da ita, kamar zai shige cikin ta, magana ya fara qasa qasa, duk maitar Zeenat na son jin me ya ke fada ta kasa jin komai, murmushin jin kunya da kuma rufe fuska ta ga Suhailah nayi, tsayuwar ce ta kusan gagarar ta, ta dogara tabarmar ta tsaya cikin bacin rai, Suhailah kuwa wuyan rigar shi ta miqa hannu ta balle mishi maballin rigar shi, ta dan yi mishi hararar wasa, sannan ta ce,
"Kwana daya kawai na yi fa amma har ka fara saka riga ba daidai ba"
"Kwana dayan da ki ka yi sai na ji su kamar shekaru"
"Gaskiya Yah Qaseem ba zan boye maka ba, ni ma jiya na yi kewar ka sosai"
Rufe fuska ta yi da hannayen ta masu kyau, kallon hannun ya yi, tare da qoqarin tabawa dan dauke su a fuskar ta ta, da qarfi Zeenat ta yarda tabarmar can gefe, sannan ta ce,
"Me ye haka za ku dinga yi wa mutane iskanci a gida? Ba za ku bari ku koma akurkin gidan ku ba? Suhailah ki na ban mamaki, wai har kin san ki min kwacen miji?...
"Point of correction, mijin ki a da, ashe ma kin yarda yanzu miji na ne? Kuma muna da akurkin gidan za mu koma shi nan ba da jimawa ba, ki sha kurumin ki, na fada maki ki fita hanya ta kin qi ko? Ba fa ke daya kk iya rashin mutunci ba, kyale ki kawai ake, in kk ga nawani sai kin tabbatar da ke ba ki iya komai ba, amma ki ci gaba, watarana zan gyara maki zaman da kowa ya kasa"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...