ALBASA BATAI HALIN...53

359 45 9
                                    

Aqilu jin shi yake kamar shi ne namiji mafi sa'a a rayuwar shi, duba da yanda Allah ya mallaka mishi mace daya tamkar da ba iyaka,duk wani maraicin da ya yi shekara da shekaru ji yake babu, Nawwarah ta dauke duk wani darasi da ta samu wajen Zeenat,har da qarin nata wanda naturally kowacce macce ta na da halittar kula da abokin rayuwar ta.

Wata ranar lahadi su na kwance, Nawwarah ta dora kan shi a cinyar ta ta na shafa kan shi, ta na bin layi layin da ke kwance a kan shi wanda gashin shi ya zana, dayan hannun ta ta rungume shi tsam, kamar wanda za a kwace mata shi, yanayin yanda fatar jikin su ke gogar ta juna na qara masu wani irin kusanci, wanda suke jin kamar ba za su iya rayuwa ba dayan su ba, Aqilu duk ya sauya, a yanda da ta dauke shi mai tsaurin ra'ayi, da rashin yawan fara'a, yanzu abun ya sauya salo, ya koma mata kamar wani jinjiri, sai yanda ta juya shi, dariya kuwa kamar ka kalli qaramin yaro ne da ke koyon zama, nan da nan zai washe maka baki ya na fara'a, haka Aqilun ta ya zama, yanzu ma shagwaba ya ke zuba mata, akan shi dai gaskiya ta d'aga tafiya zuwa kano sai nan da kwana biyu, duk ya manne mata a jiki, fuskar shi na fuskantar cikin ta, sai wani lumshe ido yake, cikin sigar lallashin qaramin yaro take magana,

"Haba yah Aqilu, ka yi hakuri kaji? Da na je aka gama interview zan dawo, sai na dawo mu yi shirye shiryen tafiya gaba daya, kwana biyu fa kawai zan yi"

Zagaye hannayen shi ya yi a cikin ta gaba daya, ya yi rufda ciki, ya manna fuskar shi a cikin ta dake a shafe, hannun ta na saman kan shi da bayan shi, cikin muryar shagwaba ya ce,

"Ni dai gaskiya mu tafi tare to, tunda ba dad'ewa zaki ba"

"Kaiiii so ka ke su Umma su tsokane mu ko? Kar ma Aunty Suhailah ta ji labarin mun je tare ai mun shiga uku da tsokana a wajen ta, kamar ita ma ba haka suke da Daddy Qaseem ba, ko ina suna tare"

"Ni dai kar ki sauya magana da ta su Aunty Suhailah,ki tafi dani manaa"

Dariya sosai ya bata yanda ya ke magana,

"To zan tafi da kai kaji babyna? Daina shagwabar haka,"

Da sauri ya daga kai, cikin dakewa, ya na wani basarwa,

"Wa ke shagwaba? Ni? Habaa, sai kace ke, ni dai kawai ina son na biki ne, in ya so ko a ranar sai na dawo,"

"Okk na ji ba shagwaba ka ke ba, kwanta kai bacci,"

Komawa ya yi ya kwanta, suka ci gaba da hira akan irin soyayyar da Suhailah da Qaseem suke zubawa, su suke kalla a matsayin madubin su, a haka ta na shafa kan shi bacci ya dauke shi, ta sunkuya ta sumbaci kuncin shi, da ya dan yi bulbul, ta ajiye kan shi a hankali a pillow, sannan ta ja masa abun rufa, kwantawa ta yi itama ta manna jikin ta a nashi, tare da yin addu'ar bacci, ta shafa musu.

Da safe tare sukai wanka,kamar jariri haka take kula da Aqilu, bayan ta gama shirya shi, ta fara nata shirin, kitchen ya shiga ya dora musu ruwan tea da ya sha citta, kaninfari, na'ana'a, girfa da madarar shanu, jira yake ya tafasa ya tace musu su saka zuma, a gefe guda kuma ya fasa kwai ya yanka albasa mai yawa, ya bare garlic ya daka da dan attaruhu guda daya, ya zuba, ya saka maggi kadan, ya soya musu, suyan ta yi kyau sosai, Nawwarah na jiyo qamshin abincin ta lumshe ido, Aqilu akwai son kyautatawa, shi ya sa itama ta dage wajen kyautata masa.

(Ko murdadden miji gare ki, hada shi da addu'a,ba dare ba rana, akan Allah y miqar maki da shi, kyautata masa ko yana gwale ki, watarana zai daidaita akan hanyar da kk so da izinin Allah, da addu'a komai na daidaita, hakuri shi ne jigon samuwar farin ciki watarana,kalamai masu taushi da dukan zuciya suna taimakawa wajen tausasa namiji, ki nuna masa wane in ban tarairaye ka na gatanta ka ba akwai wadda za ta maka ne? Ko kuwa so ka ke sai ka hango ana ma wani irin abinda na ke son in maka a gida ka qi, ka ga kamar kai matar ka bata iya komai ba, bayan kai ne ka ke hana ni damar kyautata maka?ka bani dama ka ga yanda zan jiyar da kai dad'in zamantakewar aure ta kowanne angle a rayuwar mu, amma yawan nesanta ni da kan ka da ka ke ba ka tsoron watarana ka nesanta kan ka da zuciya ta? Akwai ranar da zan gaji da bin ka dan kyautata maka, ka na tunanin za ka iya jurewa? Duk yanda na ke so na kyautata maka in baka ban dama ba ka na gudu na, ba zai samu ba, da irin wannan kalaman za ki daki zuciyar miji murdadde, na san wata ma ta fini iya tsara zance amma ba zata yi ba, sai ai ta cewa miji na kyara ya na korar mace, bayan ba ta tsaya da yi mishi addu'a ba, sannan bata dage da ci gaba da kyautata masa ba, mata a waye a riqe Allah)

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now