ALBASA BATAI HALIN..23

368 43 6
                                    


"A zato na in ya shigo zai kalli inda na ke, Dan haka na tattare dikkan tunani na, da nutsuwa ta, na Kai bakin qofa, amma abin mamaki da Adam ya shigo ko kallon inda na ke bai ba, ya samu waje ya zauna, har muka Fara test Adam bai kallen ba, mun kusan gamawa kenan, na juya Dan sake kallon shi, cikin sa'a kuwa Muka hada ido da shi, da sauri ya sauke idanun shi ya daina kallo na, ko da aka fita daga test Adam da abokin shi saurayin Bilkisu, su na ta Hira akan test din da akai Mana, ni da Bilkisu mu ka' Isa wajen, Adam na gani na ya dauke Kai, muka gaisa ya bar wajen,ji na Yi zuciya ta ta fashe, ta yanda bana Jin akwai abinda zai iya tattaro min ita ta dawo daidai.

A kwana a tashi har muka Fara sabawa da yanayin daina kula junan mu, Amma fa can qasan zuqatan mu cike ya ke da tsantsar so da kewar juna, Adam sai ya fara kula course mates din mu su na gaisawa, abinda da ba ya yi, ya na hakan ne ashe Dan samun sauqin zuciyar shi akan yawan tunani in ya zauna shi kadai, a bangare na kuwa wani irin kishi ne ke addabar zuciya ta, ta yanda na kasa jurewa, ba zan iya ganin Adam na kula wata ba, saboda ba Wanda na ke so sama da shi.

Watarana na yanke hukuncin Yi mishi magana akan hakan, cikin sa'a kuwa na hango shi, Dan Haka na bi shi ina Kiran shi, ya tsaya kuwa cak, cikin rashin gwarin guiwa akan abinda na ke son aikatawa na budi Baki na Fara mai magana.

'Adam ina son magana da Kai, in ba damuwa'

'Ok ba damuwa, mu je can ajin mu zauna'

"Nan muka samu wani aji muka shiga muka zauna nesa da juna, ko da na budi Baki na zan magana, kawai sai hawaye suka Fara zubo min, Ina kallon yanda fuskar Adam ta shiga cikin tsananin damuwa, Dan ganin hawaye na"

'Adam ina son maka tambaya ne'

'Ok ina sauraron ki'

'Adam ba ka tausayi na ne? Adam ba ka tunanin halin da zan shiga sakamakon rabuwa da ni daka yi, ka na tunanin zan iya jure rashin ka a cikin wanna qanqanin lokacin?'

'Na ji tambayoyin ki, Amma ni ma ba ki tunanin halin da na ke ciki,'

'Wanne hali ka' ke ciki bayan ka na nan kana walwalar ka' a cikin mutane'

'Ba Wai ina walwala bane Dan Banda damuwa a cikin Rai na, Ina qoqarin bin duk wata hanya ne da za ta kawon nutsuwa a cikin raina ba tare da na shiga wani halin ba,kin sani ba wata wadda na Saba da ita bayan ke, wannan dalilin ne ya sa na ke qoqarin sabawa da rashin ki, qaddarar mu ce ta zo Mana a Haka Atika, dole ne mu yi hakuri, mu bi zabin Allah da hukuncin shi akan mu'

'Yanzu dai ka na tabbatar min da cewa rabuwa za Kai da ni gaba Daya, kowanne hali zan shiga na shiga ko?'

'Ba haka bane, kin fi kowa sanin ina qaunar ki, Ina son ki, Amma ba yanda na iya, tunda a yanzu ki na da Wanda za ki aura, kin ga ba zan ci gaba da soyayya da ke ba, Ina sawa Rai na abinda na San ba samu zan ba'

"Cikin kukan da na Jima dama ina Yi na ce"

'Kaico na da wannan mummunar qaddara da ta rabani da Kai bayan na Saba da son ka'

"A lokacin shi ma Adam ya Fara hawaye, Amma cikin dauriya ya ce,"

'Atika mutane na ganin ki, ki na kuka fa'

'To su ganni din mana'

"A sannan ne Adam ya yi murmushi, sannan ya Fara lallashi na har sai da na daina kuka sannan mu ka' fita muka tafi zuwa gida, abun hawadaya muka shiga, tun daga sannan a makaranta in mun hadu za mu gaisa, Amma fa ba ma Hira Kamar da.

"Watarana an tashi daga school sai wata course mate din mu ta zo da sauri, ta ce ma Adam.

'Adam yau Kai zan bi, unguwar KU za ni'

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now