ALBASA BATAI HALIN...39

376 47 10
                                    

Cikin sauri da kuma daga murya ya furta,

"NOOOOO, ban yarda ba, ummm....a ...a bar ta kawai anan..zan kula da ita, ba na son ta yi nisa da ni, na gama shirye-shiryen tafiya asibiti da ita dama a yau dinnan,ba sai kun tafi da ita ba, ba zan iya rayuwa ba ita ba"

Wani kuka mai ban tausayi ya sake, ba wanda bai tauya mishi ba a wajen,har umma da ke jin haushin shi, Nawwarah ce ta isa gaban shi, ta dora kan ta a qafar shi, sannan ta ce,

"Daddy ka daina kuka, Momma na za ta samu lafiya in Allah ya yarda, ni ma ba na son a dauke min Momma na"

"You see, yaran nan sun shaqu da ita, dan Allah kar ku dauke ta, yau zan kai ta asibiti, dama akwai likitan da ke zuwa duba ta kullum, ba mu samu asibiti mai kyau bane sai yau din,bari ma na kira likitan na ji ya maganar dakin da na ce a sama mata mai kyau,"

Wayar shi ya zaro ya dan koma gefe, likitan shi ya kira, Umma kuwa zama ta yi a gefen Zeenat wadda ke kallon gefe idon ta bude kamar ta na kallon su, amma ruhinta sam ba ya tare dare su, hawaye ne mai zafin gaske ya sauka a idon Umma, wadda tai saurin goge shi tare da riqe hannun Zeenat din, wanda ya bushe kamar icce, ba wani jini a jikin ta, Mama na gefe na sharar hawaye, rayuwar duniya ba a bakin komai take ba, muryar Hasheem ce ta karade dakin.

"Ehh, ni ne, ka samu dakin da na ce maka da za a kwantar da Madam din?...."

Ta can bangaren likita sake kallon wayar ya yi, ya na mamakin da wa ya ke magana, tabbas Hasheem ne, to wace madam? Kuma yaushe sukai magana akan kwantar da ita, bai gama mamaki ba, ya ji magana qasa qasa,

"Dalla malam ka sama min gado da daki mai kyau gamu nan zuwa?"

"Ok to sai kun zo,"

Cikin daga Murya da alamar godiya Hasheem ya ce,

"To Dr. Na gode Allah ya saka da alkhairi, gamu nan zuwa,... to sai mun zo"

Hasheem na gama wayar shi ya koma ya durqusa gaban Umman Zeenat ya ce,

"Umma za mu tafi asibitin sai mu je da ku dan ku ga waje ko?"

"To"

Tashi ya yi, ya nuna wa Waleeda wajen da za ta zuba kayan Zeenat, da duk abinda za a buqata,Hasheem fita ya yi,ya zagaya zuwa dakin da ya ke tsaface-tsafacen shi, kwallin shi ya saka da ke qara masa kwarjini,sannan ya daura layar shi da ke sawa in ya bada umarni magana ta zauna, dan bai san me zai je ya zo ba, musamman da Ummaa a kusa, ta na da tsare waje, ya na jin shakkar ta ainun.

Ya na gamawa ya zagaya ya koma gidan, a tsaye ya ga Waleeda da akwati ta na jiran a bude maba boot ta saka, kallon shi tai da tuhumar daga ina ya ke? Kauda kai ya yi, ya bude mata boot din da kan shi ya shiga mazaunin driver ya ce ta fada masu ya na jiran su a mota.

Komawa ciki ta yi, ta fada masu, Umma na qoqarin dago Zeenat ta ji ta kamar kwarangwal, sake ta tayi ta koma gefe ta sake kukan tausayin diyar ta,Zeenat ce ta koma haka?

Hajiya ce ta taimaka ita da Mama suka fitar da Zeenat, kowa kuka yake,Hasheem da ya hango su daga nesa kada idanu ya yi sama, cikin jin haushin yanda asirin shi ke qoqarin tonuwa, ga dai dukiya iya dukiya sai bunqasa take, duk wani alkhairi samin shi ya ke, da alama wannan zaben da mutane ke son ya zama Senator ma zai samu, kowa na ganin mutunci da nagartar shi, ba su da masaniyar halin shi mara kyau ko guda d'aya, suna daf da isa kusa da motar ya fita da sauri, ya bude baya, tare da amshe Zeenat din a hannun su, ya kwantar da ita a motar, Umma ta zauna a baya ta dora kan zeenat a cinyar ta, ta na ta tofa mata addu'o'in samun sauqi, Mama ta zauna a gaba, Hasheem ya shiga ya ja su zuwa asibiti.

Sun yi tafiyar awanni biyu da rabi kafin suka isa asibitin, na kudi ne, mai kyaun gaske, su na isa aka kawo gadon daukar marasa lafiya,cikin sauri aka daga ta aka dora, sai cikin asibitin, kusan duk wanda aka wuce ta kusa da shi da Zeenat sai ya tausa mata.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now