ALBASA BATAI HALIN...40

410 43 14
                                    

Fara ce tass, irin farin nan mai daukan hankali, idanun ta manya masu sanye da kwallin da ya qawata su, sai dogon gashin da ta qara a kan ta, wanda da alama ko da batai qarin ba ta na da gashi, amma rashin godiyar Allah ya sa ta qara, hannayen ta sun sha farata dogaye masu kalar ja, shigar ta irin ta turawa ita da tsirara duk daya suke, drivern Hasheem baya ya ja sosai, saboda ba zai iya jure kallon ta a haka ba, tun daga yanayin zaman da tai za ka gane akwai ta da mazaunai sosai, qirjin ta kuwa kamar su tsone idanun mai kallon su,Hasheem baki ya sake ya na bin ta da kallo, cikin fari da walwali da ido ta ce,

"Me ye haka? Kun tsayar da ni kuma kun tsaya kallo na? In ba ku da abin yi ni ina da shi"

Hannu ta saka za ta murda key din motar Hasheem ya yi sauri dakatar da ita,

"Taimako nake so mota ta ce ta lalace, ko ki taimake mu mu shiga gari sai ya dawo da mai gyara, ko ki ara mana kayan gyara in ki na da su,"

"Ka san me ya baci a motar ne da in na ara maku kayan gyara za ku iya gyarawa?"

Cike da isa da izza take maganar, muryar ta ba qaramin daga hankalin Hasheem ya ke ba, yau da ace shi ya na zina da wasu matan ba abinda zai hana ya neme ta,amma dole ne ya yi abota da ita, dan ta mishi.

"Ahh ah dama za mu dai gwada ne, bamu sani ba ko sa'a na tare da mu"

Murmushi ta yi, haqoran ta masu dauke da hushirya siririya, suka bayyana, bude murfin motar ta tayi, gaba daya, wani qamshi ya daki hancin shi, wanda ya fi na da, kallon santala santalan cinyoyin ta ya yi,ya hadiyi yawu, sanye take da wani takalmi da ya rufe qafafun ta har zuwa qaurin ta,cikin takun isa da qasaita ta isa gaban motar ta bude ta tura hips din ta baya, tare da banqare qirjin ta, duk yanda ta motsa juyawa suke suma, dirver dai kan shi na qasa ya na ta istigifari, Hasheem kuwa ba abinda yake sai lumshe ido da jin dadin kallon da yake, kamar a mafarki ya ji muryar ta,

"In ka gama kallon free show din ka fada masa ya shiga ya tada motar mu gani"

Da sauri ya hau kame kame, ya na musanta abinda ta ce,

"Ka ga ba musu in ka na so, ba ka da matsala, mazan Abuja zani rabawa, amma fa sai wanda ya ci ya tada kai, in ka na da manyan kudi all this will be urs, what do u say?"

Cikin wata iriyar tafiyar daukan hankali, da kwadaitar da mutum akan abinda yake gani take masa maganar, idon shi kuwa sai sake lumshewa suke tsabar jaraba.

"Kaiii duba ka gani, duk da na san zai wahala mace ta san kan mota"

Murmushi ta yi sannan ta kama qugu ta dage hannu daya zuwa bakin ta ta hura dogayen faratun ta, sannan ta kalle shi,

"In mace na yawan hawa mota ta yi tafiya mai nisa kamar namiji mai zai hana?"

Hasheem ya bude baki dan yin magana kawai ya ji kukan motar shi ta tashi, cikin sauri ya kalle ta, tuni ta fara takun ta cikin yanga da qasaita ta na komawa motar ta, mazaunan ta kamar a kira su su amsa sabida motsi da suke, Hasheem bai san sanda ya taka da gudu ya bi bayan ta ba, daf da ita ya tsaya, ta na juyawa gashin ta ya sauka a fuskar shi, shaqar qamshin ya yi, ya lumshe ido, dora hannun ta tayi a qirjin shi, sannan ta masa rada.

"Me ne ne na gudun, ai ba guduwa ka ga na yi ba, card di na zan baka"

Hannu ta sanya a mota tare da juya masa baya mazaunan ta na gogar jikin shi, ta dakko katin ta ta saka masa a aljihun gaban rigar shi, sannan ta hura masa iskar bakin ta, ta daga masa yatsa biyu ta fada motar ta, Hasheem daskarewa ya yi a wajen,har ta bar wajen bai matsa ba, sai da drivern shi ya mishi magana, sannan ya bi bayan shi.

"Maza ka yi gudu mu isa saboda na makara already,"

A qasan zuciyar shi so yake su kamo wannan baiwar Allah da ya gani, amma ko qeyar motar ta basu gani ba, wataqila saboda gudun da take shararawa ne ya sa.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now