ALBASA BATAI HALIN.....3

431 45 4
                                    

Ranar Iyayen Zeenat sun za ci tana da aljanu ne, irin rashin mutunci da kuka da haukan da ta dinga musu, sai da mahaifin ta ya Mata duka, ya sa ta a dakin shi ya kulle ta, ya fice wajen aikin shi, ya bada Umarnin kar Wanda ya bude ta, in sallah za ta yi akwai komai a dakin, a binci su Bata ta taga, bakin ta bai mace ba, Fadi ta ke ta na kumawa in ta auri Qaseem Allah ya tsine Mata.

Mahaifiyar ta tun tana Jin haushin ta, har ta Fara Bata tausayi, ta taga ta tsaya, ta fara Mata nasihar da da wata ce ba Zeenat ba, wata qila za ta dauka.

"Haba Zeenat , wanna halayyar da ki ke yi na matuqar bani mamaki, Kamar ba yarinyar da na Haifa a ciki na ba, Kar ki Manta mu fa iyayen ki ne, kin San ba za mu taba Kai ki inda za ki wulaqanta ko ki wahala ba, mu na son ki, ke ce Kwan mu da muka Fara gani a duniya, wanne irin gata ne da iyaye su ke ba wa yaran su ba mu Baki ba? Qarshen gata bai wuce iyaye su ba ma yaran su tarbiyya ta gari ba, sannan su zaba masu Miji na gari, ga shi ke kin samu, Amma ba ki karbar ko daya a ciki, tarbiyyar kin watsar, yanzu mijin ma kin ce ba ki so, haba Zeenat ,ya ki ke so na yi da rai na ne?"

"Ummaa indai da Ku na so na, da ba Ku zaba min Qaseem ba, me Qaseem ya ke da shi da har zai kula da ni? Wace iriyar rayuwa ta talauci da qunci zan fuskanta a gidan shi? Ki duba ki ga fa Umma shi kan shi ba kalar mijin da na ke qauna bane, baqiqqirin da shi Kamar gawayi, Ummaa ina son Miji Kamar ni, kyakkyawa, Mai kudi, Amma Ku rasa Wanda za KU ban sai Qaseem, kashe Kai na zan indai ba KU janye wannan maganar auren ba"

Ganin ba amfanin yin magana da Zeenat domin ta Yi Nisa, sai Umman ta ta Mata addu'a da fatan shiriya, ta tafi dakin ta.

Mahaifin Zeenat ya Mata horon da dik zai iya, Amma ta qi amincewa, sai ma sake hango muni da talaucin Qaseem ta ke, tare da tsana Mai tsanani, saboda ta na ganin saboda shi ne kowa ya ke juya Mata baya.

****************************

Qaseem ya dage sosai wajen Neman kudi, a ran shi Yana tunanin addu'ar da ya Yi, na Allah ya zaba Masa abinda ya fi alkhairi, Kuma an saka Rana, to wataqila auren ne alkhairi,Dan haka ya dage sosai wajen Neman kudi, so ya ke ya Tara kudin aure na gani na fada,Dan ya burge Zeenat, ko hakan zai sa ta so shi.

Mahaifiyar shi ta shiga damuwa ainun, ganin yanda ya maida kan shi Kamar agogo, ba hutu, abinci ma ya kan Manta da ya ci ko bai ci ba.

Watarana ya fita kasuwa tun bakwai na safe, bai samu ya karya ba, haka ya dinga hada Hadar kasuwanci, har akaii azahar bai karya ba, sai ruwa da ya sha, ya yi alwala zai ta da sallar La'asar kenan, ya yanke jiki ya Fadi, Nan fa mutane su ka yo kan shi, bakin Nan a bushe, maqocin shi ne a kasuwar ya ce,

" Anya kuwa ba yunwa a tattare da Qaseem , yau ma ban ga ya ci abincin Rana ba,"

Nan aka fara cece ku ce, wani bawan Allah ya siyo fura da nono damamme da ake sayarwa a gora, suka zaunar da shi a kujera aka bashi ya Sha, Nan fa ya samu hankalin shi ya Fara dawowa jikin shi, sai da ya samu nutsuwa sosai, sannan kowa ya Fara fadin albarkacin bakin shi, sukai ta Masa fada akan ya na kula da kan shi, wasu suka dinga mishi dariya, suna fadin tunanin aure ne ya sa ya shiga halin damuwa.

Ranar ka fin lokacin tashin shi,ya tashi, sai da ya biya ta chemist ya hado magani, dan Mai chemist din ya ce Masa da dikkan alamu a bayanan da ya Masa ya na kyautata zaton ulcer ke damun shi, ya je gida ya tadda Mata masu siyan dankunnaye da sarqa da abun hannu, sun zo su na ta duba kaya, Dan haka dakin shi ya shige ya Basu waje.

Inna ce ta bi shi da abinci da ruwa, ta gan shi kwance Kamar Mara lafiya.

"Qaseem me ya ke damun ka ne? Yau ga shi ka dawo ba lokacin tashi ba?"

"Innata ban Dan Jin Dadi ne, Amma jiki na da sauqi sosai, na ma biya ta chemist na siyo magunguna"

Da sauri ta duqa ta taba goshin shi, da wuyan shi, zafin da ta ji ne ya Sanya ta Zama sosai a saman Yar katifar shi, tana jera mishi sannu,

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now