ALBASA BATAI HALIN..25

487 51 8
                                    


"Zeenatu ke fito mun iso"

Kaka Fatu da ke dauke da Fateema CE ta taba kafadar Zeenat wadda tai suman zaune tsabar mamaki,cikin sauri ta daga kan ta ta kalli kowa da ke wajen, musamman suhailah da ke tsaye cikin zumudi da murnar ganin ta, idon ta ya rufe tsabar masifar da ta ke ji a cikin ran ta, da azama ta Sa qafar ta a waje, ta taka har gaban Qaseem, Wanda ya ke kallon suhailah da so da qauna, ba Dan komai ba sai dan kyakkyawan halin ta, a lokaci Daya ya na tausaya Mata, Dan ya San sai Zeenat ta ci Mata mutunci, Amma ba zai iya hana ta abinda ta ke so ba, a shirye yake da ya Kare dik wani cin mutuncin da Zeenat za ta ma suhailah, zai iya jure komai, Amma Banda taba Masa Mata.

Qanqance ido Zeenat tayi, sannan ta nuna Qaseem da yatsa,

"Me na ke gani? Daga Ina kuke Kai da suhailah?"

Har ya budi Baki zai magana, sai Kaka Fatu ta ce, su shiga gida, maganar ba ta waje ba ce, cikin d'an daga murya Zeenat ta ce,

"Ban damu da dik inda za a yi maganar Nan ba, damuwa ta shi ne, KU sanar da ni me suhailah da Qaseem suke yi a tare,"

Cikin Dan hasala Qaseem ya ce,

"Aure muke Yi a tare, ki na da wata matsala ne?"

Wani irin ashar Zeenat ta zabga, tare da juyawa kan suhailah a guje, mutanen cikin gida ne su ka leqo Dan Jin hayaniyar da ke faruwa' qofar gida, tunda sun San da zuwan Zeenat ,ga Kuma muryar ta Nan har cikin gida.

Qaseem taku hudu ya yi ya fizgo Zeenat Baya, sannan ya zaro Mata idanun shi Wanda a da ta ke ma tsananin qiyayya, yatsan shi manuni ya nuna Mata ita kuwa ba abinda ta ke kallo illa fuskar shi da gemun da ya Tara Mai Dan yawa, Wanda ya qawata fuskar shi, bakin ta ya bushe ba ko yawu a ciki, idanun ta kuwa masifa kawai suke bayyanar wa da tsantsar kishi.

"Zeenat Kar ki kuskura ki taban Mata, zan Manta da cewar ke surukata CE yanzu na babballaki, ki sani Qaseem din Zeenat Mai hakuri ya Jima da mutuwa, wannan Qaseem din suhailah ne, Mai qoqarin Sanya ta farin ciki, ko da kuwa zai Batawa wata ko wani ne"

Yarfar da hannun ta ya yi, ta yi taga taga kamar za ta fadi, Allah ya Bata sa'a ta tsaya da qafafun ta, Kaka Fatu da mutan gidan, duk sun shige ciki, Hashim na tsaye ya na kallon ikon Allah, suhailah ma ba a barta a waje ba, ta bi bayan su Umma, Qaseem da Hashim su na tsaye su na kallon juna kafin da ga baya Hashim ya gabatar da kan shi a matsayin Wanda zai auri zeenat, Qaseem ya gabatar da kan shi a matsayin Mijin qanwar Zeenat, Hashim ya so ya tambayi Qaseem abinda ke faruwa' amma ya yi shiru, ba damuwar shi kenan ba, damuwar shi daban da ke zuciyar shi, Dan Haka suka wuce masallaci, Dan gabatar da sallar azahar.

Umma ba abinda ta ke sai zubar da hawaye, Kaka na Mata fadan ta daina ma diyar ta kuka, sai ta sake lalacewa,

"Kaka na kasa gane irin halayya ta Zeenat ,ya ta ke so mu Mata ne? Yanzu bayan watanni masu yawa ki duba ki ga abinda ta Yi daga zuwan ta, ta Tara Mana maqota, da ma rannan har magana aka yarda min, Wai na Yi qiba na yi kyau, lalurar gabana ta tafi,za su zuba ido su ga in ta dawo ya zan koma, yanzu Kaka ta kyauta min kenan, ta kyautawa kan ta? Ace yarinya ta girma amma halayyar ta na sake tabarbarewa?"

Dafa kafadar ta Suhailah ta yi sannan ta ce,

"Ummaa Dan Allah ki daina kuka, gaskiyar Kaka ne, kukan iyaye musiba ne ga yaran su, sai su sake lalacewa, ki share hawayen ki, da addu'a watarana in an tuna Mata za ta qaryata ko ta ji kunyar abun"

"Uban ki ne ya ce zan qaryata? Yar cin amana, kun ci Amana ta gaba Dayan ku, ba zan taba yafe muku ba, miji na za KU aurawa qanwata, wannan wanne irin cin Amana ne,"

Cikin fushi suhailah ta ce,

"Ke me ya sa ba ki da hankali ne Zeenat , wa ye Mijin naki? Mijin da ki ka wulaqanta ki ka tozarta, sannan ki ke qi kamar ki kashe kan ki da shi? Ki din ga Abu ki na tunani, wancan ba Wanda aka ce za ki zo da shi ba ne ya ga Baba saboda ya na son auren ki? Me ki ke tunani in ya ji wannan rashin hankalin da ki ke aikatawa, ki duba mahaifiyar ki ki ga yanda ta ke zubar da hawaye akan ki, ke hakan ba ya damun ki? kin Gama Bata ma kan ki suna, da na iyayen ki dik Dan saboda rashin kunyar ki da rashin iya magana...."

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now