ALBASA BATAI HALIN...10

457 46 9
                                    

Ko da ya shiga dakin a zaune ya gan ta a qasa, ta jingina da jikin gadon, qafafun ta a takure da jikin ta, kuka ta ke mara sauti, amma da ka kalli idanun ta za ka san ta jima ta na kukan, wanda ya gadar ma ta da ciwon kai.

Kunna fitilar dakin ya yi, su ka hada ido, wani sanyi ya ji a ran shi, ji ya ke ba zai taba iya tsanar ta ba, saboda he loves her so much,duk wani laifi in ta yi ba ya iya dade mishi a zuciya, musamman kan zai gan ta.

Miqewa ta yi tsaye da kyar, har ta na qoqarin faduwa, saboda jiri, da kuma tsami da qafar ta ta yi, da sauri ya sa hannu zai taro ta, wani irin zafi zauuu ya ji jikin ta ya dauka, cikin sauri ya sake kai hannu dan rungumar ta, tausayin ta ya gama cika zuciyar shi, wata bangaza ta mishi, ya yi baya, tare da kallon ta,

"Kar ka kuskura ka taba ni, za ka yi danasanin sani na a rayuwar ka baki dayan ta, idan yawon iskanci za ka na yi, ka dinga kwana a can dakin Innar ka in ka dawo,kar ka kuskura ka shigo min gida a irin wannan lokacin, iskancin da ka ke min a gida bai ishe ka ba, sai ka fara bin na waje ko?"

'A'zubillahi minasshaidanirrajim'

Abinda ya ke ta maimaita wa a ran shi kenan, saboda kauda bacin ran da ke ran shi,yau shi ake yi wa zargin zina? Yana saurayi ma bai yi ba balle da auren shi, tunda ya ke a duniya bai taba son wata mace ba, bayan ita, kuma ga ta ya same ta, a na shi tunanin ma, ko iskanci mutum zai yi ai sai yana son abokin iskancin nashi, ko kuma akwai wani abu dai da ya burge ka da shi, shi kuwa wata mace bata taɓa burge shi ba, bayan Zeenat amma ta ke masa wannan mummunan zaton, wani abu mai daci ya hadiya, ya zagaye ta, ya yi shirin wanka, ya sake fita, ta na ganin ya fita, ta sauke ajiyar zuciya, a qalla ta quntata ma zuciyar shi, sanda ya gaji zai sake ta ne, kuma gashi ta sha bai mata muguntar shi da ya saba ba.

Hayewa gado ta yi, bacci mai nauyi ya dauke ta nan take,shi kuma sai da ya yi nafila, ya sake roqon Allah, idan da alkhair a zaman su, Allah ya tabbatar, in Babu Allah ya musu zabin abinda ya fi alkhair, sannan ya yi shirin bacci, ya feshe jikin shi da turaren shi mai daɗin qamshi.

Ko da ya hau ya ga tayi bacci sai ya miqa hannu jikin makashin fitila, dake daf da qofar shiga, ya kashe, ya yi addu'ar bacci ya shafi jikin shi, sannan ya yi wata addu'ar ya fara shafa mata, dan ba gwanar yin addu'a bace, cikin bacci ta ji ana shafata, ta fara miqa, tana sake tura mishi jikin ta, ai kuwa bai bata lokaci ba wajen sake manna ta a na shi jikin, ya na sunsunar ta, kissing din wuyan ta ya fara, zuwa saman qirjin ta, qara banqaro mishi qirjin ta take, kamar wadda aka mare ta, haka ta farka, tare da bude ido sosai, duhu dakin, dan haka bata ganin komai, wani irin duka ta kai, a inda ta ke zaton fuskar shi na nan, cikin sa'a kuwa ta same shi, ji ya yi an zabga masa mari a saitin idanun shi, sai da ya ga wuta ta yi walll ta gifta,dafe wajen ya yi, ya hau kiran sunan Allah.

Qoqarin sauka ta fara yi a gadon, ya na jin haka ya janyo ta jikin shi, ya mammatse ta, sannan ya fara cire mata kayan jikin ta,duk wani kuka da ihun ta ba ya ji, sai da ya cimma burin shi, sannan ya kwanta a gefen ta, ya na sauke numfashi, idon shi a kulle, ya janyo ta jikin shi, ya na shafa bayan ta, ta ci kuka ta gaji, ta yi kokawar kwace kan ta, har bata da wani sauran qarfi a jikin ta.

A haka suka yi bacci, saboda gajiya, sai da asussuba ya kai musu ruwa ya ce su yi wanka tare da ta qi, sai da ta ji motsin Inna na son fitowa ta fada bayin, ba wai dan tana jin kunyar ta ba, ah ah sai Dan Kar ta ga ta sake da dan ta ta zata ko ta fara son shi ne, a mazubi daya suka yi wanka, Inna kuwa da ta ji motsin mutum a bayi, sai kawai ta koma dakin ta, ta zauna, dan jiran koma waye ya gama abinda ya ke ya fita ta shiga.

Suna gamawa suka fita a tare, ya na riqe da bokitin, ya ajiye, suka shiga daki, sai da aka dan jima Innaa ta tabbatar sun bar wajen sannan ta je ta yi alwalar ta ta koma daki itama, shi kuwa masjid ya tafi.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now