ALBASA BATAI HALIN..51

490 56 15
                                    

Shimfida masu tabarmar ta yi tare da fadin,

"Sannun ku da zuwa Aunty, bismillah, ciki akwai zafi, gashi ba waje sosai,"

Wani kallon tara saura kwata suke bin ta da shi, Zaituna kuwa ganin yanda a cikin qanqanin lokaci Nawwarah ta sauya ne ya ke nuqurqusar ta, jikin ta ya yi dumui-mui, ga gashin ta ya sha gyara sai daukan ido take, asalin Nawwarahn da ta dawo,fess da ita gwanin sha'awa, cikin hargowa ta fara magana,

"Ba zamu zauna a tabarmar ba, na ce ba zamu zauna ba din, ciki za mu shiga, in wajen bai isa ba ba uwar daka ne?"

"Akan me za a shiga mana uwar daka? A nan ta muku shimfida ku zauna anan, in ba za ku zauna ba kowa ya kama gaban shi,ba wanda aka kaiwa goron gayyatar zuwa nan gidan, ko akwai?"

Gaba dayan su juyawa sukai banda Nawwarah da ta sauke wata ajiyar zuciyar da bata san ta na riqe da ita ba, a baya hankalin ta ya tashi ta ya za ta cika umarnin mijin ta? Sai ga shi ya dawo kawo mata abincin rana, ya ji me suke muhawara akai, ran shi ya baci da jin yanda suke muzanta ta, dan haka ba wadda ya ke tsoro cikin su, zai maganin su yanzunnan.

"Aqilu ni ka ke mayarwa da mara sugar? Ashe baka da mutunci? Ina maka kallon shiru shiru ashe tantiri ne kai, ina fada ka na fada ko? To na rantse za ka ga iskanci, indai na isa da Jafaru,sai ka sako ta, kuma sai ka bar aiki a shago,"

"Saki kam tunda ba shi zai sakar min ita ba ba mai yuwa bane, aiki a shago kuwa inna bari ku ne a qasa, saboda ni ne qarfin riqe shagon naku, ba zai iya rabuwa da ni ba in ba ke za ki je yi masa zaman shagon ba, sannan ko yau na bar wajen ku ina da wajen aiki kala kala ba iya ku na ke wa aiki ba, ki tambaye shi ki ji, haka kawai ki zo har gidan yarinya ki nemi ci mata mutunci da ke da wadannan guzumomin matan? Ba zai yu ba,"

Kuka Zaituna ta fashe da shi ta sa kai waje da sauri, sauran matan kuwa cece kuce suke ta yi akan an wulaqanta su, wasu a cikin su dama munafukai ne, sun tsani Zaituna,ana tare ne kawai dan su na dangwalar arziqi,sun ji dadin abinda aka yi mata,ko da suka fita a bakin titi suka cimmata ta na tsaida machine za ta koma gida.

Tun a hanya ta fara kiran Jafaru, da ya dauka ya ji ta na kuka, da kyar ta ke magana, ta na fada masa su hadu a gida, ba bata lokaci kuwa ya rufe shago, ya nufi gida.

Aqilu kuwa ganin yanda Nawwarah ke kuka ne ya bashi mamaki, tsayawa ya yi a gaban ta ya daga kan ta,tare da share mata hawayen da ke zuba da gudu,

"Me ne ne kike kuka qanwa ta?"

"Ni dai mu bi ta mu bata hakuri, sharrin ta na da girma, ban san me za ta fada ma Uncle b, shi kadai ya rage min a dangi na da ke so na, kar ta bata ni a wajen shi, dan Allah mu je mu bata hakuri, indai dakin ne ta shiga ba komai,"

"Ba za ta shiga dakin ba, kuma gidan nan ma kar ki sake bude mata qofa, ki dinga rufewa in aka buga sai kin ji waye sannan ki bude, ta dade ba ta je ta fada masa ba, Nawwarah ni ban ishe ki zama dan uwa ba? Ki na ganin ba zan iya kula da ke kamar yanda iyayen ki suke kula da ke ba? Ki na ganin ba zan iya maki son da suke miki ba? Ki dai na wannan tunanin, Nawwarah zan maye maki gurbin duk wani masoyin ki da ki ka rasa, ba zan bari ki wulaqanta ba indai ina raye, zan aiki da jiki na domin sama maki farin ciki, share hawayen ki kinji 'yar qanwa ta"

Murmushi ta fara, ya na bin saman idon ta da kallo, wanda ya ke dauke da gashin ido masu matsakaicin tsaho, hancin ta ya tafi sambal ba karkata, lips din ta sun yi kalar ja saboda kukan da ta yi, Aqilu bai san sanda ya dora nashi lips din a nata ba, da fari zaro ido ta yi saboda bata yi zato ba, daga baya ta lumshe idon ta, ta na karbar saqon abinda ya ke mata, bata san ya zata mayar mishi da martani ba, dan haka tsayawa ta yi ya ke sarrafa labban su zuwa harshen su.

Tunda take bata taba jin abu mai dadi irin wannan ba, a hankali ya zare bakin shi, ya dora goshin shi na nata, idanun su a rufe su na maida numfashi cikin sauri, ya saqale qugun ta ya manna a jikin shi,a hankali ta janye kan ta ta dora a qirjin shi ya sake rungume ta da kyau, duk ta sake jikin ta a nashi, shafa bayan ta ya fara sannu sannu, wani irin dad'i ke ratsa ta, har ta fara lumshe idon ta, ta na son yin bacci, ya na kula da hakan ya kama hannayen ta ya kalli fuskar ta, ta kasa hada ido da shi, sai cizon leben ta na qasa take, cikin jin kunyar shi,

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now