ALBASA BATAI HALIN...52

456 50 16
                                    

Da kyar Aqilu ya kauda kan shi a wajen Nawwarah,ba tare da ya samu biyan buqatar shi ba, ya na kwance a dakin shi lamoo, tunani ya masa yawa, ta hanyar da ya kamata ya bullo mata dan cimma burin shi akan ta, lokaci ya yi, Nawwarah ta zama cikakkiyar mace, ta zam macen da kowanne lafiyayyen namiji zai so kadaicewa da ita, balle shi da ya ke ganin giftawar ta a kullum, ya ke hakuri,ga shi zuwan Zeenat, zuwa ne akan taimakon da ya ke son ta musu na ci gaba da karatu da ya ke son Nawwarah ta koma kano da yi,ba ya son ya dakushewa yarinya mai dumbin basira kamar Nawwarah basirar ta, ya na son ta fi shi zama mai ilimi, tunda ta na da dama, shi zai bata dama, sai in ita da kan ta ta ce ba ta so, in ta tafi kano weekends sai ta na dawowa, haka yake fata, amma bari Zeenatu ta zo ya ji irin shawarar da za ta bayar.

Nawwarah ta kammala kwalliyar da ta ke cancadawa, ta tsaya bakin qofa, sai zuba qamshi take, riqe da madubi a hannu, kwalawa Aqilu kira ta yi, kamar wanda uban gidan shi ya kira, haka ya miqe da sauri, komai ya tsaya mishi cak a daidai lokacin da suka hada ido da ita, lafewa ya yi a jikin gini, ya daddafe shi da hannayen shi biyu, kamar wanda aka hana qarasa fita,

'Me ya sa ta ke son kwancen dan sauran tsaron nawa ne?'

"Yah Aqilu na yi kyau? Ka na ganin Mommana za ta ce na girma sosai?"

"Kwarai ma kuwa, Nawwarah ban ga na biyun ki a kyau ba duk garin nan,da sauran garuruwan da na taba zuwa, girman ki kuwa abin mamaki ne, kamar ba ke ce yar mitsitsiyar yarinyar nan ba, da ko qirgen dangi bata fara ba, dube ki yanzu masha Allah, kamar wata babbar budurwa a birni"

Wata iriyar kunya ce mai tsanani ta kama ta, musamman da ta kula da yanda ya kafe qirjin ta masu yalwar cika da ido,yanayin shi gaba daya ya sauya, a yanzu Nawwarah ta san me ne ne so, ta san me ne ne sha'awa, sannan ta san ya ake zamantakewar aure, ita kan ta lokuta da dama ji take dama Aqilu ya karya dokar shi, ya kwana da ita, she really needs him by her side, daki ta shiga da sauri ta maqale jikin gini inda makunnin fitila da fan yake, Aqilu bin ta ya yi ya leqa ta ba tare da ta san ya na kallon yanda ta maqale a gini ba, ta na fidda numfashi mai wuyar fassara, idanun ta rufe, hannayen ta a saman wuyan ta, a hankali ya fara takawa, ya dora qafar shi ta dama kenan dan shiga dakin, ya ji sallama, hade da kwankwasa qofa, wani irin burki ya ci, da shan kwana, ya nufi bakin qofar, tambayar waye ya yi,kafin a bashi amsa da cewar Zeenat ce, cikin azama ya bude qofar tare da yin baya.

Fatee ce a gefen ta, riqe da jakar Zeenat, sai wata leda, Zeenat dauke da wata 'yar qaramar jaka, dayan hannun ta wayar ta ce da makullin motar ta da ba ta jima da siya ba.

A ladabce Aqilu ya ke mata sannu da zuwa, tare da maida kan shi qasa,ya n matuqar ganin qimar ta, kamar wanda aka kama hannu dumu dumu da abin kunya, a hanzarce ya leqa dakin Nawwarah ya ce mata,

"Momma ta iso fa,"

"Haba dan Allah?"

"Da gaske, gasu can a waje,"

Da dan gudu gudu ta wuce shi, ta na zuwa ta fada jikin Zeenat cike da murna, sannan ta sake ta ta rungume Fatee da ke mata murmushi, murna kamar ta jima kwarai basu hadu b, shigar da su parlour ta yi, ta hau hidima da su, Aqilu na taya ta miqa abinci da abinsha da ta tanadar musu.

Bayan gaishe gaishe, suka zauna yanke shawarar yanda Nawwarah za ta koma Kano d zama, dan fara karatun Nursing, a qoqarin su na son taimakawa al'ummar musulmi musamman mata, da za ta samu admission cikin sauqi a bangaren medicine da shi ya fi son ta yi, amma wannan din ma ba komai duk daya ne, sun gama tsara duk yanda komai zai kasance da izinin Allah, sai dai Zeenat ta kula da wasu abubuwa game da su, in hasashen ta ya yi daidai, da alama, har yanzu Aqilu bai angwance ba, lallai dole ne yau ta kawo qarshen komai, sallama Aqilu ya musu, ya fita daga gidan dan basu waje su sake.

A hankali da dabara kuwa Zeenat ta samu bayani daga bakin Nawwarah, ta jinjinawa qoqari irin na Aqilu,wannan shi ne dalilin da ya sa ya ke azumin litinin da alkhamis,tabbas za ta taimaka musu wajen cikar burikan su.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now