ALBASA BATAI HALIN...15

484 43 8
                                    

Baba na kaisu ko gidan bai tsaya shiga ba, ya wuce majalisar da zai samu qanin shi,su ka gaisa ya mishi bayanin komai, Baffa Nura ya jinjina lamarin sosai, sannan ya ce ma Baba .

"Ba bu komai Yaya Sule yanda duk kace haka za a yi, in Allah ya yarda sai dai ku ji alkhairi,Allah ya shirye ta"

"Ameen na gode Nura, na san kai ma kana da na ka iyalin, ga su qanana, amma in Allah ya yarda, zan dinga aiko maku, kudi, sai ku qara wajen kula da su, baki daya, Allah ya qara zumunci"

"Ameen, Allah ya kiyaye hanya, na san ba za ka kwana ba"

"Kar ka damu Nusrah yanzu ko na ce zan kwana a gida sai dai shago, mutum mai iyali kuwa yaushe zai tsaya kwana a shago"

Cikin raha suka rabu da juna, ya kamo hanyar komawa Kano.

Zeenat kuwa tunda ta qule a dakin Kaka fatu ta qi fita, yaran gidan qanana sun shiga sai fullanci suke ,su na so suga yayar su ta binni, amma ta qi fita, Matar Baffa Nusrah amaryar sun rabu, ba jimawa, uwargidan Ummalo ce a gidan, ita ke kula da dukkan yaran gidan,aiki ya mata yawa matuqa, amma ba yanda za ta yi, tunda jarabtar ta ta sa amaryar ta bar gidan.

Tattare kan yaran ta yi,ta na ta masifa, kowa ya bar wajen, dakin inna ta shiga ta zauna, su ka hau gaisawa, Zeenat kuwa yanda ta bata rai, ba mai tunanin ma za ta yi magana, saboda da alama ba ta da niyyar yi din, sai shayar da diyar ta take.

"Kaka lafiya kuwa? Me ya samu Zeenat na ga kamar ta yi kuka?"

"Rashin azziqi ta je ta yi a gidan mijin ya sako ta, shi ne muka tattaro mu ka dawo nan da ita"

"Wayyoo Allah, dama na san za ayi haka, irin tijarar da Zulfa'u ta ce ta na musu, ai ba mai jurewa, ai shi kenan, Allah ya sa da rabon komawar ta, sai a daidaita ta koma"

"Allah ya kiyaye, ko mijin da na ke so ne ya min sakin nan, na bar auren, ballantana wani wawa Qaseem ,sai me dan na rabu da shi, shi kadai ne namiji?ko shi daya ne zai so ni?"

"Ba shi kadai ba ne kam, amma kan ki samu, ina mai tabbatar maki da za ki wahala, kan ki samu kamar shi"

"Bakin ki ya sari danyan kashi mai doyi ,ai abinda zai hana ni samun miji nan kusa shi ne, zama na a qauyen nan, na san shi ne kawai matsala ta"

Wani irin kallo Ummalo ta bi ta dashi, na ni ki ke wa rashin kunya? Za mu gauraya ne, a zahiri kuwa ta ce,

"Allah to ya kawo mai albarka Zeenat, ai darajar diya mace shi ne dakin mijin ta, ko ba dadi"

"Ahhh to fada mata, ita ya za ai ta sani, tunda ta ballo na ta auren ta taho, ga shi nan, sai mu yi ta zama, ki ji ya zawarci ya ke, in kin zata abun dadi ne"

Tsaki ta dan ja mara sauti, sannan ta tashi da jaririya ta a hannu, ta shige quryar daki, ta yi kwanciyar ta, ta bar su suna tattaunawa.

Da dare bayan Baffa Nusrah ya dawo, ya shiga danyin magana da Kaka fatu ,ya tarar da Zeenat ta yi bacci, dan haka ya fadawa Kaka duk abinda suka tattauna da Baban Zeenat a game da zaman ta anan din, Kaka Fatu ta ji ba dadi, amma ba yanda za ta yi, wataqila hanyar da ta fi dacewa kenan, a yi maganin Zeenat.

***************************

Bayan Zeenat ta yi sallah, ta koma qaramin gadon da kaka fatu ta bar musu dan komawa baccin safe, Ummalo ta shiga, ta gaishe da kaka, sannan ta rangada sallama har cikin dakin, ta ce ma Zeenat

"Mutan binni a fito a taya ni hada kokon safe"

Wani irin dagawa Zeenat ta yi ta kalli Ummalo, cike da raini, sannan ta ce,

"Da da bana nan wa ke dama maku kokon?"

"Da ki ka ce? to da Ni ke damawa,amma yanzu tsarin ya sauya, Baffan ki, ya ce ke za ki na damawa, ki wa yara wanka, sannan ki na abincin dare, da na safe, Ni zan dinga na rana, ke kuma sai ki ji da wanke wanken rana, ina fatan kin fahimta,"

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now