An kafe sakamakon mutanen da suka samu shiga makarantar School of nursing ta kano, Nawwarah na daya daga cikin wadan da sukai nasarar samun shiga makarantar, Zeenat ce ta dubo mata, murna a wajen Nawwarah da Aqilu ba a magana, sai da sukai sallah raka'a biyu domin godiya ga Allah, a sujjadar qarshe Nawwarah ta dinga godewa Allah, da roqon shi sauqi da nasara a karatun ta, tare da bata ikon taimakawa al'ummar Annabi da ilimin da za ta je nema, tai addu'ar Allah ya sauqaqa ma Aqilu samun arziqin biya mata duk wasu kudaden da zata buqata na makaranta.
Bayan kwana biyu ta gama shiri tsaf na tafiya, Aqilu gaba daya ji yake kamar in ta tafi ba zata dawo ba, duk ya shagwabe mata, ita kuwa sai ririta shi take, ta na gatanta shi, ta masa miya mai yawa, ta masa cincin, duk ta ajiye, ta soya masa gyada mai gishiri, da taimakon kaka fatu, ita ma ta diba, duk da Zeenat ta ce kar ta je da komai na abinci ai duk gida ne.
Duk da haka sai da ta debi wasu abubuwan, a rayuwa ba komai za ka zauna ka ce sai an maka ba, rayuwa taimakanni in taimake ka ne.
A tashar tafiya Kano, Aqilu ya marairaice wuya kamar maraya, Nawwarah sai danne hawayen da ke qoqarin sakko mata take, itama sam bata jin dadin tafiya ta bar shi, amma ta san in mutum na son samun wani abu, dole sai ya sadaukar da wani abu, motar su na tashi ta kife kan ta a saman jakar ta ta na sharar hawayen rabuwa da masoyin ta.
Ya jima a wajen, har sai da ya daina hango su sannan ya koma, kasuwa ya nufa, bai koma gida ba, in ya kadaice tunani zai masa yawa, aiki ya dinga nema na kujeru, da kitchen carbinets, da sauran ayyukan duk da ya iya, in ya tashi daga kasuwa ya je, baya dawowa gida sai tara na dare,a gajiye ya ke komawa, da ya yi wanka, ya ci abinci, ko ya hada shayi ya sha da cincin, sai ya kira Nawwarah su sha hira daga baya su yi sallama, sai bacci.
Haka rayuwar Aqilu ke tafiya tunda Nawwarah ta tafi.
A bangaren Nawwarah kuwa, karatun bai mata wahala yanda ta zata zai yi, saboda taimako da take samu wajen Zeenat, daga makaranta sai gida, aiki kuwa ba mai barin ta tayi, sai in ta matsa, Zeenat ta bar mata gyaran dakin da suke kwana, Zeenta ke kai ta makaranta da safe, da yamma kuwa ta koma gida da kan ta.
Satin da ta fara komawa gida, a satin suka yanke shawara ita da Aqilu game da yin tsarin iyali irin wanda larabawan zamanin Annabi suka yi, in sun sadu baya releasing a jikin ta sai a waje, duk da baya wani so amma haka ya hakura dan kawai cikar burin su. Suna tsoron yin na bature, saboda ba su taba haihuwa ba, gwanda wancan da ikon Allah sun san ba za su samu matsala ba.
Duk wata matsala ba su fatan ta gifta a har kar karatun ta, a kullum qara kyautata ma junan su suke, da kuma qoqarin ganin ci gaban junan su, Nawwarah ko a makaranta ta ji labarin aikin da mijin ta ya iya, ba ta girman kai, ko noqewa za ta je ta nema masa, kuma in rabon shi ya ratsa sai a kira shi, a haka rayuwa ta ke tafiya musu cikin walwala, (Wanda ya so jiki zai ga son jiki, wanda ya sa ma kan shi qiwa zai ga qiwa, wanda kuwa ya cire qiwa zai koyi arziqn da ya nema da kan shi).
***************************
"Zeenat yau mahaifin ku ya ce ki jira kar ki fita da wuri ya na son magana da ke"
"Ok, to ummaa, bari na sha shayi to kafin ya fito daga wanka"
Shayi ta hada masu ita da Nawwarah suka sa biredi suka sha, ta na gamawa ta nifi dakin Baban su, zaune ta gan shi yana gyara maballin wuyan rigar shi, bayan sun gaisa, Ummaa da Mama suka shiga a tare, ta na ganin su ta ji zuciyar ta ta tsinke, ba ta san me ya sa aka taru haka ba, ta san ba zai wuce akan maganar da aka saba yi mata bane, wasu hawaye masu zafi ne suka fara zubar mata.
"Kin ga Zeenatu ba na son shashanci, lokacin shiririta ya qare, kin samu cikar burin ki, me kike nema? So ki ke mu zauna muyi ta zuba maki ido? Wato kin ma san me za a ce maki shi ne ki ka fara kuka ko? Wannan karon hawayen ki ba za su yi tasiri ba" cewar Ummaa wadda ta fara gajiya da halayyar Zeenat na qin aure.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...