Hankalin shi na daki wajen Zeenat, Nawwarah na ta zuba shagwaba, Waleedah ta tattare hankalin ta wajen kallo, Hajiya na bashi labarin qauyen Panda da mutanen da ya saba taimakawa, har ma da sabbin da ke buqatar taimako,kamar wanda aka mintsina haka ya miqe ya ce,
"Hajiya ina zuwa, kamar na bar wayata a daki, bari na dakko, ina tsammanin wani kira,"
Ko da ya shiga dakin sai da ya dan dauki lokacin da ba zai wuce minti biyar ba zuwa takwas, sannan ya dawo, jiki na masa rawa, hankalin shi a tashe, kiran sunan Hajiya kawai yake ya na maimaitawa,
"Hajiya...Hajiya....Hajiya... Zeenat ta fadi,Hajiyaa"
Hajiya zani a hannu da yaran suka taka da gudu-gudu zuwa dakin, sai da suka shige gaba ya murmusa, sannan ya bi bayan su, su na shiga suka ga Zeenat kwance a qasa, qafarta a wargaje, kamar wadda aka wurgar da qarfi, cikin salati Hajiya ta duqa ta daga kan ta, ta dora saman cinyar ta, nan da nan Nawwarah ta fara kuka, Waleeda kuwa damuwa ce kwance a fuskar ta, ba su jima ba fa da rabuwa da Momman nasu, me ya same ta?
"Hajiya ta na numfashi kuwa? Dan Allah duba min ita,"
"Ta na numfashi Hasheem, kwantar da hankalin ka, ka kira likita yanzu a duba ta, ko kuma a kai ta asibiti"
Da hanzari ya fara danna lambobin likita, ba bata lokaci ya sanar da shi ya same shi a gida, likita kam haushi ya kama shi, a zaton shi yanzu ma wata ya ji wa ciwo ya ke son a je a gyara masa in ta warke ya ci gaba da morewa.
Daga ta ya yi ya aje saman gado, har lokacin Zeenat ba ta san ina kan ta yake ba, hankalin Hasheem kuwa ya kwanta, dan ba mai zargin shi da yi mata wani abu kuna, tunda gashi ya sakko da ita qasa ya yi qarya ya ce faduwa ta yi.
Bayan likita ya duba ta, ya ce bai ga komai ba, kawai ta na buqatar hutu ne, kamar akwai gajiya a lamarin ta, nan ya rubuta magunguna, ya ce a siyo in ta farfado ta ci abinci a bata, a kuma kula da ita sosai.
Bayan likiya ya yi hanyar fita,Hasheem ya bishi da gudu, ya ce ya na son magana da shi ya biyo shi,wani madaidaicin parlour ne suka shiga, kujeru da komai ba wasu manya bane, amma wajen ya tsaru da kyau, dan jan numfashi Hasheem ya yi sannan ya karkace ya zaro rafar kudi 'yan dubu dubu guda uku a babbar rigar shi, a gaban likitan ya zube su, sannan ya kalle shi,
"Likita bokan turai inji bahaushe...likita ina son mu hada wani kasuwanci da kai in ba damuwa?"
Idon likita na saman kudin nan, kamar za su fado, ya amsa da.
"Wanne irin kasuwanci? Ina ma'aikacin gwamnati da kasuwanci?
"Baka da labarin a yanzu duk wanda ka ga ya na wadaqa da kudi, ko barawon gwamnati, ko dan kasuwa mai tsananin riqon amana, ko dan bokon da ya hada da kasuwanci, ko dan boko mai albashi mai tsoka, ko kuma masu shan jinin mutane dan dukiya"
"Haka ne... Alhaji ka je kan maganar ka kai tsaye, na baro marasa lafiya a asibiti"
"Gaskiya ne...likita maganar da na ke son muyi da kai ba wata magana ba ce face ina son report na qarya...ka hada report akan Zeenat ta kamu da cutar shanyewar jiki, saka makon faduwar da tai ya taba koma dai mene ne ku kuka sani harkar likitanci, kawai ina son na samu shaida a wajen ka a matsayin ka na kwararren likita sananne, in ka min wannan dan qaramin aikin, na maka alqawarin dukiya mai yawa, ga wannan ka fara tabawa"
Kallon kudin ya yi sannan ya kalli Hasheem,
"A gaskiya Alhaji Hasheem, na gaji da hada maka report din qarya...kar ka manta matsalar da ta same ka a game da......"
"Dakata, ban tambayi tone tone ba, na san me nake yi, na manta da abinda ya faru da jimawa,na kalli gaba a rayuwa ta, Allah ya hore min yara har biyu, ban damu da wata sabuwar haihuwa ba balle hankali na ya tashi, zaka min abinda na ke so ko kuwa na samu wani? Ka san ku na da yawa likitocin, kuma ba kowa ne ke riqon amana ba, qalilan ne ba su cuta ko ta wanne fanni, za ka min ko na nemi wani ya ci kudin? Abu a takarda kawai, na wancan ma da ka min wa ya matsa sai ya san gaskiya, duk da na san ban biya ka da kyau ba, wannan karon bayan wanan da na baka kyauta, kai za ka yanka nawa ka ke so, shi ya sa na ce maka kasuwanci?"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...