ALBASA BATAI HALIN...14

421 38 17
                                    



Baban Zeenat bai bude dakin ya fita ba sai da ya ma Zeenat dukan tsiya, ta na nan qasa a kwance Kamar matacciya Zulfa'u ta shiga da gudu, ita da suhailah, qoqarin daga ta sukai, bakin ta a fashe, jini na zuba, ta yawu, gefen idon ta ya kumbura, da gani buga Mata kan ya Yi, ko Kuma ta buge da kan ta, Zeenat da kyar ta ke daga qafar ta, jikin ta har rawa ya ke, tsabar wahala, ba abinda ke qara Mata zafi da radadi sama da zuciyar ta, Ashe saki na da zafi? Ba ta taba zaton dan Qaseem ya sake ta za ta ji wani Abu ba, hango shi kawai ta ke ya na ririta ta, da lallaba ta, tare da nuna mata tsananin son da ya ke Mata,kukan Zulfa'u ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, hannun ta da ya kumbura ta ke kalla, ta ga yanda ya Yi jawur, tuna dukan da Baba ya Kai wa damtsen nata tayi, da hannun shi da ya dunqule, sai ka ce suna dambe da abokin shi.

Jan rigar ta tayi ta rufe wajen, sannan ta ja baya, ta haye katifar sosai, duka Kam ta ci shi, na ban mamaki, tun da an Saba dukan ta saboda rashin Jin ta, amma ba a taba Mata ya wannan ba, Kuma duk saboda Qaseem ne, gashi duk yanda ta so ta ji muguwar tsanar shi da ta ke ji a baya, ta kasa, Kuma ba ta Jin komai game da son shi, ita da ta San kawai tana tuna cewar Qaseem mutumin kirki ne, Kuma Mai tsananin son ta.

Zulfa'u ce ta shiga kitchen ta dora ruwan dumi, ta juye Mata a bokiti, sannan suka ce ta je ta yi Wanka, ta gasa jikin na ta, ta so yin musu, amma ta fasa, Dan yanda ta ke Jin jikin ta Kamar Ana yankar Naman ta in ba wankan ta Yi ba, da kyar ta runtsa.

Umma ta hango a dakin Baban su riqe da takardar da Qaseem ya bashi, hawaye ta gani na zarya a fuskar Umman ta, abinda ya Sanya ta damuwa sosai, dik rashin Jin da take ba ta taba ganin Ummaa na kuka irin haka ba sosai, ashe abindata yi mummunan abu ne har haka? To wai me ma ta Masa ne?ita fa ba ta ganin laifin ta, tunda gaskiya ta fada ba ta son shi, wataqila Wani munafurcin suka qulla shi da mahaifiyar shi, suka ja Mata duka, da tsanar iyayen ta.

Bayan ta fito daga wankan ne, ta tadda yarinyar ta kwace, ita Daya a dakin, sai ta tuna sanda Kaka Fatu ke Mata fada ta bar ta ita Daya a daki, ta ce saboda aljanu na iya zama da ita, tun wannan lokacin su rabe ta, har girman ta, a zo Ana samun matsalar rayuwa, Amma shi ne aka aje Mata ita, ita Daya ba kowa ko? Da sauri ta Isa gaban ta, ta ga tana ta jejjefa hannu da qafa, alamar ta kusan ta Fara kuka.

Da sauri ta dauke ta, ta Fara shayar da ita, yarinyar na Shan mama ita Kuma ta na kuka.


******************************

Ko da Qaseem ya koma gida ya sanar da Innar shi hukunin da ya yanke, gaba Daya jikin ta ya yi sanyi, saboda ta so ya bar ta ta dawo, in ya so in ba ta daina ba, sai ya sawwaqe Mata, Amma ta ji Dadi da bai Mata saki uku ba, ko ba komai, ta na saka ran zai maida ta.

Qaseem daren ranar bai samu bacci ba, gani ya ke Kamar za ta shiga ta na zazzaga Masa masifar ta da ta Saba, ko masifar ne ya na so, baya son rabuwa da ita, kuka kuwa ya yi shi Kamar ba namiji ba, da ya ga abun ba na qare bane, Kuma daren Mai nisa ne, kawai sai ya sauka, ya je ya yi alwala, ya koma ya tada sallah, Yana karatun sallah ya na kuka, a sujjadar qarshe ya Yi addu'a Allah ya Sa hakan shi ne ya fi alkhairi, Allah ya bashi wata wadda ta fi ta alkhairi ,wadda za ta so shi, shi ma ya so ta, su rufawa junan su asiri.

Bayan ya yi sallar da addu'a ne ya ji wata iriyar nutsuwa ta na ratsa shi, da kwanciyar hanKali ,miqewa ya Yi, ya ninke abun sallah, sannan ya kwanta, tare da yin addu'a ,tunanin irin rashin azziqin data dinga musu ne ya baibaye shi, Nan da Nan yaji rabuwar su ma shi ne alkhairi inshaa Allahu, saboda Zeenat ba macen azziqi bace, ya yi Dana sanin hada zuri'a da ita.

*****************************


Tunda Qaseem ya saki Zeenat Umman ta daga gaisuwa ba ta Kara kula ta, Sai ko wankan yarinya da ta ke Mata, Zulfa'u ta maida Mata ita, Baba ma ya fita sha'anin ta, aikin gidan kuwa tun kan ta Yi arba'in ta Fara cin shi, dokar Baba ce, ita za ta na girkin Rana kullum, Mai girki ta Yi na dare da safe, tunda lokacin ya na gida, yace bai yadda ji labarin wata ta taya ta aiki ba, ya Sanya masu kalle Masa a cikin su, ba zai fada ba, Amma sun an kan su, Dan haka kowa cikin taka tsantsan ya ke, Kar laifi ya shafe shi.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now