ALBASA BATAI HALIN...43

373 55 12
                                    

Hasheem na jin kalaman Zeenat sai ya koma, ya tsaya daga waje, tare da addu'ar Allah ya sa kar ta tona mishi asiri, in asirin shi ya tonu ya zai yi? Ga siyasa ta gabato zabe baifi sauran kwanaki ba, yafi son sai ya ci zaben nan, koma me za a yi a yi, ya na da power, ya bazama neman aljanun da za su taimaka masa akan Zhulqiyyah.

Cike da mamaki Umma ke kallon dakin Zeenat, salati ta fara bugawa sannan ta isa qofar dakin ta ce,

"Zeenat ki ji tsoron Allah akan abinda bakin ki ke furtawa, ki guji haqqi, kin san kuwa me ki ke fada? Kuma a gaban yarinya? Shin Zeenat ba ki san rayuwar duniyar nan yanda ta koma ba ko? Abinda ka ke gani ba lallai ya zama shi ne gaskiya ba, sannan abinda ya shige maka duhu wataqila shi ne gaskiya, amma ba ka gani ba, Zeenat ki iya kalaman ki, sannan ki bude qofar nan"

Zeenat kuka ta fashe da shi sosai jin kalaman Umma, tabbas ta san ta ga kayan tsafi a dakin,kuma shi ne dalilin rashin lafiyar ta, da ta ga hoton yanda ta koma a wayar Suhailah sai da ta ji kamar numfashin ta zai dauke dan tsorata da lamarin,a hankali ta bude qofar ta fita, Nawwarah kuwa da gudu ta isa gare ta ta rungume ta, ta sake kukan dikkan baqin cikin da ke cikin zuciyar ta, ita ma kukan take duk da ba ta san na meye ba.

"Momma,Waleedah da Hajiyah sun rasu, yau kwan...."

"Me ? Me ki ke fada haka? Nawwarah ki na cikin hankalin ki kuwa? Waleedah da Hajiya? Me ya same su? Me ya kashe su? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, na shiga uku ni Zeenatu, Hasheemmmm"

Da gudu ta fita ta tadda shi tsaye a jikin motar shi, yanayin yanda ya ga ta nufe shi a fusace kuma da gudu ya mugun bashi tsoro,sai ta yi kama da mutumin da ya ga maqiyin shi a fagen daga, da sun hadu sai kisa.

Wata iriyar shaqa ta mishi, da kyar ya ke numfashi, a matsayin shi na namiji ya kasa amshe kan shi a hannun Zeenat,

"Ina ka kai su? Na san kashe su suma ka yi, kamar yanda ka so ka kashe ni, Allah bai nufa ba, ina ka kai Waleedah da Hajiyah, mugu azzalumi, ina ka kai su? Sai ka fadan inda ka kai su,"

"Ke Zeenatu, Zeenatu, sake masa wuya, sake shi na ce, ki sake shi,"

"Baba sai ya fadan inda ya kai su, ko ni ma na raba shi da na shi ran, sai dai a kashe ni,"

Da kyar da sidin goshi Baba da Qaseem su ka kwaci Hasheem daga hannun Zeenat, Qaseem ne riqe da ita, dan shigar da ita gida, ba qaramin tausaya mata yake ba, rayuwar ta duk ta zama wani a birkice, da gani ta na cikin quncin rayuwa, ba ta da mafita kuma,ta maqale a cikin tarkon da ta jefa kan ta, su na shiga ciki ya sake ta ya koma waje, qoqarin sake fita take, Umma da Mama suka riqe ta, sun sani rasuwar su Hajiya da Waleedah dole ta taba ta, fitar ta Nawwarah ta sanar da su komai, kuma a yanzu Umma da Mama sun fara zargin wataqila maganar Zeenat akwai qamshin gaskiya a ciki, wataqila Hasheem ne ya yi sanadin rayuwar su, amma zato zunubi, kar su masa zato akan abinda ya ke ba gaskiya bane.

Da kyar suka lallaba ta ta shiga ta zauna, kuka sosai suke ita da Nawwarah, cikin kuka ta ce,

"Momma dan Allah mu koma gida, in ba ke tsoro nake ji, sai in dinga ganin kamar Waleedah na yawo a gidan ita da Hajiyah, kuma an ce in mutum ya mutu ba ya dawowa, kinga Mom din mu da ta rasu har yau ba ta dawo ba, amma su ina ganin su na yawo a gidan, dan Allah momma ki koma gida,"

Da sauri ta rungume Nawwarah cikin tausayawa, kowa a wajen sai da ya tausaya mata,

"Nawwarah ba zai yu na koma gidan ku ba, gidan ku ba shi da alkhairi a ciki, na jefa kaina cikin quncin rayuwa ni Zeenat, (Qaseem da Baba ne suka shigo a wannan lokacin)....da na san haka rayuwa za ta kasance min da ban bijirewa iyaye na ba, da na hakura da koma wa suka zaba min, ballantana Yah Qaseem mutumin kirki,nagartaccen namiji, na cuci kaina ni Zeenat, rayuwa ta bata da amfani, na yi rashin biyayya dan son zuciya,gashi zuciyar ba ta samu abinda take so ba, sai sabon Allah da na yi, da kuma wahala da na sha"

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now