Washegarin suna Kaka Fatu da Ummalo, suka zo, har da baby Fateema,ko da suka iso direct gidan su Zeenat suka sauka, Zeenat din ma da mai jego su na can, a nan za a yi sunan, Kaka Fatu bakin ta ya qi rufuwa, ga tattaba kunne ta samu, sai albarka take sawa, tare da fadin ai ta so ta zo da wuri, sai akai rashin sa'a Fatee ta yi rashin lafiya sai ta ce bari har washegarin suna kawai.
Zeenat sai son daukan Fatee take amma Fatee ta qi zuwa, ita dai daga Ummalo sai Kaka Fatu ta sani a wajen, abun ya yi ma Zeenat ciwo, har da kwalla ta yi, tsine wa Hasheem ta dinga yi a ran ta, rabon ta da yarinyar ta yanzu kusan shekara, gashi nan ba ta gane ta ba, da a lokacin ya mata mutunci ta dauki 'yar ta a gaban ta yaushe za ta mance ta? Fita ta yi dga dakin ta koma wajen Zulfa'u, ta zauna cikin qunar rai.
"Zeenat lafiya?"
Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba can ta nisa, sannan ta ce,
"Ina tunanin rayuwa ta ne kawai,tun daga farko har zuwa yau dinnan da diyar ciki na ta qi ni, saboda ta manta ni😢 Zulfa'u na tafka babban kuskuren rabuwa da Qaseem,ki duba ki ga matsananciyar rayuwar da na ke ciki,daga wannan musibar na fada wancan, gaskiyar Aunty Atika ne da ta ce hakuri shi ne komai,na qi zabin iyaye na, saboda taurin kai, ga yanda rayuwa ta kai ni har gidan matsafi, ba dan da sauran kwana na a gaba ba, sai dai ku ce margayiya,ita da ta yi hakuri da zabin iyaye, duk da har yau ta na son Adam a cikin ranta, amma ta danne, ta yi hakuri da zabin iyayen ta,gashi yanda rayuwa ke mata dadi, ga zuri'a Allah ya hore musu, hajjin nan ta je ta, Umara kuwa ta na yawan zuwa, hakurin ta ya ja mata alkhairi, rashin hakuri na da taurin kan sai na auri wanda nake so ya ja min musiba da bala'i, kaico na ni Zeenat, yanzu na saki reshe na kama busasshen ganye, ba wan ba qanin, Suhailah ta yi dacen samun miji na nunawa a saudiyya,ta na cikin gata da jin dad'in rayuwa, a baya ba ta son shi, ta na da wanda take so, gashi yanzu ta dawo son shi, duk son da ya ke min a baya ya maida shi kan Suhailah, ba na gaban shi, saboda rashin mutuncin da na zuba musu, ba na gaban shi Zulfa'u😢😢 ba ya ko tunani na, yanzu Suhailah ita ce fitilar zuciyar shi mai haska rayuwar shi, Zulfa'u da me na tsira a rayuwa ta kenan? Fateen ma da na ke saka ran zan ji sauqi ta wajen ta, sai kin ga ihun da ta tsanyara da na dauke ta😢😢"
Cike da tausayawa Zulfa'u ta kwantar da jaririyar ta da suke kira da Maamaa saboda sunan Umma aka saka mata wato Sailubah, kusa da Zeenat ta zauna, wadda ke kuka kashirban, hankalin ta a tashe, dafa kafadar ta tayi, sannan ta shafa bayan ta cikin sigar rarrashi,
"Tabbas Zeenat kin tafka kuskure babba, ina mai baki hakuri da ban kasance maki qawa kuma 'yar uwa ta gari ba, lokuta da dama zugar qawaye na tasiri wajen rushewar tarbiyya, ba ki da qawaye mu ne qawayen ki, Suhailah na iya qoqarin ta wajen nuna maki gaskiya,ni kuma ina bin bayan duk wani hukunci da kk yanke ban zama daga cikin masu baki shawara ta gari ba, ki yafe min, dan Allah ki yafe min"
Da sauri Zeenat ta daga kan ta ta kalli qanwar ta ta, da hawaye ya ke gangararwa a fuskar ta, share mata hawayen ta soma yi, cike da murmushi, irin na yaqen nan, mai ciwo,
"Haba Zulfa'u, ba ki min laifin komai ba, ko kin manta wacece ni? Ai kin san ba mai zuga ni, ba mai saka ni, ba mai hana ni, duk abinda na ke ganin daidai ne sai na aikata shi, ko duk duniya za su taru su ce min ba haka bane,indai ya min sai na yi. Kinga kenan ba laifin ki bane ko? Dan haka ki daina dorawa kan ki laifi a banza,komai ya samen a rayuwa ta ni na jawa kai na,"
"Ki qara hakuri Zeenat, da yardar Allah Baby Fatee a nan za a bar maki ita ma, saboda ba zan bar Kaka ta koma da ita qauye ba, ita kadai ce za ta debe maki kewa a yanzu, sannan ko ba komai Kaka ta tsufa da yawa,ta na buqatar hutu, Fatee kuma ta fara kai munzalin da take buqatar Uwa a rayuwar ta, shekara biyu da watanni yanzu ko?"
"Eh shekarar ta biyu da wata bakwai, da kwana sha biyar yau"
"Ohhh sannu raskwana, to da awa nawa da minti nawa sannan da seconds nawa?"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...