ALBASA BATAI HALIN....7

409 37 5
                                    

Tana murna ya fita, ta daina ganin baqar fuskar shi, a cewar ta, kawai sai jin sallamar shi ta yi, cikin qosawa da ganin mai sallamar ta murguda baki, tare da amsawa, kawai sai ya ga ta qara yi mi shi kyau, tsayawa ya yi, riqe da labule yana qare mata kallo, dogon tsaki ta ja, wanda ya dawo da shi hayyacin shi,

"Bashi, ko tara, ko baqar magana?"

"Me ne ne haka kuma Zeenat ?"

"Ban sani ba, kallon na meye? Ko na ci maka bashi ban biya ba?"

Cikin murmushi ya isa gaban ta, ta durqusa, ya kafe ta da idanun shi farare, itama kallon shi ta ke, da ace Zeenat bata sa wa kan ta burin auren mai kudi ba, kuma fari, kyakkyawa, ba abinda zai hana ta kamuwa da son Qaseem, namiji ne madaidaici a kyau, mai ilimin addini, sannan a boko ma ba a bar shi a baya ba, ga uwa uba tsoron Allah, da cikakkiyar tarbiyya da ya samu,ba macen da za ta kira shi mummuna, sannan ba wacce za ta kira shi kyakkyawan gaske, sai wadda ta ke son shi, saboda shi masoyi, ba a ganin munin shi.

Kauda kai ta yi, ta sake jan tsaki, har mamaki Qaseem ya ke, ba ta gajiya da tsaki ne?

"Kin yi tambaya ba ki jira amsa ba, har kin qosa da jira"

"To ai na ga baka da niyyar magana ne, ka kafe ni da ido, kamar wani sabon maye ya ga nama"

"Ki ka sani ko ni mayen ne? Amma na ki ke kadai"

"Kurwa ta kurrrr,ka yi ka dan ka ci ni, ta Allah ba taka ba, nama na daci ne da shi, na sha ruwan kasko, na kurkure da magarya, ehe, ka ci kan ka,"

Dariya ya ke sosai, ganin yanda ta dage tana neman tsari da maye, ta hanyar maganganun camfi, canfin ma ba ta iya ba, dan a iya sanin shi ba haka ake fada ba,in shi mayen gaske ne, lallai da tuni ta qare, cikin jin haushi shi ta miqe.

"Wai Ni da ba fita za ka yi ba? Me ya sa ka dawo?"

"Haka kawai, na dawo ne, dan na gan ki, dan Allah Zeenat ki saurare ni, ki yi hakuri, na san ba ki so na, auren dole akai ma ki da Ni, amma ina roqon ki, da ki bani dama, ki ga Ni, nan da wasu watanni in ba ki ji za ki iya hakurin zama da ni ba, sai mu san matakin da za mu dauka"

Kallon shi ta tsaya yi, tana tunani, ta yarda da shi ko yaya za ta yi? Can ta zauna sannan ta kama hannayen shi kamar wadda za tai maganar arziqi.

"Qaseem, ba za ka gane yanda na ke qin ka ba ne a rai na,ban san iya girma da yawan son da ka ke min ba, amma qiyayyar da na ke maka, ta fi girman son da ka ke min, ta yaya ka ke tunanin zan iya rayuwa da kai, har qarshen rayuwa ta, qiyayyar ka a jini na ta ke, ta bi dikkan sassan jiki na ta samu wajen zama, Qaseem daidai da second daya, ban taba hango ka a matsayin wanda zan iya zama na minti biyar ba a matsayin mata da miji, ka tausaya min, ka tausaya wa kan ka, da Innar ka, ka sawwaqe min, kowa ya samu wanda ya ke so, ya aura."

Qaseem bai san hawaye na zuba a idanun shi ba, sai da ya ji gishirin su a bakin shi, saboda duk kalma daya da take fita a bakin ta, jin ta ya ke, kamar ana caccaka ma zuciyar shi wuqa,da sauri ya sa hannu ya share su, ya miqe tsaye, ya cire rigar jikin shi, Zeenat wani irin tsoro ne ya kama ta, ta miqe da qarfi, kuma da sauri, ta nufi bakin qofa, murmushin yaqe, mai ciwon gaske Qaseem ya sake mata, sannan ya cire gajeren wandon shi, ya haye gado, ya kwanta, ganin ya kwanta ne, ya sanya ta sakin ran ta, can kuma wani tunani ya fado mata, zama ta yi a bakin gado, ta yi shiru, na wasu mintinan, hannun ta guda ɗaya ta daga, a hankali, za ta taɓa hannun shi, da ya miqer a jikin shi, wanda ya kwanta, tare da juya mata baya, saura qiris hannuwan su su hadu, ta janye, tare da saurin girgiza kai,

'inaa ba zan iya ba,'

Shi ne abinda ta furta a cikin zuciyar ta, numfashin shi ta ji na sauka a hankali, hakan na mata nuni da cewar ya yi bacci,dan haka, ta sauka daga gadon, ta fita tsakar gidan, tana kallon ko ina na gidan, da ace ita wata yarinyar kirki ce, da ta je ta gaida surukar ta, amma inaa, ko tunanin hakan ma bai fado a ran ta ba.

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now