ALBASA BATAI HALIN...49

419 50 14
                                    


Ba wani alamar da ta nuna hakan, saboda mutanen da ke qofar gidan qalilan ne, ya fi kama da qawaye sun taru su na hira a qofar gida.

Zaituna ce da qawayen ta su na hira game da nasarar da ta samu wajen fidda Nawwarah daga gidan ta, tun kafin ta hana ta sakewa a gidan ta.

Sallama su Zeenat su ka musu,su ka amsa cikin kallon daga ina kuke, ganin Zeenat fess ita da diyar ta, ga ta masha Allah, mai kyau, Kaka Fatu ma ba laifi ta sanya sutura mai kyau.

"Ku kuma daga ina bayin Allah?"

"Su na na Zeenat, wannan kaka ta ce mun zo ganin Nawwarah ne"

Nan take qirjin Zaituna ya buga, ganin haka ne ya sa qawayen ta su ka ce mata bari su shiga dakin ta, in ta gama sallamar baqi sai a wuce akai amarya, kamar ta ce kar su yi nisa, dan ba ta san ya Zeenat za ta dauki lamarin ba.

"Ku shiga mu je ciki, ta na ciki,Allah ya taimaka kun zo da wuri da ba za ku same ta a gidannan ba"

"Sabo da me?"

"Mu je bissmillah, ku shiga,"

Kwance ta ke, ta yi wanka, Zaituna ta bata wani farin leshi irin dan dubu ukun nan,mai ratsin baqi, an masa sassauqan dinki,sai sarqa da dan kunnen da ta saka irin yan dari biyar dinnan, da dukkan alama ta yi kuka ta gaji, zuciyar ta na mata wani irin zafi, ji take kamar ta kumbura, waje daya take kallo a kwancen, wato qofar shiga dakin, qafafun Zeenat na shiga ta gane qafar, bata dago ba sai wasu hawaye masu zafi da suka sauka mata a daidai sanda Zeenat ta rangada Sallama.

"Nawwarah dear, me ya same ki? Ko baki da lafiya ne? Ko fushi kike da Momman ki? I am so sorry love,dan Allah ki yafe min, na san ban kyauta ba, na yi babban laifi, amma karatu ne ya riqe ni, na sani banda kwakwalwar daukan karatu cikin sauqi, shi ya sa na bawa karatun lokaci na, na san ki na nan ba ki da damuwa tunda ki na gaban uncle din ki, amma dan Allah find a place in ur heart to forgive ur Momma, kin ji?"

Shiru Nawwarah ba ta daga ba, amma ta gyara kwanciyar ta, ta na kallon su Zeenat, Zeenat zama ta yi ta kama ta ta zaunar da ita a jikin ta, ta na kallon cikin idon ta, yanda Nawwarah ta rame abun ya bata tsoro,duk da ta yi tsaho ga alamar girma ya fara bayyana a jikin ta,amma ta rame sosai, da sauri ta fara qoqarin lallashin Nawwarah akan ta bude baki tai magana, ta fada mata ko.me ke ran ta, za ta dau duk wani hukunci da za ta mata, ta sani ba ta kyauta ba, cikin tsananin gajiya da komai Nawwarah ta bude baki ta fara magana,

"A lokacin da zuciya ta gaji da komai da kowa, ta gaji da azabtuwar da ta ke sha a kullum,gangar jiki ba shi da kwarin sarrafuwa,na gaji da komai da kowa Momma, da ma ni mutuwa ta dauka ba su Waleedah ba, ina ma ni ma na bisu? Momma ban ga laifin ki ba dan baki dawo gare ni ba, na ji zafin rashin ki, amma ba zan ga laifin ki ba, 'yan uwana da na zamar masu dole ma gudu na suke, na yafe maki,kuma ina maki albishir da an jima za a kai ni dakin miji"

Kuka Zeenat take Kaka na matse kwalla tsabar tausayin kalaman yarinyar, Zaituna kuwa ko sama ko qasa an neme ta an rasa a wajen,

"Me ki ke nufi da kai ki dakin miji?"

"Aunty Zaituna ta sama min miji,Uncle ya amince da shi sun daura mana aure dazu, anjima za su kai ni gidan shi,"
Nan Nawwarah ta zayyane mata duk irin zaman da take a gidan.

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ya Allah ka yafe min, ban sani ba, ban sani ba, Nawwarah ki yafe min,da na san Uncle din ki ba zai iya riqe ki da amana da kyau ba da ban bada ke ba, a tunani na dangin ki za su fi kula da ke,"

Cikin fushi Zeenat ta janye Nawwarah daga jikin ta, ta fita tsakar gida,cike da masifa da bala'i ta fara magana,

"Ina kike Zabiya kike ko zatiya, ki fito nan maci amana, azzaluma, ki fito nan sai na yi laga laga da ke, qaramar muguwa, in kin cika muguwa ki samu manyan mata ki musu mugunta mana, sai wanan yar qaramar alhakin, Allah ba zai barki ba azzaluma, munafuka,ki na ina"

ALBASA BATAI HALIN.....Where stories live. Discover now