Yamma ta yi, kowa na qoqarin rufe shagon shi, masu rumfa na ta daure kayan su, suna adanawa, Qaseem ne riqe da leda a hannun shi, yana gyara zaman hular shi, sallama sukai ma juna da maqotan shi na kasuwa,kowa ya kama gaban shi dan zuwa gida, tafe ya ke yana waige ko zai ga abin hawa, amma shiru, sakamakon cinkoson da ke akwai a kasuwar ga kantin kwari, sunan shi ya ji an kira, da sauri ya juya, dan gane Muryar mai magana,
"Qaseem yi sauri ka shigo, kar 'yan karota su gan mu"
Cikin sauri ya bude ya shiga, tare da yin sallama, gaishe da dattijon ya yi, cikin girmamawa da mutuntawa, amsawa dattijon ya yi shi ma cikin mutuntawa da yaba hankali irin na Qaseem.
"Qaseem ba qaramin burge ni ka ke ba, duk ilimin ka, ba ka sanyawa ran ka girman kai ba, ka na sana'a, tabbas watarana zaka zama abun alfahari, dama duk wanda ya kashe zuciyar shi, ya ce zai jira aikin gwamnati, tabbas yana tare da wahala, domin ba lallai ya samu ba, daga nan sai a buge da zagin gwamnati, bayan Annabi ya hanemu da zagin shugabanni,"
"Haka ne Baba, yanzu haka abokai na qalilan ne suka samu aiki, saura ba aikin ba sana'ar, kusan mu biyu ne kawai ke kasuwanci, Allah ya taimake mu dai,"
"Ameen Al-Qaseem, kaga a haka ai za ka iya samun na kan ka, ka kula da mahaifiyar ka, har ka yi aure ko?"
Sosa qeya ya Fara, Yana murmushi, Daga baya kuma yanayin shi ya sauya, daga murmushi zuwa bacin rai.
"Ina fatan dai kun daidaita da mutuniyar, domin abinda zan yi kenan na dawwamar da alaqar da ke a tsakani na da marigayi mahaifin ka,"
"A gaskiya Baba ba mu daidaita ba, ina ganin kar ayi abinda zai sa zumunci ya rushe, tunda Zeenat ta nuna bata so, a hakura kawai, Allah ya bani wata da ta fita, itama Allah ya bata wani da ya fini"
Juyawa dattijon ya yi, ya kalli yanayin fuskar Qaseem, cikin nuna bacin rai ya ce.
"Wato yarinyar nan ba ta jin magana ko? Bari zan je gidan na same ta, ko ta qi ko ta so sai an yi auren nan, in ya so ta kashe kan ta, a hakan za a kai maka gawar ta dakin ka, in ya so an sallace ta a can kaji yarinya sakarai"
"Baba dan Allah ka yi hakuri, in ka mata magana akai na sai ta sake jin tsana ta, dan Allah abi komai a sannu, kar a bata mata ta ta sake bijirewa"
"Ita ta haife mu kenan, bana son sake jin haka a wajen ka, bar ni da ita zan maganin ta ai"
Qaseem bai sake magana ba, amma shi ya hakura da ita har abada, saboda bai ga ta yanda Zeenat za ta dawo son shi ba, ita ce zagin halittar shi, ita ce kushe samun shi, komai na shi baya burge ta, a ra'ayin ta tafi son miji mai kudi, kyakkyawa, kuma gaye ba shi mai ruwan ustazai ba.
Tsayawa da motar ne ya gane an iso gidan su, sallama ya yi ma Baban su Zeenat ya rufe qofar bayan ya fita, amsawa baban su Zeenat ya yi, ya ce ya gaishe da mahaifiyar shi, sannan ya tafi.
Da sallama ya shiga, lokacin ta na sallah, dan haka ya ajiye ledar da ya kawo mata ya fita masjid shima,sai da akai isha'i sannan ya fita dan zuwa gida, a hanya ya ta wajen mai saida tsire ya siyo masu na dari uku sannan ya koma gida.
Zaune ta ke a qasan kujera saman sallaya, tana jan carbin ta, sai istigifari ta ke, tana sakewa, saboda halin da rayuwa ta ke ciki a yau, sai da tuba wajen Allah.
Da sallama ya shiga, ta amsa,
"Bismillahi ya Allahu ya rahmanu, Inna azkar ki ke ne har yanzu? Ga wannan in kin idar,"
Sai da ta kai qarshe sannan ta kalle shi, ta ce,
"Sannun ka da zuwa Qaseem, ya kasuwar,ina fatan dai an samu ciniki, Allah ya yi maka albarka"
"AlhamdulilLAAH Inna, ga wannan ma a dan taba, yau kam AlhamdulilLAAH an samu kasuwa sosai, ina fatan kin wuni lafiya?"
"AlhamdulilLAAH to, haka ake so, Allah ya qaro budi, da kasuwa mai yawa mai albarka, Allah ya yi albarka, ka taho min da saqon sarqoqin nan qirar India da ake yayi ko? Dazu dazunnan maqota suka shigo, suna son Wanda za su saka a lefen Muhammadu,"
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...