Bakin shi har rawa ya ke, a yau ya Yi dana sanin sanin Zeenat ma, balle soyayyar da ya ke Mata, ganin halin da ya shiga nee Innaa ta juyar da shi zuwa inda ta ke, sannan ta ce,
"Al-Qaseem kalle ni, kalle ni na ce, dai na kallon ta, mu je daki na, ina son magana da Kai, in dai Ni na haife ka, Kar ka furta ko da kalma Daya ne, mu je"
Yana juyawa wasu hawaye masu gudana da qarfi, da zafi suka Fara sauka a fuskar shi, qirjin shi har dagawa ya ke saboda bacin Rai,yau shi mace ke ci wa a mahaifiyar shi mutunci, Kuma a Hana shi magana, a Hana shi rabuwa da ita?
A Hakan Innaa ta dake zuciyar ta, ta danne dik abinda ya taso Mata na bacin Rai, suka zauna a kujera a dakin ta, ba ta Masa magana ba, sai da ta tabbata ya gama koka baqin cikin ran shi, idanun shi sun kada sun Yi jajawur sannan ta ce,
"Al-Qaseem ,ina roqon alfarma a wajen ka, ka yi hakuri, kar ka sake ta, ba a son sakin mace da juna biyu, wannan shi ne babban dalili na,ka bari har Allah ya sauke ta lafiya, in ta sauya hali kafin lokacin, sai mu yi hakuri mu rungume ta da hannu bibbiyu ,in ba ta sauya ba, na maka izini, ka sawwaqe mata, ina fatan za ka duba uzuri na?"
Ajiyar zuciya mai qarfi ya sake,bai iya furta komai ba, amma ya saurari me ta ce, kuma ya amince, amma ya na tunanin yanda zai qara hada ido da Zeenat ,matar da ya ke tsananin so da kuma tsana a lokaci daya, lumshe idon shi ya yi, tare da miqe qafafun shi, ya kwantar da jikin shi a bayan kujerar, ya na ta tasbihi ga Allah, tare da neman sauqin zugin da zuciyar shi ke masa.
Zeenat kuwa hankalin ta ya tashi ainun, kar dai Baban ta za su fadawa abinda ta yi? Me suke tattaunawa ne? Me ya faru da suka shiga dakin Inna ? Sai kaiwa ta ke ta na komowa, hankalin ta ya qi kwanciya, bayan kusan rabin awa, Qaseem ya shiga dakin, ta ga ya kalle ta, fuskar shi a sake, kamar ba abinda ya hada su,sai ta ji gaban ta ya fadi, me hakan ke nufi? Sauya kaya ya yi, ya dau qaramin qur'anin shi, ya ce mata.
"Zeenat na tafi kasuwa, a sanya mu a addu'a, akwai abinda ki ke so na taho Maki da shi?"
Wannan shi ne abinda ya saba fada mata, kafin ya fita, sake baki ta yi ta na mamakin hali irin na su baki dayan su.
"Wai lafiyar ka qalaou kuwa? Ka na ma da zuciya a qirjin ka kuwa Qaseem ?"
"Ni kuwa na ke da zuciya, amma ta yafiya, kauda kai, da tausayawa, sannan da soyayya"
Bai jira ta bude baki ba ma balle ya ji me za ta fada, ya fita ya bar ta a wajen, riqe da koma me ta ke shirin furta wa, dan ya san ba alkhairi ba ne.
Ko da ya fita ya jima a soron gidan kafin ya qarasa fita waje, dan samun nutsuwar zuciyar shi.
Yau a kasuwa haka ya wuni ba wani kuzari a jikin shi, ya so ya je ya saro sabbin dan kunnayen da ake yayi, amma rashin kuzari ya hana, sai waya yayi, ya ce a aje masa, na dubu sha uku, gobe inshaa Allahu zai je ya amsa.
Ko da ya taso daga kasuwa, tsayawa ya yi, wajen masu nama, ya siyo Mata kayan ciki, na dubu daya, Inna na dari biyar, ya wuce gida, ko da ya shiga gidan, Inna ba ta tsakar gida, daki ya bi ta, ya gan ta zaune ta na lazimi, ka fin a kira sallah .
"Innaa ashe ki na ciki,"
"Eh Qaseem ina ciki, ka dawo kenan, sannun ka da dawowa, ya kasuwar"
"Sai shukran Inna ,gaba daya ji na nake kamar ba Ni ba yau, na gaji da yawa, bari na watsa ruwa kan a kira sallah, ga wannan,"
"Qaseem ba ka gajiya, Allah to ya qara maka budi, ya yalwanta maka arziqin ka, Allah ya yi wa rayuwar ka albarka, da ta dukkan yaran musulmi"
"Ameen Innata, bari na je,"
"To"
Da kallon tausayawa ta bi shi, da ya san yau me Zeenat ta mata bayan fitar shi, da ya qara hasala da ita,
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...