Fuskar ta ba yabo ba fallasa ta shiga gida, Fatee ma ta je da gudu ta rungume ta, tare da yi mata barka da dawowa, a sanyaye ta amsa, tunani ne fal ran ta, za ta auri Auwal ne domin faranta ran iyayen ta, domin ta wanke masu baqin cikin da ta sanya su a baya, dan ta kare mutuncin 'yar ta, dan ta kare nata mutuncin, amma ba dan soyayya ba, wataqila ta gama soyayya har abada ba ita ba sake soyayya, sai dai zaman girmama juna, da qaunar juna, (Qauna ta fi soyayya qarfi ai dama, ko me kuka ce? Wace za ta bamu banbanci tsakanin so da qauna ne? Ni har yau ban gama sanin banbancin su ba fa casssss ina jiran amsar ku).
Ta na cire kayan ta Nawwarah ta fito daga wanka, kallon ta ta yi, cike da kulawa sannan ta ce,
"Momma ki na lafiya kuwa?"
"Eh lafiya qlou nake, ya makaranta? Ina fatan dai komai na tafiya normal?"
"Alhamdu lilLAAH Momma, komai ya na tafiya daidai, sai dai wannan karatun ya na da tsauri, da ba na samun taimakon koyarwa wajen ki na san ba zan iya ba"
"Habaa mai zai hana, ai ko da can ke mai qoqari ce,so ba ki da matsala"
"Momma pls sanar dani matsalar ki, u ar not ok"
Ajiyar zuciya Zeenat ta sauke, sannan ta ce,
"Baqo zan yi, ban san ya zan sanar da su ummaa ba,Auwal da nake yawan baki labarin shi, shi ne zai zo yau, na amince mishi, ban da zabi Nawwarah, ina son iyaye na su yi farin ciki da ni, ko sau daya ne a rayuwa ta, ina son su ji dad'in samuwa ta a cikin zuri'ar su"
"In Allah ya yarda za ki zama Momma, kuma na yi murna sosai, da gaske, da kk samu miji kamar shi,daga yanda kk bada labarin shi mutumin kirki ne,"
"Kwarai, dan gaskiya ban taba samun shi da wani aibu ba, duk da ance mutum tara yake bai cika goma ba, amma gaskiya ba laifi Auwal mutumin kirki ne"
"Then ni zan sanar ma da Ummaa zuwan shi, kar ki damu"
"Ok dear thanks"
Wanka ta shiga, kafin ta fito har Nawwarah ta baza labarin zuwan Auwal, ranar ita da Mama suka yi abincin tarbar baqo, marasa nauyi, da abin sha, Fatee na home work, ta na tambayar waye zai zo? Nawwarah ta ce mata baqo za ai,
"Is he special Adda Naawah? Na ga kina ta aiki"
"Yes he is a special parson to Momma"
"Really?"
"Da gaske,"
"In yi wanka nima na yi kwalliya? Kamar Momma?"
"Eh je ki yi wanka ki yi kyau Baby Fateema, sannan in ya zo ina son ki gaishe shi sosai, banda rashin ji, ko rashin kunya kinji ko?duk da na san u ar a gud gurl"
"To Adda Naawah,"
"Yauwaa Baby Fateema, maza ki je ki shirya"
"Ni bana son Baby,"
Dariya Nawwarah ta yi, ta na jin dadin tsokanar qanwar ta.
Ana idar da magrib Auwal ya iso, lokacin Baba ya dawo ya kuma ji labarin zuwan nashi, ya yi matuqar farin ciki,da ka kalli Ummaa za ka gane ta na cikin farin ciki, domin Zeenat ta basu mamaki dika, a zaton su taurin kan ta na nan, sai gashi ta kawo wanda zata aura, dama sun san ta na da manema da yawa, ta dai qi fidda kowa ne.
A parlourn Baba suka zauna, Auwal ya ci abinci sosai ba wani jin kunya, ya gaida su Ummaa da Mama, ba qaramin jin dadi sosai suka yi ba da suka ga kamalar Auwal da fara'ar shi, tare da muna sakewa da su, kamar an dad'e ana tare.
Baba ma ya taba hira da Auwal, tare da yi masa tambayoyin da ya ke son fahimtar shin wane ne Auwal? Samun kyawawan amsoshi a wajen shi ya sa ya ji ya kwanta mishi, ya bashi izinin turo magabatan shi.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...