Kaka Fatu ce ta kalli Umma cikin mamaki, Aunty Atika kuwa bakin ta bude ta ke kallon ta, Ummalo kuwa a zuciyar ta fadi take,
'Ai gwanda a samu mai nuna ma wannan mara kunyar iyakar ta'
"Sailuba lafiyar ki kuwa? Ke ce da bakin ki ki ke kiran kin yafe Zeenatu? Akan wanne laifin?"
Umma ce ta duqar da kan ta, sannan ta share hawayen da ya ke barazanar sauka a fuskar ta, ba ta jin za ta iya sanar da kowa abinda ke ran ta, shi kan shi Baban Zeenat da alama bai san komai ba, dan ta ga yanda ya ke ta rawar kai a bikin, ya na kuma tambayar Zeenat din in da akwai abinda ta ke so ta fada, dan haka za ta bar komai a ran ta, amma ba za ta iya jure kallon Zeenat ba, gaba daya ta fice mata a rai, ba ta son ganin ta balle har ta zauna kusa da ita.
"Magana na ke kin duqar da kai kin yi shiru,"
Gyara zama ta yi, sannan cikin sanyin murya ta ce,
"Dan Allah Kaka ki yi hakuri, ba zan iya sanar ku komai ba, ina roqon afuwar ki in abinda nai ya bata ran ki"
Mama dai ta zuba ido ta ji ita ma wannan sabon lamarin da Umman ta fito da shi, jin ba amsa ne ya sanya ta miqewa ta fita, tare da fadin
"Allah ya kyauta"
Kaka Fatu kuwa kimtse vakin ta tayi, ba ta son ta tursasa Umma fadin abinda batai niyya ba, amma ta so sanin dalili, Umma ba mace bace mai tsanani, tunda tai kalamai haka Zeenat ta kai ta maqura, kiran sallar Azahar aka yi Umma ta shiga dan yin wanka da sallah.
Sun yi jungum jungum Suhailah da Inna suka sallama, nan aka hau masu lale maraba, Atika na ganin gidan ya fara taruwa ta miqe ta shige dakin Zeenat wadda ke kuka kamar ran ta zai fita, sakamakon kalaman Umma da suka doki zuciyar ta, tambayar kan ta take ta na kumawa akan me tayi ? Me ya faru, ko dai ta san me ta aikata da Hasheem a mota ne? Nan take gaban ta ya yi mummunan faduwa, daga kai ta yi da sauri daga kifashin da ta yi, ta fara wara idanun ta, hannun ta na tsananin rawa ta ke danna kiran shi, ba ta wani jima ta na ringing ba ya daga, dan shi ma a matse ya ke ya ji ko asirin su ya tonu,
"Hello My Zeenat, ki na lafiya? Kowa da komai lafiya ko?"
"Ba bu lafiya Hasheem, asirin mu ya tonu, ummana ta san komai,"
Miqewa tsaye ya yi da sauri, ya fara zagaye parlour-n 😨😨
"Zeenat ta ya akai ki ka bari ta ga wayar ki? Me ya kai ki barin wayar ki inda wani zai bincika? Ko kuma ki bar hotunan mu ba tare da kin goge ba?"
"Wanne hotuna?"
Damqe bakin shi ya yi, sannan ya shafa kan shi da ya sha sabon aski, lumshe ido ya yi, saboda bai ma san me ke faruwa ba.
"Kin ce asirin mu ya tonu?"
"Eh ina nufin Umma ta gan mu a mota, sanda munaa....immm sanda munaaa...abun nan"
Wata ajiyar zuciya ya sauke, mai qarfi, tabbas ba su ga video-n ba, indai ba su da ajajjiyar hujja akan shi bai damu ba ko da sun san me sukai a wayar ma, murmushi ya sake sannan ya ce,
"Zeenat ba wanda ya ga komai, ke ce dai ki ke ganin haka, yanzu ba wannan ba, ki shiga whatsapp ki goge dik hirar mu, ki je Gallery ki goge duk wani hoto da video da na turo maki,in ba haka ba, asirin mu da bai tonu ba zai tonu"
Kashe wayar ya yi, Zeenat kuwa jiki na rawa ta shiga inda ya ce ta shiga, nan fa ta dinga ganin hotunan su tsirara da video, da wanda ta dauka itama, cikin sauri da kuka ta hau goge su, ta tabbata wannan abun Umman ta ta gani, to yaushe ta gan su? Ta yi iya qoqarin ta tuna inda Umman ta gan su ta kasa, Atika da ke tsaye tun sanda ta fara wayar har goge hotunan da take, hankalin ta ya tashi, rufe qofar ta yi ta zauna a gefen Zeenat din da ba ta san zuwan ta ba ma, a tsorace ta miqe. Tare da manna wayar a qirjin ta, bakin ta na rawa, ta na son tai magana ta kasa, kawai sai ta fashe da kuka ta fada jikin Atika.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...