Sai satar kallon shi ta ke ta na mamakin anya Hasheem ne da ta gani a Panda har ta ji ta na son shi? Ga dai fuskar shi nan dauke da suffar da ta san shi da ita tun asali, amma abubuwan da ya fada mata, da kuma wanda ya aikata a gaban ta sun sauya tunanin ta akan shi.
'Allah sarki Qaseem, rayuwar ka cike take da gaskiya da amana, tare da so mai tsafta, ga tsananin tsoron Allah, wanda shi ya sa ka hakuri da halayyata, ka yi gaskiya da ka ce na je ka ga irin mijin da zan aura, ba na fatan ka san waye Hasheem, dan hakan is a very big slap to my face, i can't let anyone knw about u Hasheem, u will remain my scret, ba zan ji kunya gaban dangi na ba'
"Tunanin me ki ke haka? Mun iso, ki fito,"
Da sauri ta kalle shi, sai ta ga wata qaramar qofa sabanin babban gate da ta gani, amma qofar kalar gate din ce, baqi mai digon fari-fari a jiki, sai golden ado da akai ma qofar da wasu irin qarafa masu kyau,makulli ya sa ya zaro wani key ya bude qofar, ya ce ta shiga.
'Ni Zeenatu nan kuma ina ne?'
Wani waje ne zururu ba haske sosai, amma wajen ya hadu, duk tyles ne daga sama har qasa, farare tass, wani makunnin fitila ya kunna nan da nan haske ya gauraye wajen, ya kalli fuskar Zeenat da ta sauke wani numfashi mai qarfi, zuciyar ta na dagawa a qirjin ta, murmushin mugu ta ya yi, sannan ya rungume ta,cikin rada ya ke magana,
"This is my scret door, daga ni sai ke muka san nan, na biyo da ke ne saboda ba na son a san ba a gidan muka kwana ba, dan ban sani ba ko akwai mutane a ciki da yawa,.....nan wajen Zeenat ba na son kowa ya dinga min kai kawo a wajen,ba hanyar wucewar kowa bace, ina mai gargadin ki da kar ki sake ki zo nan, in kunnen ki ya ji, jikin ki ya tsira"
"Ok na ji, ballantana ma ni me zai kawo ni nan, waje baqiqqirin haka,"
Wani daki suka wuce, Zeenat ta bi dakin da kallo, dan kar ta zargi wani abu, sai ya ce,
"Baqin kare na aje a dakin nan, irin durwan nan, masu yagalgala naman mutum, na aje shi ne saboda barayi, kar ki ce za ki gigin budewa, duk sanda ki ka bude Zeenat sunan ki gawa, ko qashin yatsan ki ba za a gani ba"
Hannu ya sa ta baya ya sake zagaye qugun ta zuwa gare shi, wata qara ta saki, tsabar tsoro, ba ta zaci hannun shi bane da fari, dariyar mugunta ya saki,Zeenat ta matsu su bar wajen, dan bata ga amfanin tsayawar da suke suna magana a wajen ba,da sauri ta kai ga qofar gaba da ta ke kyautata zaton nan ne qofar shiga gidan, tunda ba wata qofa bayan ita.
Bude masu yayi, sannan ya kashe fitilar da ya kunna a wajen shiga, su na shiga ya kulle, wani sanyi mai ni'ima ne ya doki hancin ta, irin dakin da take mafarkin samun irin shi ne, har ma ya fi dakin da take mafarki kullum, daki ne wanda za a ce Masha Allah, in an kalla,komai na gayu da more rayuwa akwai a dakin, kusan komai milk color ne sai golden shi ma, daga nan ta fuskanci ya na son abu kalar golden, kusan kayan da ya dunka mata ma duk akwai golden masu yawa ciki.
Ta na ta qarewa dakin kallo ya zauna, a kujerar da ke dakin irin ta sarakai, ya dora qafa daya kan daya ya na bin ta da kallo, tare da murmushi, ita kuwa sai sake kallon wajen take,
"Ya ki ka ga dakin mu, ya miki? Ko akwai abinda ki ke son a sauya? Domin ni duk abinda ki ke so shi nake so Zeenat"
Ajiye mayafin ta tayi a gefen gadon, sannan ta taka zuwa inda ya mata nuni, wato gefen shi, zama ta yi duka rabin jikin ta na nashi, ta daga kai ta kalle shi, sannan ta ce,
"Ba abinda bai min ba a dakin nan, ban taba tunanin zan zama mamallakiyar irin wannan dakin ba, na gode Hasheem"
Haushin kiran shi da Hasheem kai tsaye da take yi ya ke ji, amma ya danne, bari zai koya mata yanda ake yi, tunda ya ga bata waye a harkar gidan miji ba, a zaton shi tunda ta taba aure ta san abubuwa sosai, amma inaa, yanzu kallon da ya ke mata kamar na budurwar da bata san abubuwa sosai ba ne, dadin abun da ya koya mata abu ta ke daukewa.
YOU ARE READING
ALBASA BATAI HALIN.....
RomanceI love you so much my Zeenat, and I promise to love you till the end of our time, I will never ever leave you, you are mine, and I am yours, Zeenat Allah ya albarkace ki, ya albarkaci rayuwar ki, da ta iyayen ki, da ta zuri'ar ki baki daya, Zeenat k...